Chp (24)ehhhhhh!!!!!😲

53 10 2
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(24)
Kallon su kawai ta tsaya tanayi,duk da cewa bata nuna ba amma yanayin ta tabbatar ta girgiza da abinda taji daga garesu,idonta ne yakai kan wacce tayi mata magana daga farko da alamun tafi sauran dan dama daga yanayinta,
"Shin me like nufi da cewa gidan ukuba?"
Murmushin takaici tayi dajin kalar tambayar da fahreeyah tayimata kafin ta bata amsa'
"Duk abinda zan fadamiki ba lallai ki sani ba saidai inaso kisani cewa,babu banbancin dare ko rana a wannan wajen sannan taka maimai hukuncin daya kamata a miki na dadai da laifinki wanda aka ga dama za'a miki,abinci kuma za'a dunga baki duk bayan kwana biyu ruwa kuma bayan kwana daya,baruwansu da rashin lafiya koh laluri saidai idan kin mutu a jefarki a jeji saboda kar ki damesu da wari,sannan babu wani tausayi daya taba wanzuwa a fuskar wani ma'aikaci anan wajen,kuma............"
Days daga cikin wanda basuyi mata magana ba ce ta dunguri wadda takeyi mata bayanin tareda cewa,
"Saleeerah taka mata kiyi shiru haka ,sauran abubuwan zata gani da kanta ai,ko so kike ki karar da dan karfin da muka samu bayan munci abinci akanta,?"
Shirun tayi kuwa alamun taji bayanin da daya matar tayi mata,bata sake magana ba saima juyawa da tayi ta koma daya gefen ta zauna,shiru ne ya ratsa cikin wajen yayinda bayan wani dan lokaci sai su juyo su kalleta kafin kuma sai juya.
Wata irin kara mai tsananin kara da kuma tausayi ne ta ratsa kunnensu wanda hakan yasa fahreeyah firgita har saida ta tashi tsaye batare da tasani ba,kallon fuskar su tayi amma taga babu alamar wani razana a garesu,hakanne yabata alamar cewa kenan sun saba da jin irin wannan karar,wai!!!.
Kasa jurewa tayi hakan yasa ta tambayi wacce tayi mata magana da tazo wajen wato SALEEERAH,
"Wannan kuma wace irin kara ce haka?"
Da kamar bazata amsa mata ba sai kuma tace,
"A kurkun gaban mune ,an kama wani dan leken asirine shine yayi taurin kan fadar waya aikoshi,jiya an cire masa hannu guda daya yauma kuma suna cire masa dayan shine kawai"
"Kawai!!! kuma?sai a cirema masa kuma Bakomai bane a wajensu?"
Dariyar dukkansu suka sheke da ita kafin dayar data hana saleeerah magana tace,
"Kina nufin kice baki taba jin labarin magarkamar cikin kasa bane?koda a kasar ku?"
Kallon su fahreeyah tayi da alamar tambayar su kafin ta jijjiga kai alamun bata sani ba,saida suka yi shiru kafin dayar ta tambayeta,
"Abin mamaki baki san labarin irin wannan wajen ba,amma wane irin laifi kikayi aka kawoki wannan wajen,kin yi kokarin kashe sarki ne?,leken asiri aka turoki daga wata kasar ko kuma hada baki kikayi da wani domin jawo silar yaki?ko kuma............."
Bata gama koro bayanin ta ba fahreeyah tayi saurin rufe mata baki tareda girgiza kai jikinta har rawa yake,
"Ahah ahah ahah,ban.....taba .....kkkki...saba,kawai gimbiya nameemah ceh ta kamani da mijin dazata aura ,wata yar wajen da muke tare ceh ta sakani na je ashe bahaka bane shine tayanke hukuncin a kawo ni nan dan na amshi horona akan hakan"
"Eeeehhhhhh"
Dukkansu suka fada a tare kaman ance musu ga nan aljani a bakin kofarsu.
"Kina nufin kice iya wannan laifin kika aikata ta bada umarnin akawoki nan,kuma babu wanda yayimata magana akan hakan,to ai ko wanda ya aikata yafi naki za a kawoshi nan wajen ba,gaskiya ba'a zartar miki da hukuncin daya dace ba sam"
Har saleeerah ta gama bayanin ta suna jijjiga kai saboda Mamakin abinda suka ji anyiwa fahreeyah,ganin da tayi sun dulmiye cikin Labarinta yasata karsesu tareda cewa,
"Naga kina ta Mamakin abinda nayi aka kawoni nan wajen amma ku toh mai kuka yi aka kawo ku nan wajen?"
Shirun sukayi kowa tana kallon kowa kafin saleeerah ta yanke hukuncin fada mata,
"Gaskiyar magana ni turoni akayi leken asiri daga kasarmu,basai kinji inane ba an kamanine lokacin danake tabb da haura ganuwar garinnan.
Ita  kuma wannan,'ta fada tana nuna wacce tahana ta magana dazu'sunanta leelah ita kuma ana zarginta da taimakawa abokan gaba na yamma da wannan kasar.
Sai dayar wadda tunda kika zo bata miki magana ba ita kuma laifin mu daya wato leken asiri.
Toh wannan shine laifikanmu saidai ana tambayarmu muka bada amsa batare da taurin kaiba ni da leelah,iya waseelah ceh da taki fada suka yanke mata hannu guda daya"
Tana fadar hakan fahreeyah takai idonta kan hannun waseelah wanda aka yanke shi saura gudu lumi,ganin kallon da waseelah taga fahreeyah tana yima hannun ta ne yasata boyeshi a bayanta tana sunkuyar da kai,sauke ajiyar zuciya tayi bayan taji takaicaccen tarihinsu kafin tace,
"Gaskiya abin akwai abin mamaki a cikin,amma yawancin wanda suke wajennan irin laifinsu kenan?"
"Ahah akwai wasu laifukan da dama,dan kurkukun gefen mu su anka masu dasa ka guba ne a cikin abincin sarki",
Suna cikin magana ne fahreeyah taji sunyi shiru suna kallon bakin kofar wajen,saboda ita ta bawa kofah baya bata kalli abinda suka hangoba,saidai jin motsin sawun mutum yayi kusa da wajen na su,sai ta juya sukayi arba da wani mutum kato.
Makulli yasa yabude wajen batareda yace komai ba,ya finciki kafadar fahreeyah yayi hanyar wani lungu mai dan tsawo.
Sun yi mai dan tsawo kafin suka isa wani waje mai jan haske,duk yakushin da fahreeyah take masa tun sanda ya daukota hakan bai sakashi ajiye ta ba har saida yakaita wannan filin tukunna.
Tana tsugunne a wajen har wani mutumi yafito mai dogon gemu har kusan cikinsa,saida yazo daff da ita kafin ya zauna a wata kujera da take gaban fahreeyah,
"Kehh kece karyar da aka kawo dazu kenan,?,dukvda cewa ba nan ne inda za'a kawoki mu karbeki ba,amma ba laifi hakan ma tunda har an bamu cin hanci ,dan haka yanzu inaso ki fadamin gaskiya shin kin aikata kuskuran ake tuhumarki koh kuma a'a,"
Shiru fahreeyah tayi ko dago kanta batayiba bare ta amsa maganar da'akayi mata.
Dara DA mata tsawa yayi sannan yakara da cewa,"ba tambayarki nake ba,toh inaso ki sani cewa ko kin amsa ko baki amsaba dolene saikin karbi horo dan shine abinda nayi alkawarin yi agareki"
"Ehh na aikata abinda suka,ceh nice na je har dakinsa"
Haka takare maganar muryar ta na rawa cikin kunan rai,
"Saboda ke karya ce mai bin mazan mutane koh? Sannan kuma anturoki domin ki lahantashi koh?,sarkin horo,ku mata bulala hamsin da zanen wuta abaya '
Yana gama fadan hakan yatashi yabar wajen,ko waiwayo wa baiyyiba.
Fahreeyah na nan tsugunne har aka suka gama shirye shiryensu ,bata zata ba sai jin zafin bulala tayi a bayanta,haka bulalar tayi ta sauka akan jikinta tun tana karewa har karfinta yagaza aikata hakan.
Abubuwa dayawa ne suka dawo mata a rai,ga zafin Kalmar daya kirata sannan kuma ga zafin abinda suke aikata mata.
Jikinta ne yagaza bata hadin kai lokacin da aka fara danna mata bakin karfen da yayi juwur a cikin wuta a bayanta,inda komai na dunyar ta yadauke daga cikin kwakwalwarta kaman an dauke ruwa.

SADY-SAKHNAceh❤

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now