Chapter (23)barka da zuwa cikin ukuba!!

48 7 1
                                    

¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

Chp(23)
Dan tsabar girgiza da lamarin da fahreeyah tayi ,hakan yasa ko numfashin ta kasa furzar shi tayi ballanta kima ta motsa daga kwancen da take ,wani irin duka da taji a cinyoyinta ne yasa ta jan wani ajiyar zuciya tareda sosa wajen daya yi ja alamun dukan yaratsa fatar ta,kunnen ta nameemah ta kama da karfi kaman zata cireshi tare da jan ta waje cikin huci da zuciya,bata zame ko ina ba sai tsakiyar farfa jiyar fadar tareda zefarta a kasa,tattare siket din take jikinta tafarayi tareda rufe sauran jikinta dayake a bude,duk ta tafara jin alamun mutane sun fara taruwa akanta amma hakan bai sa tayi gigin da go kanta ba,saidai duk wata irin kunya ba wacce bata jita ba a wannan lokacin,dan a yanda take ji ko kasa ta bude zata iya shigewa indai mutanen dake wajen idon su zai dauke daga kallonta.
"Kehh kirisah kika ce sunanki ko me ? Je ki kiramin sarkin horo yanzunnan ina nemansa"nameemah ce mai wannan maganar tana kaiwa tana komowa a gaban fahreeyah tareda aika mata harara kaman tana kallonta,"yanzu dan tsabar raini irin na bayi har kin isa ki hada jiki da masoyina?dan kunga bama yimuku ukuba irin na sauran masarautar koh?shiyasa har raini yashiga ysakaninmu daku koh,yau kuwa zanyi misali dake kowa yagani ,nan gaba sai wata baiwar ko bawa yasake taba abinda yake mallakina".
Tana cikin surutunne kirisah ta dawo tareda sarkin horo rike da bulala a hannunsa yana jijjigata kamar daman mai jira,ko magana batayi ba kawai ta nuna masa inda fahreeyah take da hannunsa,alamun yayi ta dukanta har sai ta ce masa yatsaya kenan.
Cikin gaggawa kuwa yafara aika mata tsimangiya a sassan jikinta babu alamar imani,tun fahreeyah na ihuu har ya zamo ba abinda take sai nishi kawai dan azaba,ganin dukan yaki ya tsayawa ne alamun gimbiya nameemah na kokarin barin sarkin horo ya kashe fahreeyah,ya wata amintacciyar baiwarta sulalewa a wajen tayi hanyar turakar sarauniya wato mamar nameemah domin fada mata abinda yake faruwa.Bayan wani lokacine suka dawo tareda sarauniya,tana isowa wajen tafara tambayar me ya faru,shiru kowa yayi a wajen hakan yasa shima sarkin horo ya tsaya da hukuncin dayake yi.
"Nameemah tambayarki nakeyi mai ya farune haka"shiru nameemah tayi har sannan fuskar ta babu alamar ta sauko daga dokin zuciyar da tayi,"kirisah kiyi mata bayanin abinda kika fada min"
Saida tayi kifikifi da ido kafin tafara magana tana sunkuyar da kai kaman wata mutuniyar arziki.
"Eh dama lokacin da shugaba zilziliyyah tace mata ta jira ta bari taje wani waje ta dawo su koma,saboda ita bata samu aikin dazata yiba,nikuma nazo zan wuce saina ga ta hade fuska alamar bata amince da abinda tafada ba,sai naga tafito da wani abu a gefen rigarta tafesa ajikinta,alamun tsimin turare ne tayi amfani da shi ,sai na ga tayi hanyar dakin mai girma yarima,sai da taga ba wanda yake kallonta sai bude kofar ta shiga,shine nikuma ganin haka kuma an hana kowa ya doshi hanyar kofar ,ya sani zuwa da gudu na fadamiki abinda yake faruwa,shikenan abinda nasani ni"
Kowa shiru yayi yana tunanin labarin da kirisah ta bayar tareda mamakin abinda fahreeyah tayi.
Zilziliyyah ceh ta iso wajen sannan da alamun sannan labarin ya isa gareta,nameemah ce ta kalleta tareda da tambayarta ya sukayi da fahreeyah a daren jiya itama,"ehh ranki yadade lokacin da nace mata ta jirani nakai sako ga jakadiya na dawo tacemin to,amma danaje na dawo saina ga babu almar ta a wajen,dana duba ban ganta ba sainayi tunanin ko ta koma dakinsune shiyasa kawai namanta da lamarinta nima".
Maganar da masoyin nameemah yayi ne yasa kowa maida hankalinsa Kansas,"amm nima lokacin da ta shigo dakin ina zaune kawai saina ga ta fara matsowa kusa dani tana lumshe idonta dana shaki kamshin dayake jikinta ne naji hankalina ya gushe shigowar gimbiya nameemah ne yasani dawowa hankalina"
"Kin ji ko AMMEEH? kinji abinda tayiwa masoyina koh?,yanzunnan a kira min manyan dogarai😠😡"
Kowa shiru yayi ana jiran aga mai zai faru,can bayan wasu yan lokutane shugaban dogarai ya iso tareda tawagarsa,saida ta kalli dogaran ta kalli fahreeyah dahar yanzu kanta kasa yake,"inaso ki amsa min na karshe shin kin aikata abinda ake zarginki da dashi ko a'a,dan yanzunnan zan yanke miki hukunci ba sai anjima ba".
"""Tabbas duk halin danake shiga a baya,tun daga tsangwamar da kawayena sukemin,da kangin bautar dana shiga harma da rashin mijina jigona,babu wanda na shika tsaka mai wuya acikinsa kaman wannan laifin da aka lakamin na kokarin yiwa masoyin gimbiya nameemah fyade!!!,yau naga ta kaina ni fahreeyahtul sharmeelah,wace irin duniya na tsinci kaina wannan wace irin rayuwa ce haka,yah allah kasan ina cikin WATA RAYUWA!!!! yah allah ka nuna min haske,sananna..........","kehh ba magana nake miki bane ko kin shirya karbar komai?"
"Kiyan kemin duk hukuncin dakika san yadace da laifina ya shugabata, a shirye nake da karbar sa hannu bibbiyu,tunda ya riga ya shigo cikin RAYUWATA"wannan shine iya abinda tace kafin nameemah ta bada umarnin hukuncinta.
"Ku kaita magarkamar bakaken bayi"
Hahhhhh kowa ya dauka a wajen saboda jin irin hukuncin da gimbiya nameemah ta yanke mata,wasu nacewa yadace da ita maganin masu halinta yayinda wasu ke cewa komai tayi laifinta bai kai a kaita wannan magarkamar ba,saboda ba kowa acikinta sai yan leken asirin da aka kama ko kuma wanda suka yi babban ha'inci acikin fada na ban mamaki,hakan ma ba kowace mace ake kaiwa wajen ba.
Su Kansu dogaran saida jikinsu yayi sanyi kafin suka dagata daga tsugunnen da take,wanda sai a sannan ne takalli dunbim mutanen dake wajen,idonta ne ya sauka akan kirisah,wanda tayi mata murmushi da alamun babu damar tayi bayan abinda ta aikata mata,idonta ne yasake sauka akan shugaban wato habeebin nameemah😊,ganin kallon da take masane yasashi juyawa yabar wajen shima ko a kwalar rigarsa tunda yafita kunya kuma masoyiyarsa bata zargeshiba shikenan.
Har sun juya sun fara tafiya taji kukan sareeenah wanda hakan yasata sake juyawa itama tana kallonta,wanda sai a sannan hawaye yazubo mata da ta tuna cewa bayan mahaifiyarta da mijinta akwai wata wacce take santa kuma zatayi kuka idan ta tafi,tausayin sareeenah ne yakamata data tuna yanda suka zauna duk da na yan kwanakine awajen amma hakan bai hana sun shaku da juna ba😢😢😢!!!.
Jan ta sukayi kaman kayan wanki suka bar wajan.saida sukayi tafiya mai tsayi kafin suka shiga wata kofa wadda zata kaika gidan yari na karkashin kasa ta wani bututu mai tsayi,tun suna tafiya fahreeyah na ganin hannunta har komai ya bacewa ganinta.
Tafiya sukeyi har suka shiga wani waje mai fili saidai yafi hanyar yalwar haske amma ba kaman haskaen sararin duniya ba,wucewa akayi da ita wani daki ita dai banda bin su babu wani aiki da takeyi,jefata sukayi a wajen batare da sunce komai ba suka juya suka a wajen.
Had suka tafi bata dago kantaba domin a tunaninta ba wani rai a cikin dakin,saida taji motsin mutanene ta dago kanta suka hada ido da wasu manyan mata masu bakar halitta,dayace acikinsu ta wullo mata wani kaya baki na saki tareda cewa,"maza ki cire wannan kayan jikinnnaki masu haske,domin mu bama ta'ammali da abu mai haske kuma kiyi shirin karbar sakamakon laifin dakika aikata, dan mu nan ba'a tambayar mai mutum ya aikata kawai idan an shigo dakai to babu alamar sassauci dazaka fuskanta daga garemu"
Kayan dake jikin fahreeyah tasa hannu ta ja,kaman masu jiran a janyesu suka yage daga jikinta,ganin kaman kiftawar bismillah tarasa suturar jikinta,yasa tafara kakkare fatar jikinta daga kallonsu,wata dariya suka sa dasuka ga abinda take saida suka gama dariyar kafin suka darara mata tsawa tareda sanar da ita cewar basason sanyar jiki a wajen.
Cikin hanzarin kuwa ta gama abinda suka umarceta,wata daga cikinsu ce ta finciketa tareda yin wata hanyar daban.
Saida sukayi wata yar tafiya mai nisa kafin suka iso wani daki mai kama da keji wanda aka yishi da bakin karfe,zefata tayi ciki ta fadi akasan wajen kafin ta juya ta tafi kaman batayi komai ba.
Bayan tafiyr matarne ta daga kanta suka hada ido da wasu mata guda biyu wanda tsabar ramar dake jikinsu kaman ba a taba halittar tsoka a cikin jikinsu ba,dayar cikin su ce tace mata"barka da zuwa cikin ukuba yar uwa muna miki jajen zuwa wannan wajen.............tofahhhhh🤫🤫🤫

SADY-SAKHNAceh

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now