Chapter (20) Zazzabin dare kuma??

57 9 1
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(20)

Fahreeyah ce a tsaye kamar mai tunanin wani abun, maganar da Sareenah tayi ne ya katseta daga tunanin da ta tafi,
"Meyasa kika samu waje haka kika tsaya,tun ban fara baki labarin ba"
Tunanin tane yadawo mata hakan yasa tayi saurin boye mamakin ta tareda barin koma menene a cikin zuciyar ta,komawa tayi ta zauna tareda cewa,
"Eh kiyi hakuri nadan tafi wani tunanine,cigaba da ban labarin ina jinki"
"Toh nayi zatan ai wani abune yasame ki shiyasa"
Toh kaman yanda mukayi bayani a baya na wannan masarautar mai suna BAHMEER,bazan baki labarin yarima saheel sosai ba saboda abinda ka iya zuwa ya dawo saidai abinda nasani nima akansa shine;bashida yawan magana sannan bai fiye shiga abinda bai shafe shiba,baida yawan magana sannan yanada tsayawa akan ra'ayinsa sosai.
Karna cika ki da surutu akansa shikadai, sai kuma na biyun shine yarima Sameer, sai kuma gimbiya NASREEMAH,sai yar autar su NAMEEMAH, dukkan su basuda damuwa sosai,saidai bawa ko wani acikin gidannan na fuskatar hukunci idan ya sabawa bukatar su ko kuma dokarsu, dukkan su uwa daya uba daya suke saboda babbar sarauniya bata haihuwa, Sai yakasance ta rike su tamakar yayan data haifa a cikin ta.
Kasance war babban yarima yayi batan zana ba asan inda yakeba saiya zamo cewa yanzu yarima Sameer shine mai jiran gadon sarauta.
Wannan shine dan takaitaccen abinda zan iya baki game da wannan masarauta sai kuma sauran abubuwan da in muna tare zaki gansu da kanki yau da kullum"
"Nagode sosai da amsamin tambayoyina da kikayi, Allah yabarmu tareda aminci"
"Ameen"
Tashi sukayi tareda uzurinsu na yau da kullum, Sareenah ce ta kalli fahreeyah kafin tace" to bani labarin ki kafin mukwanta"
Shiru taji babu alamar magana daga wajen fahreeyah, hakan yasa ta lekata kafin tace,
"Me yake damunki haka naji kinyi shiru uhm"
Nanma shiru taji babu alamar amsa daga wajen fahreeyah n,komawa tayi dagabanta domin ta juya mata bayane, idonta ne yafito da alamar mamaki matuka,
"Fahreeyah mai yasameki haka naga jikinki yana kar karwa haka,"
Daga kai kawai fahreeyah tayi tana kallon ta batare da tayi magana ba,
"Fahreeyah kiyi magana mana bai kamata kiyi shiruba fah,fada min mai yake damunki"
"Uhmm...kar ki damu Sareenah zazzabi ne kawai zai sauka karki damu"
"Ehh zazzabin ne kar na damu? Tun yaushe kika fara zazzabin to,dan naga dazu kalau kike ba abinda yadameki"
"Yau kwana uku kenan ina yi, kullum dashi nake kwana in na tashi kuma sai naji kamar bantaba yiba, ranar farko nayi zatan zazzabin ne haka,sai kuma naga ya tafi da safe, to jiya ma haka yayimin gashi yau ma kuma ya shirin yimin"
"Zazzabin dare kuma? Toh mai yake kawoshi haka? Sannan kuma kin tabbatar ba abinda yasameki koh?"
"Ni ba abinda yasameni, kawai haka na tsinci kaina, karki dama Sareenah zuwa gobe zai tafi kawai ki kwanta abinki"
"Shikenan amma abin akwai daure kai, yakamata dai asan abinda za'ayi"
Kwanciya tayi akan shimfin Sareenah, yayin da tasake rufa mata kayan ta, saboda sanyin dayake ratsa cikin jikinta, baccine yadauke ta mai wahala.
Washa gari da safe haka fahreeyah ta tashi ba zazzabi a jikinta saidai rashin karfin jiki da take fama dashi, Sareenah ce ta debo mata ruwa tareda kai mata bandaki,bayan ta dawo dakinne ta fada mata,
"Nagode da dawainiya dani da kike Sareenah,hakika ke yar uwace sannan kuma abokiya da ta ke da wahalar samu a wannan lokacin, nagode sosai"
"Kinga kibar wannan maganar haka kije kiyi wankan muje cin abinci saboda kimaida dan karfin jikinki, sannan nagode da fahimtar da kuma yardar ki a gareni"
Tashi tayi taje tayi wanka kafin tazo suka tafi cin abinci,daga can kuma suka tafi zuwa wajen da zalziliyyah take koya musu karairaya dakuma yanayin saka kaya da kwalliya idan an bukace su a wajen taryar baki,
Duk salon da'keyi musu a wajen shiga sukeyi su fita ta bayan kunnen fahreeyah, domin abu kadanne ta fahimta a wajen, saboda har yanzu bata yarda cewa zata bada jikinta wani can bakin masarauta suji dadi ba, hakan bazai taba yiyu wa ba,bayan angama yimusu bayanin daza,ayine kowa yakama hanyar inda zai nufah.
Fahreeyah ce itada Sareenah suna tafiya a hanyar su ta dawowa daga wajen koyarwar zalziliyyah, fahreeyah ce takalli Sareenah kafin tace
"Yanzu Sareenah wata rana haka zanje na bada jikina ga wani?
"Eh toh ya mutum zaiyi fahreeyah,dolene ka yarda da kaddara ko ya tazo maka"
"Yanzu kenan kema kin taba taryar wani da jikinki,kema?"
Murmushi tayi kafin tace,
"Fahreeyah babu abinda yafi kaddara,idan akace miki kaddara angama cemiki komai,tabbas na taryi mutane da jikina ba sau daya ba ma kuwa, domin hukunci ne mai tsauri zai biyo baya sakamakon bijirewa akan hakan"
"Gaskiya yanda nakeji bana tunanin zan iya bawa wani jikina a halin yanzu"
"Kidaina fadin haka fahreeyah domin kowa dakika gani ba asan ransa yakeyi ba,saidan dole kawai,dan haka inaso kimanta da rayuwar ki ta baya ki rungumi ta yanzu dan hakan shi zai taimaka miki ki maida komai ba komai ba"
"Shikenan zanyi kokarin hakan amma zuciyata har yanzu bata amince da hakan ba sam,"
Da haka suna cikin tadi har suka zo izuwa dakinnasu,.
Rayuwar tasu ce ta dunga tafiya da dadi da babu dadi,har takai cewa fahreeyah ta samu tsawon sati guda a masarautar BAHMEER,abubuwa dayawa da saba dasu yayin da wasu kuma har yanzu bata ci karo dasu ba,ciki kuwa harda abinda tafi tsoro shine bada jikinta ga wani a matsayin ta na baiwa mai shakatar da bakin masarauta.
Wata rana ne bayan sun gama duk wani abu dazasuyi, inda yakama kusan kwana goma da kenan da zuwan fahreeyah,sakone ya zowa dakinsu cewar an zabi bayi guda uku wanda zasu shakatar da bakin daza, ayi a a gobe,mai kawo sakonne ya zayyano musu wanda zasu kasance a wajen,sunan fahreeyah ne yafito dodar a cikin jerin bayi bayin, yayin da dan tashin hankali ta samu kanta a zaune a kasa

SADI-SAKHNAce

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now