Chp(38)kina tantama neh??

67 9 0
                                    

The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(37)

Ina ka kalli idon mutane ukun wato nameemah,nasreemah,dakuma kirisah kamar zai fado kasa dan zarowa,
"Me........me.....me,kake fadane haka amam banjika sosai ba,wacece matar taka?.....wai kana nufin wannan abar?....."
Tafada tana nuna fahreeyah dake kan gadon da yatsanta,wanda duk cikinsu nasreemah ceh tayi karfin halin yin maganar,
"Ohh kina tantama ne koh karya nake"
"Kehh ki karyata min abinda yake fada akanki mai kika yiwa mijina har yake wannan maganar wanda bata da ma'ana bare dadin ji"
"Keeh ya isheki haka kidaina yi mata tsawa ko ba kya ganin yanda yanayinta yake,ba sosai take magana ba,dan haka bazata sake bata lokacin sake yimiki magana ba ,maganinku kenan ai,kun dauki duniya wani abu,yanzu kuka fara gani"
Duk saheel ne yake yi mata magana shima da yanzu ransa yafara baci,
"Yah saheel dama kananan?"
Shine abinda nameemah ta fada cikin Mamakin ganin yayannasu,dan tsabar takaici babu abinda yace mata saimah wani kallo daya bita dashi.
Motsin da fahreeyah tayi ne ya jawo hankalin su,mika hannunta daya tayi gefen inda su khairiyyah suke da alamar su taimaka mata,yarima amam ne yayi saurin rike hannun tareda cewa cikin muryar lallashi,
"Menene yafaru?,yau kuma gani a wajen amma kike mikawa su khaleesah hannu su dagaki,hakan yasa naji kaman nagaza da hidimarki faryah"
"Ahah karma ceh haka,badan wani abu nayiba,naga matarka ta dawo tana bukatar lokacin ka a yanzu,saboda dawowarta kenan,kuma ta tarar dani a daki mijinta"
"Eh ni mijintane amma koh a ka'idar shari'ah ma wanda tafi bukatar taimako za'a taimakawa dan haka kin fita bukatar taimako a yanzu"
"Amma......"
"Amma me? Kibar wannan zancen yanzu me kike bukata kuma?"
"Bandaki zanje daga nan kuma su khairiyyah su maidani gun inna kainata"
"Zakije bandaki amma zuwa wajen Inna babu shi,anan dakin zaki zauna,itama da nata dakin idan taga zata zauna ai"
Yana gama fadan hakan ya dauketa yayi hanyar bandaki da ita,babu wanda yakalla acikin wanda suke kallonsa da mamakin,kaman bai masan an hallicesu ba.
"Tabbb"
Shine abinda nameemah ta fada bayan ta rufe bakinnata da saida ya bushe dan budewa ,jan hannun nasreemah tayi suka bar dakin itama kirisah tabi bayansu.
Bayan sun fito har bakin sashen nasreemah ne,nameemah tasake kallonta da tunanin abinda yafaru sakanni dasuka wuce,
"Nasreemah mai kika gani ? Cikine a jikinta amma fah girmansa ya isa,toh na waye,yaushe ya aureta,bayan tabar BAHMEER kenan?,amma toh yaushe akayi auren,kai wannan akwai alamar tambaya a lamarin,inaga muje wajen uwarsa muji kan lamarin zancen kawai"
"Ahah,bazamuje wajen uwarsaba,dan ba shiri muke ni da ita ba,kawai muje wajen sarauniya zulaikha dan wajenta zamu fi jin mai ya faru,dan nafi yarda da ita fiye da wannan mahaifiyar tasa"
Sashen sarauniya zulaikha suka nufa cikin Mamakin abinda ya faru.
Nameemah ceh ta kalli kirisah kafin tace,
"Kekam kije masaukinmu ki jirani dan bana bukatarki ana din"
"Toh rank I yadade"
Da saurin jikinta ta bar wajen,bayan ta tafine nasreemah ta juya ta kalleta,kafin ita tace,
"Amma ina kika ce mijinki ne kadai a sashen kuma kika turata wajensa?"
"Oh ba komai ko acan ma bana yarda da bayin masarautar su ita kadai ce take share masa sashensa ta gyara"
Mantar da zancen nasreemah tayi bayan tace toh,dan abinda yake gabanta yanzu yafi na wannan din,baiwar da take tsaye a baki sasheb suka kalla,
"Ke miye kuma na tare bakin kofa baki gane ni bane?"
"Ranki yadade dazu gimbiya NEELAH tazo,toh sarauniya tace ko waye yazo ya jira tukunna"
"Dallah ga fara kuma dan neelah tazo saina kasa shiga,ko kin manta ko iso ba'a min a sashenna?"
"Yi hakuri ranki yadade"
Gefe taza da sauri su nasreemah suka wuce cikin falon sarauniya zulaikhan.
Tun daga bakin kofa suka ja suka tsaya suyi magana jin abinda yake fitowa daga bakin Sarauniya zulaikha,
"""Haryanzu nace da saurinki amma kina cemin kin gane komai,wace shawara Kika taba kawowa,tun bakida wayo nakeyi ni kadai,tun daga kan zubar da cikin dana dungayi ga safeenah,da asirin danayi na fitar da son amam a ran mai martaba har ya koreshi daga masarautar nan,ko kuma da yaudarar nasreemah da nayi har nasamu nasarar bata maganin hana haihuwa tasakawa amam,wanne kikayi aciki,yanzu dole ki tashi tsaye,yanda zamu halakar dashi saboda manneer ya hau sarautar nahiyar nan,na san nasreemah ba dawowa zatayi ba,saboda zugar danayi mata,kinsan batada wayo ko kadan,kata da yarda da wuri,dan haka ki hanzarta kisamo mana mahadin maganin............""""
Saurin fitowa nasreemah tayi a kofar itama nameemah tana bin bayanta,ba abinda yake bin fuskar nasreemah sai hawaye da kuma dana sani da takaici da suka cunkushe a cikin ranta,nameemah ceh taja hannunta ganin yanda take kokarin fita waje a haka,
"Ke ki tsaya haka,mekike kokarin yi,so kike su gane munjisu kuma?,share hawayanki kiyi kaman baki jiba saimu koma muyi musu sallama,in kika gaisheta saimu fito musan abinyi"
Hawayen tashare batare da tace komai ba suka koma cikin falon ita da nameemah.
"Assalam,umma barka da warhaka"
Da mamaki zulaikha ta kalleta saikuma ta daure tareda cewa,
"Ahh yar albarka kece a gidan,yaushe kika dawo kuma,ince dai ba dawowa kikayi ba koh kuma sakinki kikazo karba?"
"Ahah babane yace nadawo,Amma gaskiya dole nasan abinyi koda menene kuwa danganin na raba auren dan bazan Zauna dashiba"
Murmushi su zulaikha sukayi itada NEELAH wanda tun gaisuwar dasukayi bata sake yimusu magana ba,
"Hakane kam,dole za'a san abinyi don bazai yiwu a cutar dake ba nayi shiru"
"Nagode ummah bari mu karisa cikin gidan,zan dawo musan abinyi"
"Shikenan Y'a ta,a huta gajiya"
Bayan sun fitone sunyi nisa da sashen Zulaikha nasreemah ta rushe da kuka,dama da kyar da rikeshi ta fadi abinda nameemah tafada mata,
"Wayyo nameemah,kiga abinda na aikata,ashe nina nakasa rayuwarsa da kaina,kuma nake ta goranta masa hakan,kaicona da wannan yardar tawa da kowane irin mutum,bazan taba yafewa kaina ba yanzu dan ji nakeyi kaman na mutu a halin yanzu"
Itama nameemah kuka tafara kafin tasamu karfin gwiwar lallashin yar uwar tata,
"Lokacin ki bai kureba tunda har kika sani da wuri,yanzu dai muje sashennaki asan abinyi,tunda yah saheel ma yana nan"
Hanyar tafiya sashennata suka nufa wanda har sannan nasreemah bata bar kukan da takeba.
A wajen su fahreeyah kuwa kowa harkar gabansa ya cigaba da yi sun ma manta da wasu nasreemah sunzo,yanzu a falon gidan suke ana ta zance shima saheel din bai tafiba,bai ankara ba sai jin mutum yayi yah rungumeshi yana kuka,khaleesah da take gefensa saurin ja da baya tayi dan ganin mai yake faruwa.
Ganin nasreemah a jikin saheel din tana kuka kamar waninta ya mutu sai kallo yakoma kan nameemah wanda itama hawayen take sharewa,saheel dinne da yanzu ya dora hannunsa a bayan nasreemah yana bubbugawa alamar rarrashi yayi karfin halin  tambayar nameemah abinda yafaru.
Dukkansu babu wanda bai cika da mamaki ba dakuma bakin ciki,da sukaji abinda nameemah ta fada musu wanda su sarauniya zulaikha suka aikata,toh wata sabuwa mai kuma zai faru???

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now