Chapter(06)auren gimbiya safeenah

76 16 0
                                    

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

    written by sadi-sakhna

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

(06)

"Da farko banason kinuna kiyayyarki a fili a wannan auran,inaso ki nuna tamkar baki damu ba ,sai kowa yasake dake akan haka kafin zamu dana tarkonmu akansu wanda basu da ikon fita daga cikinsa"
"shikenan abba zanyi yanda kace ,amma nida burina shine a wargaza aurennan tun yanzu dan har yanzu zuciyata takasa aminta da zancen kishiya,hakan yana kona min rai sosai"
"wai ke bakya jin abinda mahaifinki yacene ?ki kwantar da hankalinki da sannu zamu cimma duk wani burinmu ba karbar ragamar masarautar saraham ,ko baki gani yanzuma cikine dake ? idan kika haifi namiji ai saidai ta biyo a baya kuma bazamu taba barta ma ta haihu a cikin gidanba "
  "shikenan mungama magana kitashi ki koma kar wani yazargi wani abu sannan ki tarbeta,cikin kwanciyar hankali ,,kuma ki kula da cikin dake   jinki domin a halin yanzu shikadaine damar mu ta gaba"
  shine abinda mahaifiyarta tagama fadamata bayan hudubar da waziri uwaisu yagama fada mata,tashi tayi ta fara shirin komawa gidannata tare da damarar aikata duk wani abu daya fito daga bakin iyayennata.
A bangaren amarya kuwa koda akasanar da ita daurin aurenta da sabon sarki huruddeen ,hakan bai wani dameta duk da batada masaniya akan shirin aurennata,saboda al'adar masarautar tasuce aurar da gimbiyo ga duk wanda yadace batare da zabinsu ba.
Zaune take akan dardumar dake dakinta bayinta na zaune a gefenta sai ga kira daga turakar mahaifinta akan yana nemanta,tashi tayi batare da tace wani abu ba tabi bayan jakadan cikin sanyin jiki wanda yakasance tamkar halinta.
Koda ta isa turakar iyayenta ,shiru tayi kaman lbrin daya ke zagayawa a cikin fadar bai iso gareta ba ,hakan yasa sarki uwartu fara magana.
"safeenah nasan bazakice komai ba ,kaman sauran yan uwanki akan abinda yake faruwa wanda nasan cewar labarin ya isa kunnenki ,to ki dauka cewar haka abin yake ,sarki shamam dakansa ya zo izuwa gareni neman iri,saboda kyawawan halaaye irinnaki yasa ni amincewa da zaboki acikin yan uwanki ,duba da dattako dakuma halin kawarai na masarautar saraham ,dan haka in fatan zakiyi biyayya akan hakan"
"inshaallah zan kasance mai yin biyayya akan hakan duk wani zabi daya kasance ya fito daga gareku matukar bai kasance sabon allah bane"
"nagodee da wannan magana taki ,da yardar rayuwarki zatayi albarka saboda wannan biyayya taki ,shikenan ki tashi ki tafi zaku fara bukukuwa na al'ada a sashen mahaifiyarku kafin suzo tafiya dake ,allah ya miki albarka tareda zuri'arki gabaki daya "
Tashi tayi wanda tana fita wani kiran yazo daga sashen mahaifiyarta ,wucewa tayi zuwa ga kiran mahaifiyar tata,tana shiga idan ta ya sauka kan manyan matan da suke zaune akan kujerun turakar mamar tata ,karisawa tayi ta gaishesu da daddaya kafin ta zauna a wajen mahaifiyar tata ,kallon gimbiya safeenah tayi kafin tace.
"nasan mai martaba yamiki bayanin komai akan abinda yake faruwa dan haka inso kidora akan yanda nasanki na halayenki ,duk da bikin yazomana a lokaci kadan saida munne mi alfarmar zuwa daukar amarya nan da kwana uku ,dan haka,akwai wanda aka dauka masu gyara dakuma kwalliya wanda zasu fara yimiki daga yau har zuwa nan da ranar daukar amarya,tashi muje dakin dazaki fara zama domin yin gyaran ko ?"
Tana gama bayanin ta mike suka fara tafiya zuwa wani sashe daban inda za'a fara gyaran jikin gimbiya safeenah ,wanda har suka isa tana yimata karin haske akan sha'anin auren daya hau kanta.

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now