Chapter(05)waiwaye zuwaga masarautar saraham

86 14 0
                                    

  (¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

    written by sadi-sakhna

  ......Dedicated to proficient writer association........

(05)

Lokacin da sarki shamam girma yazo masa saiyazamana yafara tunanin sauka daga kan mulki dan bawa dansa huruddeen shima damar baje tasa fasahar a fagen mulki.
Koda ya sanar da dannasa gudurin sa sai yanuna bai amince da hakan ba ,wanda saida ya fahimtar dashi kana yakarbi kudurin mahaifinnasa.
Al'amarine yakankama na bikin nadin sarautar sabon sarki a kasara saraham wanda take daya tamkar da dubu a dukkan fadin duniya.
A bangare daya kuwa babu wanda yakai gimbiya zulaikah farin ciki domin a ganinta tasamu duk wata nasara da take da burin samu a rayuwarta,saboda lokacin tana da karamin ciki wanda sai mutum ya kula sannan yasan da zamansa.A dukkan hidima da ake da kuma shirye shirye babu wanda yakai gimbiya zulaikah narka dukiya dakuma tanadin ranar nadin mijinta akan karagar mulki,a ganinta dole ne tafikowa a cikin taron duk dama allah yayita da san mulki dakuma mallakar kowa a karkashinta.
Gimbiya zulaikah ya' ce ga wazirin masarautar saraham wanda yashiga yafita har saida yayi nasarar hada yarsa da yarima huruddeen domin wani nasa kudurin da ba wanda yake da masaniya akai ,a fada lokacin da sarki shamam yayi niyyar murabus wazirin sa UWAISU yafi kowa bada baki akan kar hakan ta faru saidai lokacin da ya koma gida yasanar da matarsa SARAAHAH wato mahaifiyar gimbiya zulaikah sai yazamana sun fi kowa farin ciki da hakan,waziri uwaisu ne yakalli matartasa kana yace.
"a yau ina farin ciki sosai ,lokacin damuka dauka na burinmu yacika yazo,matakin nasara yana tare da mu ,da sannu ragamar wannan masarauta zata dawo jinina watarana"
"hakane kam domin a halin yanzu yar mu zulaikah na dauke da yaron ciki kaga idan ta haifi da namiji sarauta ta dawo jinin mu gabaki daya,dasannu zamu mamaye wannan masarsuta da kadan kadan "
kallon matar tasa yayi data gama goya masa baya da bayanin dayayi kana yayi murmushi gefen baki mai dauke da mugunta.
Ranar da takama ranar nadin sarki huruddeen sai yazamana maimakon wanda za,a nada yayi farinciki sai murnar takoma ga iya matarsa da danginta ,wanda a zahiri kuma kowa zai dauka tamkar basa farinciki da hakan.
Bayan angama nadine a fada ,sarki shamam mai sauka daga kan mulki yafara bayani kamar haka:
"hakika yau ta kasance ranar farinciki a gareni da allah yabani ikon mika wannan mulki ga dana wato huruddeen,ina yiwa daukacin dukkan al'ummata farinciki dasamun sabon sarkinsu wanda zai shigaba da mulkarsu har zuwa yanda allah zaiyi,kai kuma inajan hankalinka daka dora akan adalcin da wannan masarauta tasaba yi harma dakuma kara kokarinka akan yanda kasameta,saidai kafin na rufe jawabina ina mai sanar dakai cewar nayimaka zabin iyali ta biyu wato gimbiya SAFEENAH  wanda take ya ga daya daga amintaccen sarkinmu wato sarki URWATU,wanda za'a daura a yanzu ,domin bai kamata sarki kaman na nahiyar SARAHAM yakasance da mata daya ba ,dan haka ina mai tayaka farinciki dasamun wannan dama na auran gimbiya SAFEENAH "
Koda yagama bayaninsa sai a take waje yadauki sautin muryar mutane na taya sabon sarkinsu wato huruddeen samun wannan nasarori a rana daya.
A bangaren waziri uwaisu kuwa har akagama hidimar daurin auren sarki huruddeen da gimbiya  safeenah baiyi koda tari ba ,domin abin yazomasa a bazata yanda bai taba tsammani ba.
A cikin gida kuwa gimbiya zulaikah wanda yanzu takoma sarauniya zulaikah kuma mata daya tak awajen sarkinnata zaune take akan kujera tana wani shan kamshi agaban mutanen data gayyata domin su tayata murnar wannan rana ,a inda gefe daya kuma bayinta suke yabonta da kalmomi masu sawa duk wanda aka amdata masa su cewar yafi kowa a fadin duniya.
suna cikin murnar ne wata baiwa tashigo da hanzarin ta ,takai bakinta ga kunnen sarauniya zulaikah tana me rada mata wani abu da mu bamu ji mai aka fada ba,wani irin zabura tayi ta mike daga kan kujerar datake tana wani kumbura kamar maciji, fuskarta kuwa dauke take da wata irin razana kaman an aiko mata da sakon mutuwa,magana tafara cikin daga murya wanda har saida muka razana mu masu rahoto(ummu najma uwar tsoro canna ganta ta buya a bayana tana leko kai kaman kace fittt ta tsere da gudu)...
"hakan bazai taba yiyuwa ba domin nice ta farko kuma ta karshe a wajen sarki huruddeen ,bazan taba yadda wata tashigo gonata ba,idan kuwa har tayi garajen hakan to hakika sai ramin maciji yafi mata kwanciyar hankalin zama fiye da cikin gidana ,kin tafka babban kuskuren shiga gonata ko ke wacece ,inaaaa bazai yiyu ba dole a katse wannan auren dan ban amince dashi ba,bazai yiyu baaaaa"
wani irin numfarfashi take wanda har saida yasa mutanen dake wajen bajewa batare da sun shiryaba ,inda ita kuma uwar gayyar tai cikin turakar ta a fusace....nina ce madallah ,ni gani nasan waje ,harda gayyatar mamar faruqu rakiya ita da ummu najma ,amma ko yar kazar basu yaga musu ba ,tsabar rowa 😊😊😊. 
koda ta nufi dakinta,daukar alkyabbarta tayi tai hanyar  bata zame ko ina ba sai hanyar wajen inda bayinta da dakaru ke biye da ita a baya ,harara ta tsaya ta daga musu ,wanda har saida tasa hantar cikinsu kadawa dan tsoro ,ja sukayi suka tsaya daga bin bayanta ,yayinda tayi wucewarta zuwa gidansu .
shigarta gidannasu ne ta tarar da mamar ta tsaye ,bude bakinta tayi zatayi magana sai takatse yar tata tahanyar nuna mata daki ,wato ta shiga ciki,shigewa tayi inda tasamu babanta a zaune yayi shiru kaman yadaina motsi ,zama tayi a gabansa fuskarta a jike da hawaye ,tana ayyanawa a ranta kenan abinda aka fadamata gaskiyane,batasan maganar ta ya fito filiba saida taji mahaifinnata yana fadin ,
"tabbas abinda kikaji da gaskene babu karya a ciki ,dan a gabana hakan tafaru ,ban taba tsammanin ko wani ne yace da shamam ya aurawa dansa wata matar zai aminceba bare kuma shida kansa ,hakan yaban mamaki ,nayi tunanin yadauki ya' ta kaman yarsa ashe bahaka bane ,wai to yaushe suka hada baki da wancan sarkin ne bansaniba ?hmmmm ,saidai ki kwantar da hankalinki hakika shamam yasaya wa gidan sa tashin hankali da kansa ,domin kuwa bazan taba bari abinda suke tunani yakasance ba,inaso kibude kunnuwanki ki saurari mai zamu fada nida mahaifiyarki a halin yanzu"............
    kuka sance dani a chapter ta gaba 😊😊😊😊
   

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now