Chp(28)ohhh allah!!!

51 10 0
                                    


(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(28)
Karbar abincin tayi daga hannun khairiyyah n tafara kaiwa bakinta tana taunawa kaman magani,khairiyyah ce ta riqe hannunta tareda yi mata magana cikin muryar lallashi,
"Yakamata ki danci dayawa saboda jikinki yana bukatar abinci sosai,kwananki uku fah baki ci komai ba,jijjiga kai fahreeyahn tayi kafin ta fara kaiwa abincin cikin bakinta da suri baka man lokacin da tafara ciba.
Sun dan dade a wajen har fahreeyah tagama cin abincin tasha ruwa ,sannan khairiyyah ta bata maganin karfin jiki,ganin jikin da dan sauki sai ta taimaka mata ta tashi suka koma masaukinsu.
Sun a Shiga kuwa idon kowa a cikin dakinnmasu yadawo kansu,khairiyyah ceh tayi saurin sakin fahreeyah daga rikon da tai mata sannan ta tayi mata alama akan ta gyara tsayuwarta,hakan kuwa tayi saboda taji abinda khairiyyah tafada mata kafin su shigo din.
Jaliyyah ceh ta tashi daga kishingiden da take kafin ta kalli khairiyyah,
"Keh kuma mai ya hadaki da ita sannan daga ina take tsawon wannan lokacin?"
Gyaran mirya khairiyyah tayi kafin tace ,
'
"Ehh dama a hanyan dawowa daga sashen gimbiya nasreemah na ganta wai taje wajen wadda suka zo tarene,toh sai aka saka su zuwa wani aiki shine bata dawo ba sai yanzu"
"Toh miye kuma naga kona riketa kaman wata mai koyon tafiya?"
"Ahh ta fa dine lokacin da take shigowa shine na taimakamata"
"Toh uwar magana da taimako ita bata da baki saike koh,khairiyyah ki kiyayeni a dakinnan,ke kuma wuce allah yakara da'aka sakaki aikin gobe kuma idan koka sake barin wajennan batareda nasani ba sai kin fuskanci hukunci daga wajen mai horo kinjini koh?"
Sauri daga kai fahreeyahn tayi alamar taji mai tace,
"Vance ki daga min kai ba,magana zakiyi,kike wani sunkuyar da kai kaman wata sabuwar munafuka"
Bude baki tayi a hankali tareda cewa ,
"Naji "
"Toh yarage naki sai ku kiyaye nagaba"
Kowa tashi yayi yakama aikin gabansa,yarage saura fahreeyah kadai a dakin ,saboda har kowa yabar dakin bata matsa daga inda take ba,taka kafarta ta fara tafiya hankali zuwa wajen da aka bata na kwanciya,juyawa tayi ta bawa dakin baya tana kallon bangon dakin tai likimo kaman mai bacci.
Har bacci ya fara daukarta cikinta yayi wani kara wanda koh wanda yake gefen ta zai iya jiyowa,kai wa hannun ta tayi kan cikin dadai inda taji yana motsawa,zabura tayi ta zauna kaman wanda akayiwa wahayin hakan,kara zare ido tayi jin yanda kasan cikinta yake motsawa,wanda har batasan sanda ta fara magana a fili ba,
"Ohh allah Wannan kuma menene,koh kuma maganin da inna kainana tabani ne yake saka cikina yana juyawa? Gaskiya yakamata na nemo wanda inna tace ta sameta idan nazo garinnnan,saboda na tambayeta menene,nasan bazata gagara saniba"
Shiru tayi da surutun tafara taba fuskarta jin zafin da jikinta yafara,sanyine taji yana ratsa jikinta hakan yasa ta koma ta kwanta tareda zanyo rigarta ta kara rufe jikinta.
Saida ta shafe kusan sati amma ba wanda yagane bata da lafiya a dakin,saboda duk kular da khairiyyah take bata babu  wanda yasani,saidai itama batada masaniyar zazzabin da fahreeyahn take a dare ,duk da yana bata wahala amma haka take daurewa,sboda a ganinta iya abinda khairiyyah takemata tayi kokari,bataso tasake dora mata wani sabon abin bayan tayta aikin datake ma.
Yauma a zaune suke itada khairiyyah bayan sun gama goge falukan sarauniya safeenah suna hutawa,khairiyyah ce takalli fahreeyahn kafin tace,
"Amma fahreeyah anya kuwa kin warke?gashi a fili babu wani abu dayake damunki amma kuma ina kulada ke idan kikayi wani abu sai ki fara haki numfashinki yadunga sama sama,kalau kuwa kike?"
"Ahah Bakomai kawai yanayin rashin karfine amma zai daina inshaallah"
"Amma kuma naga kina ta ramewa"
"Karki damu khairiyyah babu komai,kulawar da kike dani ma na gode miki sosai,allah yabani ranar dani ma zan taimakeki idan kuma bana duniyar ina miki addu'ar allah yabaki mai miki"
Kwallah ceh tadan fito daga idon khairiyyah inda tayi sauri ta rungume fahreeyahn,
"Ki daina min godiya har haka,nima ban taba samun abokiya ba sai yanzu,dan duk su Jaliyyah ina zaune dasune kawai,amma yanzu damuka hadu ji nake kaman ke yar uwataceh"
Juyowa da fuskarta fahreeyah tayi tana mata murmushi kuma sai tace,
"Kidaina bata farincikinki da kuka mana,duk da ni nafara bansan zaki dau har haka ba kiyi hakuri"
"Shikenan na daina,yawwa tunda mungama aiki da wuri zo muje mudan zaga na dan nuna miki abubuwa kafin Jaliyyah ta hangomu takara mana wani aikin"
"Toh shikenan mutafi dama inaso nadan zaga"
"Toh muje"
Dasauri khairiyyah ta tashi daga inda take zaune tayi wata hanya da sauri tana dan murmushi kaman ba ita bace take kuka yanzu,fahreeyah kuwa ganin khairiyyah ta bar wajen saida tayi dan yunkuri kafin ta tashi daga inda take zaune saboda azabar ciwo da kasan cikinta yake mata,khairiyyah tana jiyowa tayi sauri ta tashi tareda binta a baya saboda kar ta gane halin da take ciki.
Sun dads suna dan zagayawa inda duk inda suka wuce sai khairiyyah tayi mata bayaninsa saboda idan tazo wajen tagane ya yake,sashen sarauniya zulaikha suka wuce,wanda girmansa yake kama da na safeenah saidai yafi nata yawan bayi dakuma kayatuwa,khairiyyah ceh taza hannun fahreeyahn ta nuna mata wajen kafin tace,
"Wannan shine sashen sarauniya zulaikha wadda itace babbar matar sarki huruddeen sannan kowa yana ji da ita sosai,akawaita da karfin mulki sannan kuma da iko,yar ta dayace kuma itace Y'a ta fari a wannan masarautar wato gimbiya NEELAH tana aure a masarautar KAIRASH,tana da Y'a Y'a biyu,da MANNEER da kuma zulaikha mai sunan mamarta,sannan..........."
Fahreeyah ceh tayi saurin katseta tareda cewa,
"Inaga dahaka da labarin masarautar kika bani khairiyyah idan babu dama dan inason labari irin wadannan"
"Ahh in kina so muje na baki,zakiji labari kam"
Har sun fara tafiya fahreeyah ta dafata tareda cewa amma ina babu wani abu a cikin labarin da akace karkowa yadunga fadawa wasu?"
Shiru khairiyyah tayi kaman mai Tunani sai kuma tace,
"Ahah babu amma mai yasa kika tambaya?"
"Ahah babu komai"
Bakomai fahreeyah ta tunaba sai labarin da sareeenah ta bata lokacin da take masarautar su nameemah,haka kawai ta tsinci kanta da Murmushi lokacin da ta tuna,jijjiga ta khairiyyah tayi tareda cewa,
"Mekike tunanine? Zo muje mana"
Binta tayi a baya suka koma sashen su inda zata bata labarin...toh kubini don jin labarin.
Inshaallah a chapter ta gaba zamu cigaba da labarin masarautar sardaham lokacin da yarima amam yabar gida da kuma aurensa da gimbiya nasreemah,harma da wacce irin rayuwa ake aikatawa a cikin gidan sarautar sardaham din,ku kasance dani.

SADY-SAKHNAceh❤❤

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now