Chapter (10)ahah bana sonta

71 12 3
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(10)

har gimbiya meelah tafara surutunta ta gama babu wanda yakalleta acikin dakin kaman bata samu mutane acikiba .
Dahaka rayuwa tagara har zuwa ranar bakwai da haihuwar yaro yaci suna SHAMAM ake kiransa da AMAM ,biki akayi na kece raini a nahiyar masoya nata farinciki da samun karuwar yaron ,yayinda a daya bangaren kuma wato iyalan waziri suka yi bakinciki da hakan .
Bayan wani lokaci rayuwa ta gara haka kuma abubuwa sun auku ciki harda harin da ake kawowa yarima amam ,wanda daga bayane aka kebeshi cikin sashensa da bawanda yake shiga sai mahaifiyarsa ko wani na kusa dashi .
Ganin sarauniya zulaikah takasa samun ganinsa bare cutar dashi sai kuma shiga hanyar malami ,inda har tayi nasarar tura masa asirin tsanar mace a rayuwarsa da kuma mulki ,babu wanda yasan yana dauke da wannan sihiri sai wanda yayishi da kuma wanda yasa akayi .
Tohh muje zuwa ...................
           。。。。。。。。。。。CIGABAN LABARI 。。。。。。。。

Daular saraham ta kara samun daukaka da kuma kawatuwa fiye da yanda take a kwanakin baya ,saida na kare cikin fadara da kallo ,anan naji labarin auren gimbiya meelah da akayi ga dan  masarautar KHAIRASH ,wanda ta haifi danta mai MANNEER ,wannan labarin yaban mamaki ,ashedai na dade a tafiyar baya dana yi 😊.
Hankalina ne yatafi zuwa wani arnen gini da'aka yishi da farin dutsi mai walwali ,hanyace mai matuka tsayi ta bi takan wata gada (bridge )daga cikin masarautar har zuwa ga cikin ginin .
  Bakomai bane a wajen ginin idan aka hada da cikinsa a bangaren ,babban falo ne da dakuna ,wajen wasa ,motsa jiki1,wajen hutawa ........komai ma akwai a wajen na more rayuwar dan adam dai ,motsi naji a dakin motsa jiki hakan yasa hankalina yakai wajen ,wani matashin kyakkyawan saurayine a tsaye ,daga shi sai wani farin wando iya gwiwa ,jikinsa kuwa gumi ne yakebi takan fatar jikinsa da take fitar da wani haske mai kyau ,abinda yaban mamaki shine tafiya zuwa labarin rayuwarsa shekara 50,amma yanayin girmansa tamkar dan shekara 25,gaskiya halittunnan suna da abin mamaki .
Tafiya yake yana goge jikinsa ,da wani farin nafkin ,kafin ya wuce cikin wani daki da alama wajen baccinsane ,wucewa yayi bandaki.
Yadade kafin yafito daure da towel ,ya nufi gaban wata drawer da aka jera wasu nau'ikan taure masu matukar kyau ,saida yashafe jikinsa da turaruka kafin ya yasaka wasu fararen kayan masu adon sarauta a jiki ,karar bugun kofane yasashi daga daradaran idanuwansa ya zuba su akan kofar ,yadade kafin yayi wata yar kara da hannunsa alamar a shigo .
Wani bawane yashigo tare da tsugunnawa a gabansa yana cewa ,
"ranka yadade sarki ya aiko ganinka a zaman karshen wata dayake da iyalansa a fada ,"
kada kai yayi tare da yimasa alamar ya fita ,
(tohh shikuma baya magana ne ?),
Takawa yake a hankali bayan yafito daga sashensa kana ya wuce wajen mahaifiyarsa ,bude kofar yayi ya shiga bayin na bashi hanya tare da gaisheshi ,saidai ko kallonsu bai yiba bare ya amsa musu.
sarauniya safeenah ce a zaune a bakin gadonta tana kokarin saka alkyabbarta domin hallarar taro daza'yi,juyowa da kallanta tayi zuwa kan dannata ,zuwa yayi ya zauna a bakin gadon kusa da ita tareda rike hannunta da alamar kulawa ,itama kallonsa tayi tana jijjiga kai tare da cewa ,
"hmm nafara gajiya da halinka amam ,kai shikenan ba dama kayi magana saidai kadinga yin abu da hannu ,menene hakan ,in wani abune yake damunka ka fada mun mana ,bakayin abu ,irinna kowa ,meyake damunka ne ?"
"babu komai ummah ,dafatan kina lafiya ?"
yafada muryarsa cikin sanyi kuma mai matukar dadi ,
"lafiya kalau ,ka tabbatar bakomai ko ?"
ta kara tambayarsa a karo na biyu fuskarta dauke da damuwa ,
"ehh bakomai "
"toh shikenan allah yasa hakane ".
Tafiya suke yi ita da dannata har suka iso ga babban dakin da'ake tattaunawa a ciki ,,kowa samun waje yayi ya zauna,dama su ake jira kafin mai martaba yafara bayani ,
"to barkanku da zuwa wannan taro da'aka sabayi a duk karshen wata domin tattaunawa akan matsalar data shafi kowa ,kowa ina masa barka da zuwa musamman ke meelah dakikazo daga wani waje keda danki ,sannan kowa yasani akan dalilin yin wannan taro bai wuce saboda kai ba AMAM ,(yafada yana nuna yarima amam ),koyaushe akan abu dayane ,yanzu ma inaso kasanar dani abinda ka yanke ,shin ka samu wacce kakeso ?ko kuma ka amince da wacce na zaba maka,?"
"ahah abba bani da wacce nakeso "
"to ka amince da zabina,da auren yarinyar dana zaba maka ?"
"ahah bana sonta "
"kanada wata masalane daya hanaka aure ka fadamana ?"
"ahah "
"hmmm to shikenan idan har wannan shine ra'ayinka ,to koban fadaba kasan hukuncin dana yanke akan ka ,idan baka zo min da amasata ba ko ?"
"ehh na sani abba "
"to shikenan zaka fara shirin barin masarautar daga yanzu na sallameka ,ba zaiyiwu ina mulkar dukkan mutane ba ,kai kuma ka bijireminba dan haka ka barmin nahiyata gaba daya ,kaje inda zaka bi ra'ayin kanka "
yana gama fadin hakan ya buga tebur din dake wajen ya tashi cikin bacin rai yabar wajen ,kowa kallon kowa yake a cikin wajen ,daga baya sarauniya zulaikah ita da yar ta suka kece da dariya harda tafawa ,sarauniya safeenah ce ta kallesu cike da mamaki ,yayinda shikuma yarima amam baiyi mamakin abinda sukayi ba ,saboda bai manta yanda suka yita galla masa azaba ba ,dakuma jifansa da mugan kalamai ba sanda yaro ,dan haka batare da yace komai ba yabar wajen dama shi bayi da surutu dan sai ya yini bai ce komai ba ,itama sarauniya safeenah tashi tayi tafita tana neman tsari daga sharrinsu ,saidai al'amarin yana cinta azuciya sosai duk da juriya irin nata .
"Gaskiya ummah keta musamman ce ,yanzu kinga zaiyi nesa da wannan nahiyar watakil ma yayi rayuwar bauta tunda ankarbe duk wani launi da daraja irin na mutanen wannan wajen ,manneer shine zaiyi mulkin saraham ,da sannu badai jinin safeenah ba "
"hakane gimbiyar saraham ,jinina ne zaiyi mulki indai ina numfashi a cikin wannan masarautar ,tun da munyi nasarar fitar masa shi a cikin ransa ai komai ya kare ................hmmm

      SADI-SAKHNA ce😊

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now