Chapter (12)shi wa ?? Wanene shi ???

60 10 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(12)

"wayyo ummaaaaaahhh ki tashi kar ki barni a wannan kuncin nikadai ummah ,kinji "
gunjin kuka take mai cike da ban tausayi tana jijjiga ummannata wanda take kwance kamar matacciya ,wani tunani yazomata ,aikuwa batare da bata lokaciba ta nufi dakinnasu ta dauko ruwa a kofi ,watsa mata take tana cigaba da kiranta .
Wani irin numfashi ta saki tareda ajiyar zuciya ,can kuma saita kalli y'ar ta ta ,tareda tunanin abinda yafaru ,al'amarin daya farune ya dawo musu a kwalkwal warta ,zawo fahreeyah tayi tareda matseta a jikinta tana sakin kuka mai tsuma zuciya ,
"ahah fahreeyah bazan bari ta dauke min keba ,bazan bari ta zefaki cikin wani kangin bautar ba ,bazai yiyuwa ba fahreeyah "
"ehh ummah bazata rabamu ba ,kidaina wannan kukan umnah ,yana sakani cikin tashin hankali "
"shikenan fahreeyah allah yana tare damu ,tashi "
tafada tareda tashi daga inda take zaune ,kama hannun ta tayi sauka tashi kafin suka shiga daki .
Kwanaki sun karu kuma abubuwa sun faru ,saidai duk da abincin da aryana take bawa su huda hakan bai saka fahreeyah tayi kiba ba ,saima sake ramewa datayi saboda tashin hankalin data kara shiga ,ga shi kuma dadin karin abun tahana ta tafita koda nan da wajene ,a ganinta tadaina aikin wuya saboda tasamu kudi dayawa idan akazo siyan bayi .
A bangaren saheel kuwa abin yabashi mamaki dayaga fahreeyah ta daina zuwa diban ruwa tsawon kwanaki ,hakan yasa yafara tunannin anya kuwa lafiya take ?baidai saka abin a ransa ba ,sai yabarshi akan cewar watakila sun sanja mata aikine ,ta koma yin na cikin gida .
Yau ne takama saura kwana uku masu sayen bayi sudawo kaman yanda suka ambata , yayinda fargabar bayin allah wato huda da yar ta ,takaru fiye da mai tunani ,dan har yakai bacci ma kaurace musu yake ,yanzunma zaune suke a tsakar dakinnasu suna tunanin mafita ,huda ce ta kalli yar ta ta kafin tace ,
"tabbas yanzu nafara nadamar aikata kuskuren dana yi ,dana ga yana shirin shafar rayuwarki ,nayi tunanin cewar idan muna cikin wannan bautar in kin girma ke zakiyi aure ki samu sabuwar rayuwa ba irin wannan ba ,ban taba kawo kaina ba ,nidai burina shine ke kisamu ingantacciyar rayuwa ,amma gashi sanadiyyar gangancinmu zaki tsinci kanki a WATA RAYUWA ,wacce tafi wadda muke ciki muni ,wayyo ni da wannan rayuwar"
"ahah ummah kidai na fadin hakan da sannu hakan zaizo da sauki "
"hmm meyasa zakice haka bayan kinsan bamu da mafita "
"akwai mafita ummah ,yacemin akwai mafita "
"shi wa ?wanene shi ?"
"uhm yaya saheel ne ,yacemin akwai mafita ,kuma wai ke da kanki da kuma ni zamu samo mafita ,in muna son hakan yakasance kuma wai ,sai mun daina tsoron rabuwa ,ko nesa da juna "
"a ina kika hadu dashi ?"
"a inda nake zuwa diban ruwa "
shiru huda tayi kaman mai nazari kafin tace ,
"inaso gobe ki saci hanya ki kira minshi ,zamuyi magana nidashi "
"ammma umm ........."
"karki ce komai kiyi yanda nace "
"tohh ummah "
haka kuwa akayi da safe su fahreeyah suka fito fuskarsu babu damuwa mai yawa akan fuskarsu  kaman wanda aryana tace ta janye gudurin ta daga kansu ,ayyukan dasuka san aikinsu ne suka fara ,har huda ta fice domin debo itace ,sai kuma tasaki kara ta zauna ,tana shure shure ,fahreeyah ce ta taho da sauri dan ganin abinda yasamu umman na ta sai kuma taga mamar ta ta gigicewa tayi tana mata sannu itakuma tana kara narkewa ,ganin abinda yake faruwane yasa aryana zuwa kansu tatsaya dan ganin mai yafaru ,
"hmm munafukai ,saiki tashi kiban waje ai ,ke kuma (tafada tana nuna fahreeyah )sai ki tashi ki debomin itacen ,kuma idan kinga dama karki dawo nasa abi bayanki ehe "
kallon mahaifiyartata tayi sai gani tayi ummah nata tayi mata alama da ido ,hakan yasa tagane duk shirine domin taje ga inda ta aiketa jiya .
Juyawa tayi ta fita daga gidannasu ,batare da tsoron hukuncin da aryana zatayimata ba ,tayi hanyar gidan saheel domin isar da sakon mahaifiyartata ,domin tasan wannan aikan yanada alaka da rayuwarta ,tafiya take tana tunani a zuciyarta har ta iso ga gidan saheel din ,tsaywa tayi a bakin gidan tana tunanin tashiga ko ta tsaya .
Tana tsayenne taga fonee yafito daga gefenta ,nufarsa tayi tana tambayarsa dauke da murmushi akan fuskarta ,tana tsugunne ne ,taga saheel shima yafito daga inda fonee ,kallonsa take batace komai ba yayinda shima yake kallonnata ,ganin hakan zai ja musu lokacine yasa ta fadin ,
"uhm ya saheel ina kwana ?"
"lfy kalau ,da wata matsalane ?"
"ehj dama umma ce tace nafada maka tanaso kuyi magana da ita "
tafada fuskarta tana fitar da hawaye ,matsowa yayi kusa da ita kafin yace ,
"menene yake faruwa faryah ,kifadamin ?"
labarin abinda yafaru ta fadamasa tana share hawayen daya fito daga idonta ,jijjiga kai yayi dauke da damuwa akan fuskarsa kafin yace ,
"shikenan kice mata zan zo da daddare saboda idon mutane tunda batason a sani "
"to 😩"
"ki kwantar da hankalinki kinji komai yana zuwane yanda aka tsara shi "
"shikenan ya saheel nagodee "
juyawa tayi ta tafi zuciyarta cike da kunar rai ,sauri tayi ta hada itacen da aka aiketa kafin ta dauka tatafi gida .
Aikuwa batayi mamaki ba saida tasha na kullum wato zagi ,shigatayi wajen mahaifiyarta datake kwance a daki sannan ta fada mata yanda sukayi saheel din .
bayan gari yafara duhune haske ya fara daukewa daga kallon mai kallo yayinda fahreeyah suke zaune suna jiran tsammani ,fonee ne yashigo dakin yana shafa kansa a jikin fahreeyah ,huda ce ta zabura zata gudu ganin abu yashigo ,saidai kuma abin ya bata mamaki ganin yanda fahreeyah ta shagala tana shafashi ,daga kai tayi ta kalli mamar ta ta kafin tace ,
"ummah ya zo ,yana waje "
tashi sukayi suka fita wajen gefen dakinsu , samunsa sukayi yajuya bayansa ,fahreeyah ce ta fara magana ,
"ya saheel "
juyowa yayi tareda gaisheda da ummar tata ,wato huda ,shirune ya wuce a tsakaninsu kafin huda tace ,
"ina so kubiyoni muje wani waje yanzunnan "
binta sukayi batareda musu ba ,sunyi tafiya mai nisa cikin garin kafin suka zo wani gida mai dan rufin asiri ,saidai kuma kaman gidan mutum dayane .
Juyawa tayi tana kallonsu dauke da murmushi yayinda suma ita suke kallo dauke da mamaki ,kallontane ya koma kan saheel ,
"saheel ina so ka ............"

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now