Chapter (22)an turoni ne aiki

57 7 1
                                    

The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

Chp(22)
Shi run da taji a dakin alamun bakowa,yabata damar tsayawa tana karewa dakin kallon,"""waiii irin wannan daki haka,saikace ba'a zama acikinsa dan kyau ,gaskiya wajennan yayi kyau sosai,""",
Saboda nisa data yi cikin yaba dakin,ta sau baki tana zuba murmushi har bata kula da mitumin daya ke bayanta ba,gyaran muryar da taji ne yasa ta juyawa da sauri tana zare ido,
"Wacece ke?,ko bakyajin magana ne inata gyaran murya amma hankalinki yana can wani waje,ko abinda ya kawoki kenan,uhm?"
Dago fuskarta tayi jikinta har rawa yake tana kallon mutumin dayake gabanta ,ganin daga shi sai farin kyalle a kigunsa ga kuma ruwa na bin farar fatar jikinsa ne yasata kara tsorata da lamarin tsayawa a kusa dashi.
Saida ta bata jinkirin lokaci na wasu mintuna kafin ta fara magana cikin in-ina,
"U hmm ...dama anturoni nan ne aiki"
Saida yayi jimm da bayanin ta kafin ya sauke ajiyar numfashi tareda wani murmushin gefen baki yana karewa dukkan ilahirin surar jikinta kallo saboda yanayin yanda kayan da'aka yi mata kwalliya dashi suka dauki surar jikinta.
Karar kofar daya jine yasa shi tsayawa da abinda yace kafin yanufi kofar dan ganin waye ,wasu bayine yagani ajere kowa da kayan abinci a hannun ta,basu hanya yayi suka wauce cikin dakin tareda jerawa akan daddumar cin abinci.
Bayan sun juya sun fitane shima ya nufi wani waje a dakin domin saka kaya.Duk abinda yake fahreeyah natsaye a wajen da yasameta bayan fitowsrsa daga bandaki,ko motsawa batayiba kaman wanda akace za'a yankata.
Bayan yagama abinda zaiyine yazo ya zauna agaban kayan abincin,har sannan idanunsa na kanta,magana tafara mata cikin sanyin murya,
"Meyasa kike tsaye a wajen?zonan!!!"
Takawa tafara yi a hankali kaman mai tsoron tafiya har ta isa ga inda yanuna mata,duk da dauriya take na ganin ta boye bayyanar bugawsr zuciyarta ,amma duk wanda ya kalleta yasan tana cikin tsoro da fargaba,sunkuyar da kanta tayi tana jiran taji mai zai faru kuma.
Jikin ta ne yafara rawa sakamakon jin hannun sa akan nata hannun, dagowa tayi da fuskarta izuwa kan tasa fuskar, aikuwa idonta ne yayi arba da mayun idanuwansa wanda yazuba mata su ko kiftawa bayayi,wani murmushi gefen baki yayi mata kafin yace cikin wata sansanyar murya,
"Meyasa jikinki yake rawa ko ba abinda kikazoyi kenan ba?"
Koda maganar ta doki dodon kunnenta sai ya kasance maimak on jikinta yadaina rawa saima kara mazari daya sake yi, ganin hakanne yasashi sakin hannun ta tareda sake matsowa inda take,
"Saka hannun ki muci abinci"
"Ahh.....yallabai..na..koshi,naci kafin na zo"
"Baambayarki nayi ba umarnine na baki"
Hannun ta saka acikin abincin cikin sanyin jiki kafin ta kai ga bakinta.
Haka cin abincin yakasance,yazamana cewa idonsa yana kanta yayin da itakuma takasance a takure,bayan sun gama cin abincin ne fahreeyah ta dauki kayan abincin da nayyar fitar da su daga dakin, saidai kafin da tashi yayi saurin dakatar da ita,
"Kibarsu basai kin fitar da suba,in kika ajiye su gefe ma yayi"
Ajiyewar tayi kaman yanda ya umarce ta,tana juyowa kuwa tasake hada ido dashi akaro na biyu yana karemata kallo,
"Ke kyakykyawace sosai, menene sunanki?"
Cikin muryar sa da ta kashe mata jiki dazu yasake tambayar ta,
"Fahreeyah"
"Wow suna mai dadi,zo kiji wani abu"
Yafada yana mika mata hannu alamar ta zo,kwalkwalwar ta ce tatafi wani tunani na wucin gadi,game da sakamakon abinda zai faru idan ta amsa kiran dayake yimata, sannan rashin takawar ta izuwa gareshi dadai yake da fuskatantar hukunci daga wajen horo.
Share duk tantama da kuma wani fargaba dake jikinta tayi,tareda mikawa mai duka dukkan lamarinta ta hanyar jan jikinta har izuwa gaban sa,yazamana cewa cinyoyinsu na gogar na kowa saboda tsananin kusantar su da juna,hannunsa yasaka yana shafar gefen fuskar ta yayinda idanunsa suka sauka a kowane sako na jikinta,magana yafara mata cikin wani irin murya wanda ta sanya cikin wani irin yanayi.
"U hmm fuskarki akwai laushi sosai dafatan dai nine wanda yafara taba wannan lallausar fatar kohh"
Yafada yana dago da fuskarta izuwa ga tasa fuskar.Idonta ta bude wanda su ke rufe tun lokacin da ta matso kusa dashi wanda suka cika da hawaye masu dauke da ma'anoni da yawa,
"Lah Lah Lah,karki bata wannan fuskar mai kyau mana,"
Cikin maganar maza masu shakiyanci yake magana ,yayinda hannunsa kuma ya fara yawo a jikin ta.Duk abinda yake aikatawa ko motsawa fahreeyah batayiba sai sakar zuci da tunanin ta yake tayi"""ohh allah ya saheel kana ina? Yah Allah ka taimakeni agun wannan bawa naka,"""
Rintse idanunta tayi jin sanyi ya jiyarci fatar jikinta alamun babu wata sutura da tayi mata katanga da sanyin dakin sai rigar maman dake jikinta,"""ohh allah ohh allah,koda yake bani bace,sareena tace banice bace wannan wata daban acikin wata rayuwar daban,baneee bace,😭😭😭"'""
Sun dau wani lokaci yana shafa wasu sassa na jikinta kafin ,tsayawa yayi na wani lokaci kafin yakalli fuskarta da niyyar yi mata magana,duk da yasan cewa bazata kalleshiba bare kuma mai da masa martanin amsar sa ba ,amma hakan bai hanashi yiba"
"U hmm sanyi da almun yanaso yakama ki yakamata mu isa ga kan gado danna lura jikinki har rawa yake koh,"yana gama fadin abinda ke bakinsa ya sureta izuwa ga kan gadon dake cikin dakin.
Abinda yake shirin aikatawa ya fasa tareda kallon yanda jikinta ke fitar da wani irin turiri na zafin zazzabi ga kuma jijjiga da takeyi kaman an jona mata wutar lantarki.
A dadai lokacinne kuma aka bugo kofar dakin da karfin gaske kaman ana shirin cireta,nameemah ceh a tsaye a bakin kofar tana murmushi kaman wanda ta hadiye maciji,saida ta saita numfashinta ta hanyar furzar da wasu numfashi kamin ta taka har izuwa ga bakin gadon da su fahreeyah ke kwance.
"Dama abinda aka fadamin dagaske ne mai wannan baiwar take akan gadonnan,ko bataji umarnina bane na cewa,kar wata baiwa ta tako kafar ta izuwa ga turakar da aka saukeka"duk maganar tanayinta ne cikin zafin kishi irin na mata masu jin kansu,katsata yayi da maganar da take tareda boye razanarsa yace,"nima bansaniba kawai shigowa tayi tana wani salo najan hankali sannan tace aikota akayi,"shiru nameemah tayi tana nazarin maganarsa yayinda muryar mace ta katse mata tunani ta hanyar cewa,"ehh hakane ita da kanta ta shigo domin taga bata samu inda zatayi aikiba ko kuma saboda wani boyayyen nufinta dan nima ban yarda da ita ba,"kowa kallonsa ne yakoma kanta ciki kuwa harda fahreeyah wanda tabude baki da ido tareda furta,"KIRISAH😯😯😯!!!!!

SADI-SAKHNA ceh❤❤

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now