Chapter (16)ke tawace har abada

60 11 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

chp(16)

Jijjigata yafara yi amma shiru babu alamar zata farka daga suman da tayi ,tashi yayi ya nufi bandaki ya hada ruwan wanka mai dan zafi kafin yadawo ya dauke ta kana ya kaita bandaki .
Cikin nutsuwa yake tafiyar da duk wata gaba ta jikinta saboda tsoron sake ji mata ciwo a karo na biyu,wani irin ajiyar zuciya ta saki sakamakon ruwan daya ziyarci fatar jikin ta ,shehsekar kuka tafara a hankali ,wanda hakan ya tabbatar da cewa ta tuna abinda ya faru da ita sannan yanayin jikinta ya tabbatar da cewa ta jin jiki.
Dago idonta tayi suka hada ido da saheel wanda shima dama kallonta yake ,da fuskarsa yayi mata alamar bada hakuri sakamakon har sannan bakinsa yagaza cewa komai ,mayar da idonta tayi ta rufe ,har yagama yimata wankan bata sake kallonsa har ya daukota suka dawo daki ,wata doguwar riga marar nauyi yasaka mata mai shara shara ,kafin yagyara mata kwanciya akan gadonnasu .
kallonsa tayi da mamaki jin yanda yake bata hakuri akan abinda yafaru ,domin batayi tsammanin zai yi magana ba ,
"FARYAH kiyi hakuri da abinda yafaru ,hankalina ya gushe a lokacin ina .......mai ....baki hakuri "
tsayawa yayi da hakurin dayake bata ganin murmushi akan fuskar ta 😊,
"wannan shine1dalilin dayasa kake kauracemin ? saboda kar ka rasa nutsuwarka a kusa dani ? "
"eh.....hh faryah ina tsoron aikata miki abinda nariga na aikata shiyasa bana zama kusa dake .........saidai aikin gama ya gama a halin yanzu wanda nariga na aikata ............."
katseshi tayi da cigaba da yake fada kafin tace ,
"yah saheel ka daina bani hakuri dan ka dau abinda yakasance mallakinka ,yanzu ina cikin farinciki daya kasance ba fushi kke dani ba ,kayine da wani dalili ,tun lokacin dana gane haka da baka cutu har zuwa yanzuba "
mamaki yaji dajin furucinta ,"kenan ta san wani abu akan wannan lamarin "yafada a cikin ransa ,
kaman tasan mai yake sakawa acikin ransa kuwa ,
"nasan kayi mamakin furucina koh ?😊😊,duk da nakasance wacce bata tashin cikin kawaye ba amma mahaifiyata tabani matsayi biyu a wajenta ,na uwa,dakuma na abokiya ,tasanar dani duk wani kalubale dazan fuskanta haske akansa ,hakan yasa lokacin da naji abinda kake aikata min banyi kokarin hanaka ba ,sai kawai na kudura a raina ajiyarka zaka karba a wajenna sai kawai na shirya taryar abinda zai biyo baya a zafin dazan ji ,domin ummah ta sanar dani wata magana lokacin da za'a daura aurenmu da daddare ,
"""fahreeyah inaso ki budemin kunnenki kiji mai zan fada;karki sabawa mijinki matsawar ba sabon ubangiji ya umarceki dayi ba ,sannan karki hana shi jikinki indan yabukaci hakan ,sannan kiyi hakuri da halin dazaki shiga a lokacin ,komai zai wuce watarana """
"hakanne yasa nasaka shi a cikin jerin abubuwan dazasu kasance abin tunawa a rayuwata "
rugumota yayi a jikinsa tare da saka kansa a gefen wuyanta yana shakar iskar data fito daga cikin gashinta ,
"faryah ke ta musamman ce ,hakika duk wanda yasameki a matsayin abokiyar rayuwa ya taki sa'a babba ,nagodee da fahimtar ki a gareni ,KE TAWACE HAR ABADA ,kuma nayi alkawarin baki kariya dakuma kulawa har karshen rayuwata ,zan zauna dake a kowane hali matsawar muna numfashi faryah nayimiki wannan alkawarin "
kara kankameta yayi a jikinsa har saida tayi yar kara ,dagowa ya da sauri tareda tambayarta menene ? Murmushi tayi masa tareda cewa cikin muryar shagwaba ,
"yunwa nakeji ,kuma nakasa motsawa "
"ohh shine dama yasaki yin kara ?
"uhm "
"ni nayi tsammanin ko matseki nayine ai ,bakida matsala idan abincine bari naje na kawo miki ,kar ki tashi kinji ?"
"tohh "
"yawwa sarauniyata "
"sarauniya kuma ? nidin ?"
"eh mana ,karki damu dayawan magana ,baki da lafiya ,bari na dawo yanzu ".
Yinin ranar fahreeyah batayi komai ba domin duk wani abu da take bukata daga fada yake kokarin yimata shi ,idan ta tashi to wani laluririn zatayi shima sai ya taimaka mata ,koda kuwa bata bukatar hakan .
Bayan sati daya da faruwar sabon al'amari tsakanin wannan ma'urata sai yazamana shakuwa da shiga tsakaninsu sosai ,koyaushe suna tareda juna ,yanzunma saheel ne a zaune kan kujera fahreeyah kuma na kitchen tana hada abinci ,batayi tsammani sai jinsa tayi a bayanta ,
"ahhhh yah saheel abincin zai kone fah "
"idan bake kika koneba banida matsala da hakan "
"uhm to kabari na gama tukun "
"idan kuma bazan iya jiraba fah ,kincemin ba yunwa kike ji ba ai ,to idanni kike dafawa ai kinsan ba wannan yunwar nakeji ba ........."
"uhm kayi shiru haka naji toh ",
ajiye abincin sukayi tareda lulawa inda suka ga yafimusu abincin.
Fahreeyah ce ita kadai a cikin gidan kasancewar rana ta fara zamanne ya isheta sai tashi tana zaga bayan gidannasu domin samun abinda zai debe mata kewa ,wani lambu gefe da gidannasu taje ta zauna ita kadai tana tunanin yanda rayuwarta ta sanja daga bakin ciki zuwa farinciki ,murmushi ita kadai take fitarwa daga fuskarta ,wanda duk wanda yaganta yasan tana farinciki ,wata k'ara da tajine yasa tashi da sauri tana waige waige kozata gano daga inane ,kuma da alama muryar macene mai karancin shekaru wanda take cikin tsaka mai wuya ,bin karar take har tazo ga wani waje ta labe tana ganin mai yake faruwa da yarinyar,wasu mazane masu jikin karfi suka daddaureta wani kuma na dukanta akan sai ta tashi .
Azabar da taga ana ganawa yarinyarne yasata rufe bakinta domin kar muryarta ta tona mata asiri ,jikinta ne yafara rawa har takai ga tazame daga inda take tsaye ,karar faduwarta ne yajawo hankalin mazan daga inda suke ,itama kuma a lokacinne ta dago da niyyar tashi daga wajen ,idanuwansune yahadu da nata ,inda tayi sauri juyawa da gudu ,amma kashh domin kafin takai ga barin wajen har suncimmata cikin zafin nama irin na yan maza.
Tsayawa tayi tana karemusu kallo cikin tsoro ,ganin yanda suke zagayata kamar sun samu nama ,ja da baya take yi suna kara binta suma ,fuskarsu babu alamar tausayi bare tasaka ran zasuji rokonta idan tayi niyyar yi ,bata gama tunanin mafitar datake kokarin samu ba taji wani abu yadaki tsakiyar kanta ,take wani duhu ya lullube ganinta ta fadi kasa sumammiya ............

SADI-SAKHNAce

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now