Chp(34)haduwar masoya❤❤

60 10 10
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(34)
Saida suka dan zagaya tukun kafin yarima amam yace masa su tafi yakarbi maganin kawai yagaji da tafiyar.
A baking kofar shiga wajen suka samu inna kainana tana gyara wani magani,sallamarsu taji ta dago kanta tareda kallonsu tana Murmushin manya,
"Ahah yau hada mai gaba daya ne a sashennawa gashi kuma kunzo ina aiki amma bari na karisa daka shi tukun,dan so nake tafara shansa zuwa gobe"
Saheel ne yayi murmushi kafin yace,
"Na yarki ne kenan,dan naga kon bashi muhimmanci"
"Kwarai kuwa sonake tafara shansa da safe kafin taci wani abun,kasan idan haihuwa tazo sai a hankali,sai kuma naga ka dawo bayan kayi mana sallama kuma,koh wannan mai shunanniyar fuskarne yadawo dakai?"
"Haba inna harda ke a tsokanar tasa,bai da lafiya yazo a dubashine,saboda bayaso a sani shiyasa yaxo da kansa"
"Ayyah to kuzo mu shiga ciki mana,dama khairiyyah ta tafi bari naje na dagata daga zaunen da ta ke ,nasan yanzu ta gaji"
"Allah sarki har yanzu ana ta fama"
"AI ankusa ai saheel tunda takusa shiga wata na tara,saidai abinda nake jiye mata shine kar ya dora akan watan haihuwar kowa"
Da haka ta gama daka abin tayiwa su yarima amam iso ciki,wanda har ya gaji da tsayuwa.
Fahreeyah ceh ita kadai a dakin a zaune,tana kallon inna tashigo ta daga mata hannu tareda kobare baki irinna masu shagwabar nan,
"Innnaaa kings khaleesah koh,wai bazata dagani ba tunda kika sakata tayimin dambu,wai saina kara har a minti talatin,kuma...............maganar tace ta tsaya ganin wanda yabiyo bayan saheel din.
Shima a nasa bangaren ture saheel yayi dayake gabansa yatsaya kaman ya mutu a tsaye,mika hannunsa yayi dayake rawa ya fara nuna fahreeyah da take zaune ,itama kallonsa take tana zare ido kaman taga aljani,takawa yafarayi a hankali yana karisawa inda take har saida yah tsugunna akan gwiwoyinsa,hannunsa yasaka yadago fuskarta tareda rikewa acikin hannunsa,
"Itace itace,wallahi itace"
Saikuma ya fashe da kuka tareda rungumeta a jikinsa,itama a nata bangaren saida ta jishi a jikinta kafin ta kankameshi tana mai sakin wani irin kuka mai tsima zuciyar mai sauraro.
Kowa a dakin kallonsu yake da mamaki dan saida sukayi kusan minti talatin a hakba batareda sun bambare da juna ba.
Dagowa yayi yana kallonta itama shi take kallon tana zubar da hawaye,daga hannunsa yayi yana share hawayen dayake kan fuskar ta kafin yace,
"Yah isah haka kukan,kinsan zai taba zuciyata sosai"
"Yah saheel kayi hakuri bazan sake fitaba in baka nan,bazan sake barin gidaba zan zauna,dan allah karka sake bacemin,idan mafarkine karka bari na farka"
Kara rungume ta yayi yana shafa bayanta,
"Nima kiyafemin nakasa fita duniya neman ki faryahh,bankasance mai cika alkawarin ummah bah,dana barki tsawon wannan lokacin,hakika na azabtu da rashinki faryah,zuciyata bata gano tayi rashiba saida na bude ido narasaki a duniyata abubuwa sun faru nakasa jurewa faryah dan allah karki sake bacemin a karo na biyu na rokeki"
Sun dade suna magana da kuka,ganin hakan bazai kare bane yasa saheel yin gyaran murya,sai a sannan yarima amam yasaketa yana sake share hawayen dayake bin kumatunta,
"Wai mayake faruwane?kun sakamu  a duhu  yakamata kuyi mana bayanin mai yake faruwa"
Amam ne yazuyo yana kallon mutanen dakin harda khairiyyah wacce ta dawo daukar abinta ta manta,da ita aka more dramar data wanzu tsakanin yarima amam da fahreeyahn.
"Saheel itace Wacce nake baka labari,narasata shekara guda da suka wuce a ina kuka sameta?"
Duk maganar da sauri yakeyi kaman wani zai rigashi,khaleesah ceh tayi saurin cewa,
Koh kaine saheel din datake bada labarin mijinta?"
Daga kai kawai amam yayi,a tare suka amsa dacewa " toh taya haka ta faru? Juyawa sukayi a tare ganin numfashin fahreeyahn yana yin sama sama,duk matsawa sukayi kisa da ita domin ganin mai ya faru,inna ce ta dagota jikinta da niyyar daga ta,cikin sauri yarima amam yagata tareda tambayar inna ina zai kaita,
"Eh muje ka kaita daki idan ta ware numfashin zai daina,girman cikinne yafara fin karfinta ,sannan ta dade a zaune ga kuma kukan datayi"
Bayan ya kwantar ta da kyar inna tayi dashi ya fito dan gani yake kaman zata tafi ta barshi.
Dawowa yayi ya zauna yayi shiru kaman mai Tunani hankalinsa yana kan dakin da fahreeyahn take,
"Abokina yadai kayi shirune,baka tambayi mai yafaruba koba ka ganta da ciki bane?"
"Nagani saheel saidai nasan dole akwai abinda yafaru saboda na yarda da ita sosai"
"Hakane kam hakika taji dadi data samu wannan yardar daga wajenka"
Ananne aka bashi labarin halin data shiga tunda kan bautarta dazuwa Gidan kurkun kasa har da kwantar da cikin da akayi na tsawon shekara guda da kuma zamanta a wajen inna kainata da kuma watannin cikin dayake jikinta,kasa magana yayi sai kawai hawayen daya share dan yarasa ma mai zaice,tashi yayi kawai ya koma dakin da take kwancen.
A kwance yameta saidai yanzu numfashinta yayi dadai,tsira mata ido yayi duk ta sanja kama a idonsa ga kuma wahalar dayaji labarin ta shiga koshi bai isa ya jureba,amma hakan bai sa ta gaza da cikin dake jikinta ba,hannunsa yakai a hankali yana shafa cikin dayake jikinta,murmushi yayi dayaji yanda dan dake cikinta yana motsi,bai kula ba yatafi duniyar tunani sai ji yayi ta dora hannunta akan nasa,juyar da hannunsa yayi yarike nata acikin nasa yana kallon cikin idonta,
"Har yanzu banyarda cewa ba mafarki bane yah saheel,dama zan ganga da idona,tabbas ina cikin farinciki daya zama kaima kana gefen a halin yanzu"
"Kiyi hakuri da boyemiki wani abu danayi faryah,ba Sunana saheel ba ,nayi amfani da sunan abokinane yarima saheel saboda banason a game ni waye a wancan lokacin.
Ainihin Sunana shine Shamam huruddeen (yarima amam)"
"Hum kana nufin yariman masarautar nan kuma mijin gimbiya nasreemah,yah jikinka naji a labarin da aka bani wai baka da lafiya ka warkene?"
"Kibar wannan zancen yanzu,yakamata muyi shirin tafiya koh?"
"Ina zamuje?"
"Sashena mana kinsan bazan iya tafiya ba idan bakyanan koh?"
"Kayi hakuri yah saheel,au amam amma bazan iya binka wajen matarka ba ,kabarni a wajen inna zata kuladani"
"Bakyason zama Dani faryah?,matata batanan tatafi gidansu,inkuma saboda matsayina ne zan iya zama koma miye indai zayyi dadai da yanda kikeso,amma kiyi hakuri faryah bazan iya bari ki na tafiba,saidai nima nazauna a nan din"
Kallonsa take da mamakin abinda yace ,dan gani takeyi kaman sauya shi akayi bashi bane,inna ce takatsesu tareda cewa,
"Shikenan Zara bika kutafi saika je kashirya kafin na gyarata,amma fah zaka kulada ita sosai,sannan zaka boye matsayin ta acikin gidannan kar kowa yasani har zuwa wani lokaci,kuma zan dunga zuwa ina dubata koda bayan kwana biyune,kadunga zuwa kana karbar maganinta kuma,dan ba cikine kamar kowanne ba yana bukatar kulawa sosai,idan ba haka ba zaka iya rasata itada abinda yake cikinta".
Take ya amince da duk abinda innan tace masa,ya fita da sauri domin shiryawa kaman yanda tace.
Matsawa tayi ta zauna a wajen fahreeyah kafin tace,
"Naji duk abinda yace,yakamata ki bishi dan yana cikin tsaka mai wuya,zamanki kusa dashi zai bashi nutsuwa sosai,sannan inkika ce bazaki komaba toh kullum sai yazo wajennan kuma cikin sauki za'a gano mai yake faruwa wanda kema kinsan kuma sauran,karki damu zan dunga zuwa ina dubaki babu abinda zai faru kinji"
Gyada kai fahreeyahn tayi alamar ta amince,taimaka mata tayi ta tashi tareda sauya mata wata rigar sannan ta bata maganin ranar kafin yadawo.

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now