Chapter (07)Sabuwar rayuwa 👼

65 10 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

(07)

Share hawayen daya fito daga idonta tayi ,,kana ta gyara zamanta domin fuskantar sabuwar tafiyar dazasu tsinci kansu a ciki ,duk da dauriyar da zuciyarta ta kudurci niyyar yi ,amma duk da haka hankalinta a tashe yake domin bata san mai zata riska a wannan sabuwar rayuwar ba ,da haka suka yi ta keta garuruwa da kuma hanyoyi har ta kaisu ga isa ,nahiyar saraham,tun daga yanayin kananan garuruwan da suke farko farkon nahiyar ,hakan ya tabbatar musu da cewa tabbas sun shigo babbar nahiyar ,da babu kamarta.
Wasu irin dakarune masu yanayin halittar karfi ,suka fara zuya karafan dake jikin kofar shiga masarautar domin bawa gimbiya safeenah damar shigewa ita da tawagarta ,yanayin yanda kofar take budewa shiya zamo abin kallo ga tawagar ,saboda girma dakuma tsari na masarautar.
  koda suka isa masarautar basu zame ko ina ba ,sai sashen da aka tanada a al'adarsu na saukar duk wata amaryar data shigo gidan sarautar.
  Tun daga bakin sashen da aka sauke su suka tabbatar wajen ya hadu matuka ,inda aka saukar da amarya daban haka sashen da bayinta yake daban ,shkma maza daban mata daban ,sannan inda masu tsaronta suke shima daban.
  Baiwa daya ce a wajenta itace sameerah ,wanda dama tun tasowarta ko yaushe tare suke ,gimbiya safeenah ce ta yaye mayafin dake kanta kafin tace ,"sameerah shin ke wani irin yanayi gameda wannan masarautar ,gaskiya har yanzu zuciyata a raunane take da wannan sabon waje dana tsinci kaina a ciki"
  "ya shugabata hakika dole zuciya zata ji rauni kasancewar ta a wajen da bata mafarkin kasancewa ,sai dai duk wanda yadogara da allah to lallai allah yana tare da shi ,sannan dun rintsi mu ma zamu kasance tare dake ,a wannan waje batare da mun juya baya ba inshaallah "
"nasan zakuyi hakan sameerah sai dai ..............." bata kai ga karisa maganar ta ba ,suka jiyo maganar wasu mata daga bakin kofar suna neman izinin shigowa ,sameerah ce ta kalli gimbiya safeenah ,kafin ita kuma tayi mata alamar tace su shigo,ai kuwa kamar jira take ,ta daga murya tare da fadin,
"izini ya karbu daga wajen gimbiya sannan kuma sarauniya a wannan masarauta mai dumbin daraja"
  koda jin furucin sameerah dasukayi ,sai suka fara shigowa ,daya bayan daya suna jeruwa a gaban gimbiya safeenah bayan sun gama shigowa ne suka rusuna gabadaya a gabanta su goma shabiyu ,yan mata ne masu kyawun halitta ,gabadaya fatar jikinsu kyalkyali take duba da yanayin halittarsu ,sannan kuma kayan jikinsu dukka iri dayane ,hakika wannan yan mata sun hadu sosai ,daya daga cikinsu ce tafara magana ,kuma da alama itace shugabarsu saboda yanayin shigarta ya fi nasu kayatuwa,
  "laleh mar haba ya shugaba ta dazuwa wannan masarauta ta saraham ,kuma sarauniya kana kuma amarya ga mai girma sarki huruddeen,hakika idan za'a bamu dama ,zamu gabatar da kanmu a matsayin wani rukuni na  bayin wannan masarauta wanda suke da alhakin kula da duk wani nau'in kwalliya na jinin sarautar saraham ,a yanzu ma idan sarauniya bazata damuba ,mun zone mushiryata cikin kayan ado na al'adar wannan masarauta domin fita da ita zuwa ga sauran bangaren wannan masarauta"
kara sunkuyar dakai sukayi lokacin da shugabarsu tagama jawabinta ga gimbiya safeenah ,uhmmm tunda suka fara bayanin sameerah ta tsiresu da ido ,yayinda gimbiya safeenah kuwa idonta yake kasa tun kallonsu da tayi na farko,sameerah ce ta yi gyaran murya kafin tace,
"shin sarauniyar saraham ta amince da bukatar wannan bayi na kwalliya ?"
sai a sannan ta dago kai ,kafin tace" ba matsala zasu iya fara aikinsu "cikin sanyin muryar ta.
Bayan sun ji abinda tafadane suka fara fitar da wasu abubuwa kala kala ,take yan matan suka rabu gida uku kowanne layi da aikin da zasu aiwatar ,wani rukuni ne suka shiga bandaki ,kafin suka fito ,domin sanar da ita cewar ita suke jira domin fara wankan sarauta ,tashi tayi cikin sanyin jiki ,yayinda wasu acikinsu suka matso domin tayata cire kayan dake jikinta ,saida yazamo daga ita sai farin mayafi iya girjinta ,shiga tayi cikin ruwan da aka tanada domin wankan ,turarene kala kala acikin ruwan wankan banda wanda ake shafeta dashi dakuma wasu fulawoyi da ake mulkawa a jikinta ,sai da wanka ya kammala kafin masu kula da kayan shafe shafe suka fara nasu aikin ,bayan suma sun gama tasu fasahar sai kuma masu kula da ado dakuma sutura ,cikin kan kanin lokaci aka shirya gimbiya safeenah cikin kaya mai matukar kayatuwa ,sannan suka ja dabaya tare da rusunawa suka bar dakin ,sameerah ce tashigo bakinta asake domin ganin irn haduwar data yi ,dama kuma ga ga kyau ba karya ,bayan fitarsu da dan lokaci kadan kuma ,sai ga wasu rukunin bayin suma sun shigo ,saidai su sun fi na baya dan manyanta sannan masu da adon kaya kaman na farkon ,suma gaishe da ita suka yi kafin suka nemi izinin ta wajen fita ,domin ganawa da mutanen gidan sarautar.
Bangaren mahaifiyar sarki aka fara kaita wanda ta manyanta sosai ,kasancewar ta dade kafin ta haifi huruddeen ,basuyi wani dogon surutu ba kasancewsrsu dukka basuda wani surutu ,fatan alkairi tayi mata kafin sukayi sallama ,sashen sarauniya zulaikah suka wuce kasancewar matar sarki shamam ta biyu ta rasu bayan auro zulaikah da lokaci kadan ,tun daga hanya gimbiya safeenah ta jinjina karfin mulki na sashen sarauniya zulaikah ,domin to ko ina dakarune majiya karfi suke aikin tsaro ,kana kuma da bayi kala kala cikin kaya daban daban kowane da aikin da suke aiwatarwa ,bayan isarsu bakin kofa saida aka nemo izini daga wajen hakimar kafin suka samu damar shiga falonta na farko wanda shima tsaruwarsa tafi gaban kwatance ,zama tayi akan kujera yayinda sauran bayi kuma suka zauna a akan shimfida ,domin sauraron isowar babbar sarauniyar .
Can bayan wani lokacine suka ji takunta daga babban falonta tana fitowa ,wanda saboda shanya su datayi ,duk hakurin gimbiya safeenah saida taji ranta yabaci da abinda yayar tata tayi musu ,takowa tayi cikin takama gamida kasaita,tana tafiya bayi na tare mata rigarta saboda kar ta fadi ,saida ta iso har kujerar dake kallon gimbiya safeenah kafin ta zauna ,duk wannan abinda ake sarauniya zulaikah bata kalli inda sarauniya safeenah take ba ,saida tagama gyara zama tare da dora kafa daya kan daya ,kafin ta dago da idonta ta kalli inda sarauniya safeenah take ,zare ido tayi game da razana saboda .............

     SADI -SAKHNA ce 😊😊😊

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now