Chp(25)na shiga uku!!!!

66 8 2
                                    

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(25)
Sanyin daya busane a ciwon dake bayanta ya farkar da ita daga wahalallen baccin data lula.
Yunkurawa tayi ta tashi dakar saboda azabar ta takeji tana jiyartar ko wane bangare na cikin jikinta,dago idanunta tayi suka hada ido dasu saleeerah wanda dama suma ita suke kallo,bataji wani abu waishi sannu ba daga bakinsu saima ji datayi sunce
"Kinyi sa'a ma basu wani yimiki hukunci mai tsanani ba saiki saba kafin zuwan na gaba"
Shiru sukayi babu wanda yasake cewa komai a cikinsu ,ita tanaji da ciwon dake jikinta suma kuma sunaji da nasu azabar.
Haka fahreeyah tafara sabuwar WATA RAYUWAR,a cikin kurkun har ta shafe wata guda,jikinta yasanja sosai haka ma kamanninta,ga kuma zazzabin data keyi a kowane dare wanda yanzu shima yazame mata jiki,tun tana damuwa har abin ya daina bata tsoro,saboda tasan kawai mutuwa zatayi sboda wahala.
Wata ranane bayan an bude kofar kurkukunsu zasuje sassakr dutsi,sai yakasance su saleeerah sun fito suna jiranta amma fahreeyah ta gagara tashi daga inda take zaune,masu aikin wajenne daya ya darara mata tsawa,dan a irin tsoro irin na fahreeyah da tuni ta tashi daga inda take,saidai abin yawuce karfinta da tunaninta,saboda abune daya dade yana cinta tsawon wata guda a yanzu kuma tazo dadai inda bazata iya jurewa ba,dayanne wanda yake gefen wanda yayi mata tswar yace,
"Ka kyaleta kawai inaga mutuwa zatayi ,mutafi da sauran in kafin mudawo ta mutu saimu zefawa kuraye a jeji kawai"
Juyawa sukayi zasu tafi alamar sun yarda da zancen dayan,nishi dasake yi mai karfi wanda yasasu tsayawa suna kallonta daga inda take kwance,kaman masu nazarin wani abu sai kawai suka ciccibeta sukayi wajen shugabansu da ita,domin yaga mai yake faruwa.
Jefata sukayi a gabansa tareda labarta masa abinda yake faruwa ,kallinta yayi babu alamar wani tausayi a fuskarsa yace,
"Ku maids its Iran ta Marisa mutuwa ku bawa kurayen su cinye duk da ba wani nama zasu samu ba"
Amasawa sukayi da to tareda janta domin mayar da ita inda suka dauko ta,har sunyi nisa sai saleeerah tayi caraf tace,
"Dama so take ta mutu ta huta da wannan wahalar inaga allah yakarbi addu'arta neh"
Shugabanne yajuyo dayji mai saleeerah tace,sannan yayi ma yarabsa alamar su dawo da fahreeyah,
"Karku mayar da ita wajen,hakan shine fatanta,domin saboda bata aikata komai ba mutuwar tamkar hutuce a gareta dan haka ku kiramin,INNA KAINANA,yanzunnan tazo aiki yasameta"
Toh suka amsa da karfi kafin shikuma ya zauna akan kujerar sa yana jiran.
Bayan wasu dakiku ne gasu sun shigo da wata tsohuwa wanda bazata wuce,shekara sittin ba,kallonta yayi kafin yace,
"Ga wannan halittar zaki je ki kula da ita sannan kibata duk wani magani da zai sa ta warke,bayan ta warke saiki fada mana zan turo a zo a dauketa ,inda zatayi aikin da saita biya kimanin kulawar da za'a bata"
Ya na gama fada ya bar wajen cikin wani sauri irin na wanda karfi ya ratsa cikin jikinsu, inna kainana,batace komai ba si juyawa da tayi ta nufi hanyar data shigo,suna ganin hakan wani ya ciccibi fahreeyah yabita a baya.
A bakin wata bukka suka tsaya wanda take kewaye a wajen wasu bishiyoyi masu yalwar duhu,inna kainana ce ta fito da wani dan makulli daga aljihunta ta bude dakin,yayinda shikuma mutumin ya shiga da fahreeyah cikin dakin tareda shimfida ta akan wani buzu daya gani a tsakiyar dakin.
Saida tagama nazarin jikin fahreeyah kafin tafara dan dagata tareda jingina ta da jikin bukkar,kallon mutumin tayi kafin tace,
"Kana iya tafiya aikinka yagama cika"
Sunkuyar dakai yayi alamar girmamawa kafin ya bar cikin dakin.
Saida fahreeyah tayi sati a wajen inna Kainana inda take bata kulawa ta musamman,tareda gyra mata ciwon dake jikinta,wanda a yanzu har tashi take tana zaunawa da kanta saidai har yanzu ko magana batayiwa inna Kainanan ba,illah iya kaci idan ta kawo mata magani zata karba tasha ko kuma abinci.
Rananne tana zaune ta zuba wani gefe a dakin kallo da alamun ta tafi wani zurfin tunani wanda ita kanta bata san taka maimai mai ya kunsa ba,maganr INNAN ceh ta katseta inda taji tana tambayarta,
"Y'a ta tsawon sati guda kenan ina kula dake saidai kowane dare ina jin jikinki yana zafi alamar zazzabi shin dam kina fama dashine ko sanadiyyar jinyar nanne kika fara,?"
Kaman fahreeyah bazatayi mata magana ba saikuma tace,
"Ba sanadin ciwon nafara ba dama inayi "
"Kaman tun yaushe kenan?"
"Zaiyi wata uku kenan"
"Ayyah sannu kinga na cika ki da surutu koh,kuma a yanayinki naga kin shiga al'amura da dama a rayuwa,saidai inaso kidaure akan yanda kike a da kinji ,wata rana sai labari,ki kara hutawa saidai inaso kibani tarihinki koda ba yanzuba saboda naga ta ina zan fara taimakonki kinji?"
Jijjiga kai fahreeyah kawai tayi batareda tasake cewa komai ba.
Haka rayuwarsu ta cigaba da gudana inda har saida fahreeyah tasake samun sati guda akan wanda tayi a wajen innan,yanzu tafara sakewa har hira suna danyi kuma tana tayata wasu kana nan aiki duk da jikinta bai gama yin karfi ba,inna ce tafara sako hira akan rayuwarta lokacin da dare yayi zazzabin yafara rufe jikinta,
"Ina so Y'a ta yaukam ki bani labarinki saboda nasan wane magani zan baki akan wannan zazzabin,saboda bansan ta yanda zan faraba harvsai idan nasan mai yake faruwa"
Tunani fahreeyah tafarayi a ranta cewa mai kuma hadin zazzabin da labarin ta,anya kuwa ta bata labarinta,kaman innan tasan mai take ayyanawa a ranta tace,
"Babu abinda zan miki na cutarwa kawai inaso na taimaka miki ne,sannan banaso kimin karya saboda koda kinyi zan gane hakan kinji"
Duk maganar cikin lallami takeyi mata tareda kwantar mata da hankali wanda hakan yasa cikin sanyi rai fahreeyah ta bata dukkan labarinta,cikin shashshekar kuka saboda tuna mata da tsohon mikin da yake cikin ranta,na ummanta da kuma mijinta harma da sareeenah.
Innan ceh ta jawota ta rungumeta a jikinta tana bata baki tareda rarrashinta,wanda itama saida kwallah ta zubo mata saboda tsabar tausayin rayuwar fahreeyahn .
Cikin satin inna tafara hada wani magani daban tana bawa fahreeyahn wanda ko yaushe take shansa lokacin dazata kwanta.
Murnace tafara cika fahreeyah da taga cewa zazzabin da keyi yanzu yafara denawa,saidai wasu canji da take ji ajikinta amma duk da haka tasamu sauki fiye da ,yau ma wankan maganin tayi tareda da sha inda har tayi bacci ta tashi bata ji alamar wani zazzabi ba,da safe murnarta cike da fara'a tasamu inna a bakin bukkar tana dafa musu abinci take fada mata,
"Inna kings yau kam koh zazzabin ma banyiba saidai cikina naji yayi dan tauri ta nan"
Tafara tana danna kasan cikinta,murmushi inna tayi mata tareda jijjiga kai itama tace,
"Gaskiya mag an in yayi kyau haka akeso ai ,yanzu sai kijo kici abinci,shima na kasan cikin zai daina kwanannan"
"Ahah Bari na share dakin tukun"
Tafada tareda komawa dakin da Sauri,tana tsaka da gyaranne taji muryar mutane inda ta dago idon ta dan gani su waye,mutanen da bazata taba mantawa a rayuwarta ba idonta yayi arba dasu,wato wanda suke kula da kurkukun da take,😯
"Na Shiga uku tafada tareda tafeckirjinta tsintsiyarvda take hannunta kuma ta fadi kasa!!!!!!¡!!

SADY-SAKHNAceh❤❤❤

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now