Chp(32)ahhhhhj......!!!

49 10 1
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(32)

Shiru su fahreeyah sukayi kowa da abinda yake tunani aransa itada khairiyyah,a bangaren fahreeyah kuwa tunda taji labarin yarima amam wani nauyi ya dauru akan kirjinta kaman guduma,ga kuma wani tausayinsa daya darsu acikin ranta kaman ita akayiwa abinda yafaru dashi.
Khairiyyah ceh ta jijjiga fahreeyah da ta tafi wani dogon tunani wanda ita kanta batasan dalilinsa ba,
"Fahreeyah mai yasameki kike hawaye daga jin labarin wani?"
"Ahah na komai khairiyyah kawai.............ahhhhhhh..........ahhhhhhhh"
Khairiyyah ceh tayi saurin riketa ganin yanda take rike ciki tana kara ga kuma numfashinta yana hawa sama sama,
"Wayyo fahreeyah mai yasameki ki kokarta bari muje nakaiki wajen inna watakila ta gane abinda yake damunki".
Riketa tayi dakyar sukayi wata hanyar daban zuwa wajen mai maganin cikin gidan sarautar.
Bayan sun shiga sashen innan ne khairiyyah ta shiga da ita ta kofar baya inda ba kowane zai kula da suba,wani daki ta shiga wanda bakowane yasan yana sashen ba,haduwa sukayi da wata budurwa mai kyau amma batayi kama da bayi ba wanda suke masarautar,khairiyyah ceh ta gaisheta kafin ta tambayeta inda inna take,
"Khairiyyah wannan kuma fah?,ahah inna bata nan,saidai tunda naganki ta wannan kofar da alama bakyasan asan da ciwonne,amma kwantarta akan gadon bari na duba nagani",
"Toh tana jin jiki sosai,amma kuma ciwon nata ne ni bantaba ganin irinsa ba"
Duk abinda sike fahreeyah batasan anayi ba banda jijjiga kai da cize lebe ba abinda takeyi saboda azabar da itakadai tasan ya take.
Budurwar ta dade tana duba ta amma ba abinda ta gane,saidai maganin rage radadi data bata wanda ya taimaka mata tasamu tayi bacci.
Sai san wajen yamma innan ta dawo daga wajen hada maganin dasuke na matsalar yarima amam wanda ita kanta tasan kawai bata lokaci ake dan aikin gama yariga yagama,a zaune ta samu su khairiyyah da kuma matar da take kwance a akan gadon tana bacci.
Dagowa sukayi tareda yimata sannu da dawowa sai kuma bayani dasuka fara mata na ciwon fahreeyahn,
"Wannan it ace wada Kik ace Bata da lafiya kwanaki ina koh khairiyyah?"
"Ehh it ace yanzuma muna zaune kawai tarike ciki tana kara"
Karisawa wajen innan tayi tareda karemata kallo can kuma saitacewa ta gefenta,
"Keh khaleesah daukomin wannan kwaryar ta maganinnan sannan ki tahomin da ruwan dumi a cikinta"
"Toh inna"
Bude cikin fahreeyahn tayi tareda matsawa kadan ,wata kara fahreeyahn tayi tareda bude ido tana kallon wacce take kanta,
"Inna mafarki nakeyi ko kece dagaske agabana?"
Shiru sukayi kowa yana kallonta da Mamakin a ina tasan innan,
"Inna kainana dagaske ina kece koh?"
Tafada tana narai narai da ido,itama innan kallonta tayi kafin tace ,
"Keceh fahreeyah"
"Ehh"
"Ina Wasikar da innan naki tabaki toh"sauri fahreeyah tayi tana kwance gefen zaninta,can ta fito da wasikar wanda dama kullum tana jikinta dan batada inda zata saka ta,karba innan tayi tareda warwarewa.
Bayan tagama karantawane ta dago ta kalli fahreeyah tareda rungumeta tana dafa bayan ta,
"Sannu yarinya hakika kin shiga cikin tsaka mai wuya ko kuma nace kina ciki dan wuyar bata kare ba,wata wuyar ma yanzu zaki fara shiga,saidai yanzu kwanta na duba tukun kafin na  sanar dake .
Komawa tayi ta kwanta kaman yanda innan tace mata.
Wani ruwa ta shafa mata akan cikin sannan tafara dora hannunta tana juya wa can kuma saitayi shiru kaman mai jin wani abu,ta dade tanayin hakan kafin ta dauke hannun ta sannan ta mayar rigar fahreeyahn ta rufe mata cikin,tambayar ta farayi,
"Sannu kina jin yunwane yanzun ?"
"Ahah na sosai ba"
"Khaleesah debo mata abinci amma mai kara lafiyar jiki wanda na taho dashi dazu daga wajen sarauniya"
Saida taci abincin da dan yawa tasha ruwa kafin inna takira sunanta cikin magana mai muhimmanci,
"Inaso ki bani hankalinki dan kiji mai zance yanzu"
Tashi su khairiyyah da khaleesah sukayi zasu fice inna ta dakatar dasu kafin tace.
"Ku Zauna domin kuma kuji mai yake damunta ko zaku tayani kulada lafiyarta kodan tausayin halin da take ciki"
Samun waje sukayi suka zauna kowa na tinanin toh me inna zatace,
"Fahreeyah da farko inason gabatar miki da kaina duk da nasan yar uwata tafadamiki Sunana KAINATA wannan kuma itace Y'a ta khaleesah,sannan kafin nafada miki abinda yake faruwa inna Kainana tace na rokeki ki yafemata bisa zartar da abinda tayi a rayuwarki batareda amincewarki ba ko saninki....
Zazzabin da kikeyi tun farko cikine dake karami,wanda lokacin da aka kaiki magani wajen ta saita kula da abinda yake cikinki yagalabaita sannan kema kuma kina halin rashi ishashshiyar lafiya,sannan kuma idan aka gano cewar kina dauke da ciki toh komai zai iya faruwa,saboda ta kare lafiyar ki sai ta kwantar da cikin jikinki da nufin idan ta tashi barin masarautar saita fita tareda ke ta kuladake har ki haihu a inda zata zauna,amma lokacin da ta ga cewar zaki taho nan amatsayin baiwa shiyasa ta baki maganin da zai tayar da cikin dake jikinki sannan kuma tace ki nemeni kafin abin yafi karfinki wato idan kika fara jin ciwo kaman yanzu.
A halin yanzu cikin jikinki ya shekara guda kenan amma kuma yana a matsayin cikin wata uku kafin a kwantar shi,saidai wahalarsa da kuma watannin haihuwarsa zasu fi na kowane irin ciki saboda yanayin wahalar dakika shiga da kuma tsawon lokacin da ya dauka a kwance"
Kowa acikinsu zaro ido yayi in kadauke inna wanda ita take labarin,uwar gayyar kam batasan sanda ta tashi tsayeba a kan gadon duk da zafin ciwo da takeji.
"Karki damu yarinya ki kawantar da hankalinki ba abinda zaifi karfin Allah sannan kuma inkika daure wata rana sai labari,nasan saboda karki rasa dankine yasa ta kwantar da cikin ganin yanda tace bakya tareda mijiki,nasan ko bakiga wani naki ba in kina tareda danki hakan zai rage miki wani abun,sannan kuma gasu khairiyyah nasan zasu tayani kulada ke,dan hala ki kwantar da hankalinki in ma bananan kikaji wata alamar ciwo to kisanar da khaleesah kinji,zamu kulada ke sosai"
Kukan da fahreeyah takeyine tafara ragewa jin abinda innan tace,komawa tayi ta zauna kafin kuma tafara magana cikin kuka,
"Allah sarki inna nasan dan kinasona kika min haka,bazan taba mantawa dakeba allah yasaka miki alkhairi innata"
Tana gama suruntun dasake rushewa da kuka,wannan karon suma su khairiyyah kukan suka sa suna tayata,saida inna tabasu baki kafin sukayi shiru kowa na maimaita al'amarin a ransa cike da mamaki.
Haka fahreeyah ta zauna a wajen inna kainata tafara kula da ita batareda kowa ya sani ba inka dauke khairiyyah da kuma khaleesah,balaifi khairiyyah tana zuwa dubata wani lokacinma suyi ta hira ana dariya,inda ita kuma khaleesah take taimaka mata da abinci mai ware jiki dakuma wasu maganunnuwa na masu ciki.
Kular da fahreeyah take samu a wajen mutane ukun koh koh wata mai gatan bata samun haka,wanda hakan yasa har jikinta yafara sauyawa gakuma cin abinci davtake saidai zazzabin dare wanda shima daga yafara khaleesah take bata magani saboda tare suke kwana,komai tare suke har tayin kananan aiki wanda jikinta zai dunga warewa in tanayi.
A bangaren su yarima amam kuwa yarasa ta inda zaiji dadi saboda yanda matarsa take masa abin yayi yawa
koshi yake bawa kansa haihuwa iya kaci gakuma surutun gidan sarauta wanda shima yafara yawa da kadan kadan.
Yanzuma zaune yake yasaka Kansa a cinyar mahaifiyar sa yayi shiru saboda abubuwan dasuke faruwa dashi dayawa,cikin kuka yake yiwa safeenah magana wani ma baisan yana fada ba,
"Ummah yazanyi,mai yasa saini?,da wanne zanji da batan matata zanji koh kuma da auren dolen da akayimin ko kuma da rashin haihuwar da banida iko akai?”
"Mai kake fada haka lafiyarka Kalau kuwa,wace matarce ta bata kuma?"
Shiru yayi sai a sannan yatuna subutar bakin da yayi wanda ba damar komawa baya bare ya goge abinda yace.

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now