Chapter (14)Me yake shirin yimin ?

70 10 6
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(14)

Wuceta yayi ya bud'e dakin ya shiga ,ganin bai mata maganaba itama ta bishi cikin gidan .
bata sameshi a cikin falonba ,sai tasamu waje ta zauna akan kujera kalle kallen cikin gidan ,sai yanzune take karewa cikin gidan kallo, ba  kaman zuwanta na farko ba ,
""a zagaye dakin yake ,anyi masa shafe da farar kala ,ga kuma kujeru guda uku a cikin dakin ,sai wata hanya dazata kai mutum wani dan karamin d'aki inda ake girki ,dakin da saheel ya shiga kuma shine wajen kwanansu wanda yake dauke da gado dakuma dan karamin shimfid'a a gefe ta  fonee , a bangaren hagun kuma a akwai kofa dazata fitar da kai inda bandaki yake .
Gidane dan karami amma mai kyau da ban sha'awa ""
tana cikin nazarinne taga saheel ya fito daga dakin daya shiga lokacin da ya dasuka shigo cikin gidan ,yanzunma bai mata maganaba kawai ya wuce inda yake dafa abinci ,ta dan dade a zaune yasake fitowa hannunsa dauke da kwanon abinci ,a jiyewa yayi a gabanta kafin yayi hanyar fita ,binsa tayi da kallo har ya bacewa ganinta ,ajiyar zuciya tasake kafin tadawo da hankalinta kan abincin daya ajiye mata.
Bayan tagama ci ne ta kwantar da kanta akan kujerar da take zaune.
Jitayi kaman ana shinshina ta ,tana bude ido taga fonee akanta yana jujjuyawa ,kallon lokaci tayi ,sai sannan takula da rana ta kusa faduwa ,mamaki abin yabata ganin irin baccin datayi daga kwanciya ,wanda hakan yanada nasaba da tashin hankalin dasuka shiga itada ummahn ta a baya ,saheel ne ya shigo shima gidan wanda dawowarsa keanan gidan tun sanda yafita ,kallonsa tayi kanta a kasa ,domin tun sanda aka hada rayuwarsu waje guda take shakkarsa ,
"uhmm ya saheel zanje bandaki "
"uhm "
shine kawai abinda yace kafin ya tashi yayi hanyar dakinsu ,binsa tayi itama a baya ,inda yanuna mata bandakin shikuma yafito dakin yazauna.
Fitowa tayi daga bandakin kanta a sunkuye ganinsa acikin dakin ,kayan dayake hannunsa ya mika mata batareda yace komai ba, karba tayi tana dubwa .
kayan matane masu dadai kudi wanda take tunanin watakila sanda ta kwantane yazo dasu ,
"nagodee allah yasaka da alkhairi "
bai amsa mata godiyar da take masa ba ,yatshi yabar dakin domin bata damar shiryawa a dakin .
  Haka rayuwar fahreeyah ta cigaba da garawa a cikin gidan saheel cikin kadaici ,babu abinda yarageta dashi ta bangaren ciyarwa da kuma bukatunta ,saidai magana bata hadasu tsakaninta dashi saidai idan ta tambayeshi ya bata amsa a aikace ,tun abin bai damunta sosai har yazam cewar a yanzu tana ganin cewa ta takurawa rayuwarsa saboda zaman ta a cikin rayuwarsa .
Yauma hakan ce takasance ,bayan ta tashi da safe taga ita kadaice kawai acikin dakin ,akan katifarta daya kawomata lokacin da tazo gidan ,yunkurawa tayi zata tashi aikuwa marar ta tayi wani irin amsawa ,gabantane yafadi dajin abinda yake shirin tunkarota ,gashi babu ummanta a kusa bare ta taimaka mata,domin duk sanda tafara al'ada mahaifiyar tqce take taimaka mata da su ,maganin juko ,dumdumen ruwan zafi da sauransu.
har ta koma  zata zauna sai kuma tamike da shiga cikin bandaki domin ta gyara jikinta ,duk da tasan ba lallai bane yazo mata a sannan ba ,dan saitayi ta ciwon ciki tsawon kusan kwana uku ko biyu kafin yake zuwa ,dan tana tuna lokacin da ummahn ta ke nema mata magani akan hakan ,saidai rashin gata dasuke ciki badama suyi wani neman magani mai zurfi ,hawayene ya ziraro daga idonta data tuna zamansu itada ummah nata ,wata biyu da suka wuce ,
"wayyo ummah kinga yauma ciwonnan yadawo mun ,umma yazanyi ina kike ummah "
ganin kiran umman bazai mata ba gakuma ciwon yana cinta sai ta tashi tashiga kitchen dinsu ta tafasa ruwan zafi ta sha ,sannan ta dan tsakuri abincin da taga saheel yabari ta ci ,komawa tayi tasake kwanciya akan katifar tata  tareda tausayin irin rayuwar data tsinci kanta a ciki .
Sai can wajen yamma taji shigowar saheel cikin gidan ,ta kwance tayi shiru kaman mai bacci ,ita dai tana mamakin wannan rayuwar dasukeyi ita dashi ,domin kwata kwata yakoma kaman ba saheel din data sani a baya da.
saida yagama abinda yake yi,yazo ya wuceta ya shiga bandaki ,tana kallonsa har ya shirya cikin wasu kaya farare masu matukar kyau ,karemasa kallo tayi tana ayyana irin kyau na hallitar sa mai dau kar hankalin mai kallonsa ,musamman ma mace ,
"kinci abinci ?"
mamaki maganarsa tabata tareda kuma kunya data kamata ganin yana sane da kallon da take yi masa tun da farko ,saida ta danyi jimmm kafin tace ,
"ahah "
"meyasa to ? baki gani bane ?"
"nagani "
"tohh tashi kije kici "
shiru tayi kaman mai nazari kafin ta kokarta ta  tashi daga kwancen da take ,tashi tayi tamike tana cije fatar bakinta ,cikin azabar ciwon dataji ya ratsata ,duk abinda take bai kula da ita ba yajuya yabayansa ,jin yar karar data sakine yasa shi dagowa ya kalleta tareda cewa ,
"meyake damunki ?"
"babu komai "
daga haka bai sake magana ba ,yazo zai wuce ta gefen ta ,wani irin jirine ya d'ebeta tayi baya zata fadi ,kafin takai kasi taji yariketa fuskarsu tana kallon juna ,hawayene ya cika fuskarta ,kafin ta sakemasa kuka.
dagota yayi ya rungumeta a kirjinsa tareda da tallafo kanta ,numfashinta yaji yafara sama sama ,hakan yasashi kwantar ta akan gadon tana kallon sama kafin yafita daga dakin ,bai dade da fitaba yadawo da kofi a hannunsa ,zama yayi a gefenta tareda tallafota a jikinsa yana kallonta ,rufe idonta tayi tareda yin luf a jikinsa, saboda haji jiyar datake ji,dauko kafin yayi tareda cemata ,
"tashi saka wani abu a cikinki kafin nasan halin dakike ciki "
karba tayi tarada kafa kanta tafara sha ,saida tasha kusan rabi kafin ta mika masa kofin ,karba yayi ya ajiye a gefe kafin yajuyo da kansa gareta rabata yayi da jikinsa kadan yana kallon ta ,rigarta yafara d'agawa sama da nufin cireta ,inada tafara ayyanawa aranta cewar
"mai yake shirin yimin ?"
tohhh waya sani sai fah kun biyoni tukunna saimu sani abokai 😊😊😊,

#comment
#vote

SADI-SAKHNA ce

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now