Chp(39)mu zuba mugani!!

61 7 0
                                    

The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(39)
Jijjiga kai kawai nameemah take idonta yana zubar da hawaye,batareda tace musu komai ba ta juya ta bar ma sashen gabaya.
Komawa wajen su nasreemah tayi saidai bata samesu a parlorn ba dan ba kowa a wajen,har zata fita saikuma ta jiyo kaman nishin mutum a dakin da fahreeyah take,karisawa tayi inda tayi arba da ita a tsakiyar gadon tana zuba uban nishi kaman ranta zai fita,ga kuma gumi da yake bin jikinta kaman an yi mata wanka da shi,karisawa tayi wajenta da sauri tana rike kafadarta hade da yimata sannu cikin kidimar ganin halin da take ciki,
"Sannu bari naje na kira inna kainata yanzu bazan dade ba"
Kwace hannun ta wanda fahreeyah ta rike tayi tareda fita daga dakin cikin sauri har tana hadawa da gudu.
Tun daga bakin kofar take kwalawa innan kira cikin daga murya,bayan tashiga cikin dakin saida ta tsaida numfashinta kafin tace,
"Inna fahreeyah tana ta nishi inaga haihuwa zatayi gashi........."
Basu Bari tagama fadar abinda yakawota ba suka nufi waje gabadayansu harda nasreemah wanda itama ta shigo wajen inna ana ta hirar labarin baya.
A yanda nameemah ta tafi ta barta haka suka sameta tana ta nishi har ta fita hayyacinta dan azaba,kokarin bata taimako suka farayi wata na shafa mata ruwan sanyi a goshinta wata kuma na kokarin bata maganin taimakawa wajen nakuda.
Tun sunayi ana ganin da alamar cigaba har dare yayi suna abu daya,haka kowa yayi tsaye da kaga fuskar su kasan suna cikin tashin hankali.
Da dare ma haka suka kwana babu wanda ya runtsa yanda suka ga dare haka suka ga rana.
***
Sarauniya safeenah ce a zaune tana saka wani abu kamar riga da zare,hankalinta daga gani ba akan sakar yakeba tanayine dan ta kawar da wani tunani a ranta,sameerah ta kallah wanda take gefenta tace,
Nikuwa kinga amam kuwa tsakanin jiya da yau,jiyama dana aika a kiraminshi ance yana zuwa amma kuma har yanzu shiru,?"
"Eh hakane ranki yadade,ni ina tunanin anya kuwa lafiya,dan daga shi har abokinsa saheel babu wanda nake gani acikin gidan kaman wanda suka bata,kuma yanayin shi yariman kaman wanda yake ramewa kullum"
"Hadamin fita yanzu zanje sashennnasa"
"Amma Ranki yadade da kanki zakije?"
"Eh yakamata naje dubashi,ko haramunne dannje sashensa?"
"Ahah yanzu kuwa za ayi yanda kikace"
Cikin kankanin lokaci sameerah ta gama hadawa Sarauniya safeenah fita zuwa sashen dannata wato Yarima amam.
Tun daga bakin kofar sashen nasa abun yabata mamaki ganin baby bawa ko hadimi ko d'aya daya gibta ta gabanta,a palorn ta samu saheel da khaleesah dakuma nameemah a zaune dukkansu sunyi tagumi babu abinda ke kwance a fuskar su sai tashin hankali da kuma rashin bacci.
"Menene yake faruwa a nan din haka?"
Dukkansu daga kai sukayi da Mamakin ganinta a lokacin,sai kuma kowa ya sunkiyar da kansa babu alamar zai bata amsar abinda tace,ihun nishin da taji ne yasa ta maida hankalinta ga inda amon muryar yake fitowa,hanyar wajen ta nufa tareda bude kofar,arba tayi da matar da take nishin a tsugunne a kasa gefenta na dama kuma amam ne yake rike da ita yana zubar da hawaye,yayinda ta daya barin kuma inna kainana take ta kokarin danna cikin kasa,Nasreemah kuma tana share gumin dayake fitowa a goshinta da wuyanta.
Mitstsika ido tayi tasake budewa koh mafarki take,amma abinda ta gani da farko shidinne dai yanzu ma a gabanta,karisawa tayi a hankali ta zauna cikin sanyin jiki,dan koba tasan dalilin faruwar abinba,amma idon ta sun gane mata wahalar da baiwar allahn take sha a halin yanzu.
Amam ne yakula da wanzuwar mahaifiyar tasa a wajen inda ya yi saurin kiran Sunanta cikin karayar zuciya Yana cewa,
"Ummmmah,kiga wahalar da take sha,ummah karta mutu,ta barni,ni basaita haihu ba amma karta tafi ta barni"
Inna ceh tajuya itama ga safeenah tareda cewa,
"Ranki yadade tunda kinzo inaga kiyi kokarin fitar dashi waje,ko ya daina wannan sambatun dan itama kanta mai ciwon karya mataa zuciya yake in tana ganin yana kuka"
"KO ma menene yafaru ni bansaniba amma ina ganin zaifi kyau ka basu waje,zamanka bazai kara komai ba"
"Amma ummah......."
"Kayi yanda nace karka kara laifinka akan wanda kayi"
Tashi yai cikin sanyin jiki da nufin bin bayan ummah wanda itama ta mike dansu su basu waje,hannunsa fahreeyah tayi saurin rikewa,kafin tace cikin muryar Wahala wanda bata fita sosai,
"Tafiya zakayi kabarni?kace bazaka barni ba,kaine kwarin gwiwa ta a wannan wahalar karkayi nesa dani a halin yanzu ina tsoro zuciya ta gaza cigaba da kokartawa akan wanda take,na rokeka karka tafi"
Shiru sukayi suna kallonta yayinda shikuma yayi saurin komawa jikinta yasake makalewa tareda damke hannun da ta rikeshi dashi,wani nishin ajiyar zuciya tayi kafin taciga da nishin da take.
Nasreemah ceh ta share hawayen fuskar ta tareda cewa,
"Ummah dan Allah kibarshi,ganinsa kusa da ita yana karamata kwarin gwiwa,shima hankalinsa bazai kwanta ba idan baya ganin halin da take ciki"
Safeenah bata ce komai ba said fita da tayi daga dakin tana share kwallar da ta fito mata ta Mamakin menene a tsakaninsu haka,abu daya tasani shine tana tausayinsu dukka,musamman halin data gansu a ciki shiya kara narkar da zuciyarta.
Zama tayi akan kujerar daya daga cikin palorn kafin ta tambayi saheel,
"Meyake faruwa anan wajen inaso kabani labarin duk abinda yake faruwa ban yadda kuma kamin karya ba"
Aikuwa kaman yanda tace cikin hanzari ya zayyane mata duk abinds yafaru,harda maganar dasu nasreemah suka jiyo su zulaikha suna yi,bai boye mata komai ba.
Jinjina abin tayi a ranta,can kuma sai tace,
"Hakika babu abinda yafi karfin Allah,tabbas duk da nasan abinda suke aiwatarwa ban raba yinkurin yin wani abu ba saboda na barmusu aniyarsu,amma yanzu dole a taka musu birki saboda suna kokarin cutar da ahalina ba iya nikadai cutar su ta tsayaba,dan haka zanyi komai dan kubutar da zuri'ata daga sharrinsu sunyi abinda banzan taba yafemusu ba ,domin sun riga sun kaini bango,za'ayi koni kosu a cikin masarautar sardaham muzuba mugani"
Idontane yayi ja fuskarta ta nuna alamar bacin rai,da alamun mikin dake cikin zuciyarta yadawo danye shakaf a lokacin....................hmmmmmm!!!

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now