Chapter (19) yarima SAHEEL

58 9 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(19)

Wajen kwalliya aka shiga da duk wata sabuwar baiwa domin gwada yanayin salon ta dakuma roll din dazata taka a matsayin ta na baiwar daza ta na dauke wa bakin masarautar kewa.
Tun daga wajen gyaran jiki fatar fahreeyah tayi wani irin laushi da haske tun kafin a je ga dora kwalliya dakuma kayan sakawa, zalziliyyah ce ta matso kusa da ita bakin ta a bude saboda kyan da taga fatar ta tayi da kwalliyar,
"Gaskiya jikinki yana da kyau sosai,zaki kasance a wajen masu tarar manyan baki"
Wani irin faduwar gaba ne ya riski kirjin fahreeyah sakamakon furucin daya fito daga bakin zalziliyyah, yayin da a bangaren Kirisah kuma bakin cikin ya lullubesu ita da mabiyanta saboda jin matsayin da aka bawa sabuwar baiwa bayan su sun dade a wajen basu samu ba, fahreeyah yace ta daga idonta tana kallon zalziliyyah da take ta kwaro mata bayani kafin tace,
"Shugaba da kinyi hakuri kin barni a matsayina na da din kawai domin inaga kaman shiya dace dani,a matsayina na sabuwar baiwa a wannan wajen"
"Nariga na Yankee hukunci, sannan inaso ki sani cewa abinda ya dace da masarauta nakeyi ba wai ra'ayinku ba, domin inaso kusan cewa tun ranar da kuka shigo wannan masarauta da sunan bayi kuka rasa duk wani yanci da kuke da shi dan haka banason wani yasake saka min baki ko shishshigi a cikin aikina"
Shiru ne ya ziyarci wajen sakamakon yanda sukaji zalziliyyah tana ta fada akan maganar da fahreeyah tayi dahaka wajen ya watse kowa yakama hanyar inda aka kaishi domin yin aiki.
Fahreeyah ce tsaye a bakin dakin su na da, kafin a sauya mata matsayin ta, shiru tayi kaman mai tunani tana cizon yatsa, domin daga ganin ta zakasan cewa tsoron shiga dakin take,waigawa tayi da saurin jin anayi mata magana a bayanta,a jiyar zuciya da sake dan ganin mai maganar ba kowa bace illah Sareenah,wanda suka hadu a wajen wanka jiya, murmushi tayi mata kafin tace," me yasame ki haka kike tsaye a wajen? Ko tsoron shiga kike?"
"Ehh to.... dama kayana zan dauko a dakin"
"Karki damu muje na rakaki dama nazo wajenkine, domin naji dazu shugaba ta mayar dake sashenmu kuma naga baki zo ba har yanzu to shine nazo Naga ko lfy?"
"Ahah bakomai kawai ina tsoron shiga dakin ne"
"Hmm ai naga alamar hakan, karki damu muje na rakaki"
Shiga dakin sukayi amma duk da haka fahreeyah na boye a bayan Sareenah,
"Hhhhhhhhh hmmmm wai ke gaki baiwa mai matsayi ko? to ki saurari zuwana cikin rayuwar ki,sai kin kwammace ba a haifeki ba wlh, hmmmm mujuba ni dake,nadade ina mafarkin zama baiwa mai babban matsayi amma wai zuwan ki yau har kin samu, hakan bazai yiyu ba .......
"Gashi kuma ya yiyu kuma, sannan da kike zancen ta kwace miki matsayi ai ba ita ta Hana a dauke ki ba koh!??baki cancanta bane shiyasa,ke fahreeyah je ki dauko kayan ki kizo mutafi"
Cikin sanda kaman za'a ce arrrrr ta ruga da gudu,taje ta dauko kayan a wajen kwanciyar ta jiya, hanyar kofa suka nufa zasu fita,sai kuma muryar Kirisah ta kara ziyartar dodon kunnensu,
"Da gake har mai daure miki kan macijin kina wasa da wutsiyar zaku ga abinda zan muku hmmmmm"
Ko ci kanki basu ce mata ba suka fice daga dakin,tana ta bambamin fada ita kadai.
Bayan sun fitone Sareenah ta kalli fahreeyah kafin tace,
"Gaskiya kina da sanyi dayawa sannan tsoron ki yayi yawa"
"Kiyi hakuri nasaka ta zageki koh"
"Ina zancen kinada tsoro amma kina ban hakuri"
Murmushi kawai fahreeyah tayi mata kafin tace,
"To ai bansan mai zance miki ba saboda ban tashi cikin mutane sosai ba, shiyasa"
"Menene tarihinki to?zanso naji sannan kuma mai yasa kika tsinci kanki a wajen nan?kada kiyi tunanin ni macuciyace, kawai tun ranar da nafara ganin ki nasan bakiyi kama da irin bayin nan wajen ba,naji kawai kin burgeni sosai".
"Shikenan nayi alkawarin zan baki tarihin rayuwa ta amma inaso kidan bani lokaci kadan, sannan inaso kibani takaitaccen bayani akan wannan masarautar ko kadanne"
"Shikenan inshallah zan sanar dake dan abinda nasani akan wannan masarautar,amma kafin sannan mudan zaga sauran wajajen da baki saniba tukunna"
Sareenah ce ta jaa fahreeyah sukayi cikin fadar domin zagawa da ita ko ina.
Tafiya suke suna dan taba hira,duk inda suka wuce sai Sareenah ta fada mata inane sannan kuma ya ko'ina yake dakuma tsarin sa, fahreeyah yace ta tsayar da Sareenah tare da nuna mata wani gini mai kyau amma da alama bakowa a wajen,bayan ta nuna matane kuma ta tambayeta to wajen shikuma inane,ajiyar zuciya Sareenah tayi kafin tace,
"Fahreeyah ba'ason a dunga maganar da ta shifi wancan ginin a wannan masarautar saboda hukunci yakan iya hawa kanki idan akaji hakan,tunda na gama nuna miki komai yakamata muko ma haka kuma,"
Zanta Sareenah tayi suka fara komawa muhallin su,amma har sannan idon fahreeyah yana kan wannan ginin da tagani, haka kawai taji wajen ya birgeta sosai.
Saida sukaci abinci kaman kullum kafin suka koma dakin su, fahreeyah ce ta kalli Sareenah cikin kaguwa da san jin labarin masarautar,
"Uhmm Sareenah ina jinki bani labarin to"
"Uhm dama kinada surutu haka fahreeyah? Sanda na fara ganin ki ban zata zakiyi surutu haka ba"
"Eh nidai naji,mufara labari tunda kinmin alkawarin koh?"
"Shikenan to"
""Da farko naji kince baki san ko sunan masarautar nan ba, to sunan ta*masarautar BAHMEER* ita wannan masarauta tana da karfin mulki da iko domin itace da biyu a duk duniya mai fada a ji,dazu kin tambayeni wani gini muna tafiya,to wannan ginin ba mallakin kowa bane face na babban dan sarkin wannan masarauta wanda yayi batan zana shekaru uku dasuka wuce sanadiyyar wani sabani sa suka samu shi da iyayensa,mai suna yarima SAHEEL, kuma har yanzu ba wanda yasan inda yake, saidai labari ya taba zuwa cewar anganshi a garin bardugu ...........
Ehh saheel, kuma garin bardugu.   ..

SADI-SAKHNA ce

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now