Chp(42)Nagode maka

61 11 0
                                    

The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(42)
Hakan bazai taba yiwuwa ba,dariya tafarayi tana cewa,
"Dama yace in aka gano ni na aikata toh zan haukace gashi kuwa na haukace,shikenan abu yayi dadai,koh neelah,na fadamiki ki kawomin manneer wajena dolene shi zayyi sarautar kasarnan,gashi kuwa ina ya hau koh?,heeeeeehuuuu haka ne kam"
Ganin abun bazai karebane yasa alkalin wajen cewar,
"Bisa hukunci wanda masu laifi suka amsa laifinsu,shi waziri saboda shine yakullah komai,zai sauka akan mukaminsa sannan an yanke masa hukuncin zama gidan yari har karshen rayiwarsa ,ita kuma zulaikha za'a kaita gidan mahaukata in ta dawo hankalinta za'a yanke mata hukunci in kuma bata dawo hankalinta ba,toh zata kare rayuwsrta a can,sai neelah ita kuma zatayi shekara biyar a gidan yari,kasancewar babu wani aiki da itah ta aikata saidai tayawa da take ko kuma ta rufe"
Fadarce ta dau hayaniya kowa na fadan albarkacin bakinsa,ganin hakanne yasa yarima amam yadauki fahreeyah suka nufi sashen safeenah inda dama tace akaita,hardasu nasreemah wanda suke rike da yaran.
Kafin wani lokaci har masarautar sardaham ta dauka da cewar matar yarima amam wanda ya aureta lokacin da ya bar masarautar ta haihu har y'ay'a guda uku.
Bikin shirye shirye aka farayi tun kafin bakwai din sunan yaran,kaida ganin dumbim shirin da akeyi kasan yara sun amsa sunansu na jinin sarauta.
Ba abinda fahreeyah takeyi sai Godiya ga Allah bisa rayiwar daya sanja mata batareda ta yi tunanin hakan ba,a wajen yarima amam ma kuwa ganin abin yake kaman mafarki,wai yau shine da y'ay'a uku kuma wai duk nasane,bayan ya cire tsammanin samunsu a rayuwarsa.
Ran suna kuwa makil masarautar ta cika da mutane,wanda kowa yazo domin murnar taya sarki huruddeen samun jikoki dayayi.A bangaren fahreeyah ma kuwa ba karamin kyaututtuka ta samu ba,tun daga kan,mahaifin mijinta dakuma uwar mijinnata wacce da dauki a fahreeyahn tammakar y'ar da ta haifa,nasreemah ma da nameemah ba karamin bajinta suka nunawa y'ay'an ba barekuma uban gayyar wato uban yaran,shima yarima saheel tare yabayar da tasa shida khaleesah,wanda suke shirin zama ango da amarya bayan amincewar mahaifin nasa,sanda yazo bada hakuri na abinda yafaru tsakanin su nasreemah da yarima amam din.
Dan tsabar kaya dakuma kyaututtuka da aka tarawa fahreeyah itada y'ay'anta batasan lokacin da ta fashe da kuka ba,dan ganin abin take kaman yayi yawa,ina zata kai wannan kaya haka harda su zinare da kayan ado ,wanda bata taba ganinsu ba bare kuma jin sunan su ba.
Da haka taro ya kare inda yara suka ci suna kamar haka,
Namijin aka saka masa sunan baban fahreeyah wato shuraim(Abeeh),matan kuma sukaci suna ,HUDA(Hudiya) da SAFEENAH,wanda ake musu lakabi da (Feenah,da hudeeyyah).
Duk wani abu da fahreeyah ta nema babu abinda ta rasa wajen safeenah saboda kulawa ta musamman take basu itada jikokinta wanda take jinsu har a kashin ranta.
Bayan wata biyu da haihuwar fahreeyah har ta koma sashenta wanda bashida maraba dana nasreemah wanda ta Zauna a ciki,shirye shirye ake tayi na auran saheel da kuma khaleesah,su fahreeyah babu zama itada su nasreemah,koyaushe suna kofar nasreemah ana tsara yanda abu zai kasance.
Saboda nameemah ta koma dakinta bayan artabun da aka sha da ita,na laifin da mijinnata ya aikata mata,saida ta tabbatar ya sanja daga halayyarsa kafin ta yarda ta koma,shima da sharadin kar ta sake kamashi da wata nan gaba,indai ba aure zai karaba.
Y'ay'an fahreeyah sunyi bulbul dasu kaman wanda sukayi wata biyar abinka da gidan hutu da jin dadin,kowa sha'awar daukarsu yake,musamman ma nasreemah wanda koyaushe suna sashenta sai cin abincinsune yake mayar dasu wajen mamartasu.
Darene yafara shiga,fahreeyah suna kwance itada amam,wanda ta karbi kwananta ba da dadewa ba,juyowa tayi ta kalli amma kafin tace,
"Zaujeee,karima bakayi bacciba?"
"Eh taya zanyi bacci ina tunannin yanda zanyi missing din ku kedah su ummeenah,"
"Missing dinmu kuma wani abune yafaru,Koyaushe ai muna tareda kai wani waje zaka tafi?"
"Ahah baby inda zanje kunedai zaku tafi,saidai yanzu nasanja shawara tare zamu tafi dukkanmu,zan kaiki garin bardugu wajen mahaifiyar ki,amma yanzu tare zamu tafi,saboda inaso naje har gidan su ummah wajen kakanninki saboda lokaci yayi daya kamata wannan gabar ta gushe tunda har anyi y'ay'a da jikoki"
Wani tsalle fahreeyahn tayi ta rungume amam din tana zuba masa gidiya da duk abinda yazo bakinta,
"Kiyi a hankali faryah,dan har yanzu baki gama warwarewa ba karkiyimin asarar lafiyarki,dan banason abinda zai taba ahalina"
Dahaka gari yah waye fahreeyah tana ta dokin zuwa garinnasu wanda rabonta da shi tafi shekara biyu,lokacin da ta fito tayi Mamaki da taga anshirya komai na tafiyar wanda bata ma san sanda hakan ta faru ba,lallai amam dinta yacika miji na kere sa'a,tafada aranta tare da yi masa addu'a allah ya barsu tare.
Saida fahreeyah taje wajen sarauniya safeenah sukayi sallama kafin taje wajen nasreemah ma,dukkansu tsaraba mai yawa suka mata,nasreemah kam kaman tabisu taji saboda rashin su hudeeyyah da zatayi.
Tafiyace mai nisa suka dauketa ,ita da mijinta da kuma y'ay'an ta,lokacin da tazo kasar ta tuna sanda ta shigo a matsayin baiwa sai gashi yaukuma zata fita cikin karamci,lallai ba abinda yafi karfin allah (allah yayi mana mai kyau)
Kwanci tashi ba wasa harsu fahreeyah suka iso garin bardugu kuma anguwar tsarauni,gaban tane yafara bugawa da tsammanin mai zataje ta tarar acikin gidan,jin and dafa kafadarta ne yasata juyawa ta kalli amam din,
"Ni tsoro nakeyi zaujee"
"Karkiji tsoron komai ina tare dake"
Daga kanta tayi alamar taji mai yace,kafin tasa kafarta acikin gidan shima amam yana biye da ita,sai kuma bayin da suke dauke da su Abeeh a hannunsu su uku.
Sallama tayi a hankali kaman mai tsoron magana,saida aka dade kafin aryana ta amsa cikin masifa.
Tana nan bata sanjaba,fahreeyah tafada aranta,
"Lahhh baki mukayi daga masarauta ?ku shigo amma inaga gidan sarki kuke nufi mai yakawoku wannan anguwar kuma........"
"Baaba aryanah"
Turuss tayi wanda sai yanzu ta gane wacece a gabanta,
"Ffff.....ahreeeyah........kece"
Tafada tana nunata da yatsa,daga mata kai fahreeyahn tayi tareda tambayar ta ,
"Nice ina ummah nah?"
Kwalawa huda kira tayi wanda take daki,da sauri kuwa ta fito jikinta har rawa yake saboda jin kiran aryanan.
Tsayawa tayi daga inda take tana kare fahreeyah da kallo,itama fahreeyah kallonta take,ganin yanda ta rame kaman an lullubawa kashi fata,kuka ta fashe dashi tareda nufar mahaifiyar tata da gudu tana rungumeta kamar wani zai kwace mata ita.
Susar kai aryana tafara kaman mai shirin fara sabuwar hauka,wani kallo dakarun wajen sukayi mata,cikin sauri ta hadiye wani yawu ,mukuttt!!😂,
"Hattara gareki hakika kin b'ata ran gimbiya fahreeyah,uwargida a wajen yarima amam na masarautar sardaham sannan kuma uwar y'ay'a uku,hoood'an ,diyar albarka kenan,lallai saikin fuskanci hukunci"
Ba iyah aryana ba,har huda ma saida ta dago jin abinda dogaran sukace kafin tasake kallon fahreeyahn ,sannan ta sauke idonta akan yaran da suke hannun matan wanda suma sun sha ado barekuma uwar gayyar.
Tofahhh Baaba aryana mugunta takare😂😂😂..,.........

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now