Chp(30)karka koya masa mungun hali

57 11 0
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(30)

Hidima da shirye shirye aka fara na daurin aure a masarautar amma ba ango,abinne yabawa kowa mamaki ciki kuwa harda sarauniya zulaikha wanda duk tambayar da ta yiwa mai martaba yaki bata amsa gamsashshiya said ce mata kawai yake ta zuba ido ta gani,saida aka gama shirya komai kafin dogaren da ya aika suka dawo tareda cemasa sun samo inda yarima amam yake har sun isarda sakon sarki a gareshi dan har ya iso yana yankin cikin nahiyar sardaham.
A bangaren yarima amam kuwa tare suka dawo shida abokinsa yarima saheel wanda sun dade dama da haduwa tun a garin bargudu, koda ya shigo kasar tasa ta gado bai zame ko ina ba sai sashen sa inda ya samu angyarashi kaman dama yana zaune a cikinsa tsawon shekara daya da yayi baya nan.
Masauki yabawa abokinsa wato saheel wanda shi yayi niyyar yin gaba zuwa wata nahiyar daban,amam ne ya talasta masa dole ya zauna,tunda dama shi a masarautar su ba nemansa ake ba shiyayi niyya ya barta da kansa saboda wani dalilinsa.
Bayan sun hutane yarima yasa kayansa kamar kullum yanda yake a masarautar wato fararen kaya wanda suke fito da ainihin kyansa,takawa yake a hankali tareda nufar sashen mahaifiyar sa,duk wanda baisan da dawowarsa ba kawai tsugunnanwa yake yana gaisheshi da Mamakin yaushe yadawo,babu wanda ya amsawa gaisuwar saboda yanda fuskar sa take dauke ta yanayi kala kala masu wuyar fassara,har ya isa sashen sarauniya safeenah mutane basu daina mamaki ba kowa da abinda yake sakawa aransa.
A bakin kofar falonta na karshe yatsaya wanda zai sada shi da ainihin dakinta,yatsaya zaiyi magana kenan sameerah tayi saurin cewa masa yashiga tana ciki,shima gyada kai kawai yayi ya shiga.
Wani zan ajiyar zuciya safeenah tayi tareda juyowa da sauri ta rungume danna ta,shima rungumeta yayi da sauri tareda fashewa da kuka ,wanda yataru masa a zuciya na abubuwa da dama,sundade a haka tana shafa bayansa itama tana share kwallar da take zubowa daga idonta,banbareshi tayi daga jikinta tareda rike fuskarsa a tafukan hannun ta tana kallon cikin idaniwansa,babu abinda take haskowa a cikin idonsa sai kadaici,rashi da kuma damuwa,wani Murmushin takaici tayi kafin tace,
"Meya Samu gwarzon dana yake kuka haka kaman sanda yake shekara bakwai,uhmm?"
Dagowa yayi ya kalli idonta kafin yasake rungumeta da karfi,tareda kiran sunan ta cikin raunin murya,dan a lokacin shikadai yasan me yake ji a vikin zuciyarsa ,Wanda babu abinda yake matukar bukata daya wuce ya jishi a jikin ummahnnasa,shiyasa ma ya amince da dawowar lokacin da yaji sakon mai martaba,
"Sokake ka karyanine yakamata ka barwa Y'ayanka suma waje su samu koh"
Sakinta yayi kafin yaja hannunta suka zauna a bakin gadonta,
"Ummah kina lafiya kuwa naga kin rame sosai?"
"Taya kake tunanin lafiya ga uwar da aka rabata da danta na tsawon shekara guda batasan kuma wane hali yake cikiba"
Riko hannun ta yayi cikin nasa kafin yafara magana cikin lallashi,
"Haba ummah yanzu fah ni ba yaro bane yakamata kisaki ranki ina lafiya sosai"
Hade fuska tayi kafin tace,
"Kana tunanine zan sake bari ka tafine?toh kasanja shawara ko lafiya kake ko akasin haka ba inda zaka sake zuwa dan ban yadda kasake haura wannan nahiyar ba koda bana kallo,sannan duk abinda mahaifinka zai fada ka amince dan ni na amince,saidai idan kuma kanaso kasake nesanta dani kasaka ni cikin damuwa"
Karisa maganar tayi cikin damuwa sosai,
"Ahah ummah hakan ma bazai faruba inshaallah ki daina damuwa sosai,bari na kawo miki abinci ki ci"
Yana gama fada yatashi domin karbowa abincin a wajen sameerah.
Hakan kuwa akayi lokacin da mai martaba yakira yarima amam da zancen auren daya yi shirin yimasa ,amincewa kawai yayi batare da ya tambayi wani bayani akan matarba saboda yaji kashedin da mahaifiyar tasa tayi masa,shima a bangaren sarki huruddeen bai fada masa komai ba daga haka zancen ya wuce.
Sashen sarauniya zulaikha ya nufah saboda safeenah tace yaje ya gaisheta,yana shiga ya sameta a zaune ita da munneer,matsawa yayi ya zauna tareda gaisheta,wani kallo tayimasa kafin ta amsa ciki ciki,mika hannu yayi da niyyar kamo hannun manneer da niyuar jawoshi kusa dashi.
Zulaikha ce tayi saurin janyeshi tareda cewa,
"Ahah barshi yana jin magana,kuma a nutse yake kar yaje yakoyi guduwa daga gida idan aka saka shi a abu ko kuma ya koyi bakin hali,zan ga taya ma mai irin wannan halin wai zayyi mulkin sardaham"
Shiru yarima amam yayi yana mamakin furucin matar babannasa,ganin abin bazai kaishiba kawai yayi mata sallama yafita.
Kaman jira takeyi yana fita ta dauko alakalami ta fara rubutu kamar haka:
Salam
Neelah kinga abin mamaki kuwa,wannan dan matsiyaciyar yadawo fah ,kuma sumul yake babu alamar yanzu yana tsanar kasarsa da kuma aure,saboda ana yimasa zancen aure ya amince,kawai dai shi babannasa ne maganin bai sau shiba,dan anfada min bai wani yi doki dawowarsa ba.
Kai wannan matsiayatan mutanen jinake kaman na kashesu duk na huta,koyaishe saina yi shiri na sai su rugujeshi nan take,in akwai wani abunyi maza ki fadamin.

                                        Ummanki.
Ninke wasikar tayi  tareda kiran wani amintaccen bawanta wanda take aika ta bashi sakon da doki ya kaiwa yar ta gimbiya neelah.
Shirye shirye ake ka'in da na'in a Masarautar sardaham yayinda shikuma uban gayya wato ango yake fama da ciwon dashi kadai yasan kasansa,saheel ne yake kokarin bashi baki,wanda shima fama yake da nasa tsohon ciwon a zuciyar,dukkansu abokan kowa ji yake da nasa ciwon saidai ta wani bangaren saheel yana tausaya wa abokinsa saboda abubuwa da suka yi masa yawa,saidai ya boye babu wanda ya sani sai iya yarima saheel din.
  Bikin yarima amam da gimbiya nasreemah a chapter gaba inshaallah, ku ci gaba da bada hadin kai har akai ga ci,da bazar ku nake rawa masu karatu,kar a manta da:
Comment
Following
Like
Share
Please
SADY-SAKHNAceh❤❤❤

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now