Chp(43)finally💃🏼💃🏼💃🏼

126 17 1
                                    

The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(43)finale!!!
"Dagaske ne abinda nakeji fahreeyah ko mafarkine?"
"Ummah dagaske neh,saheel shine ashe yarima amam na masarautar sardaham,abubuwa da yawa sunfaru yakamata muzauna saikiji komai"
Yadda tayi da abinda fahreeyahn tace,saidai amam ne yakatsesu ta hanyar cewa,
"Ahah daganan ummah gidanku zamu wuce dan sunsan da zuwanmu,dama ke kadai mukazo dauka kawai"
Tayi Mamakin abinda yace,amma batace komaiba sai amsa masa da toh,takalminta dake bakin dakinta tasaka suka nufi hanyar waje,ko ta kan aryana basubi ba,wanda taketa musu borin koro kunya,
"Mekuke nufi,saiku bani kudin yanda nasiyesu kafin ku tafi,tunda bazaku bani dan wani abuba na ladan rikesu danayi saiku bani kudin yanda na siyesu.
Dama kaman jira dakarun sukeyi amam yana musu alama da ido,suka hauta ds duka kaman an aikosu,saida sukayi mata karaya ta kusa biyar a jikinta kafin suka bar wajen.
Mamakin saukar da aka musu a gidan su hudan shiya fi basu mamaki matuka, bayan sun hutane,kowa yafara zuwa suna gaisawa,ananne huda taji labarin rashin lafiyar mahaifinta da kuma rasuwar mahaifiyar ta,bakaramin girgizata abin yayiba.
Lokacin data je dakin da mahifinnata yake ,a kwance ta ganshi da alamar tsufah,karisawa tayi wajensa itada fahreeyah,rike hannunta yayi gam,
"Kiyafemin huda na korarki danayi daga gida saida ga baya nagane kuskuran dana aikata"
"Karkace haka Abba nayafemaka,nima kayi hakuri na abinda na aikata"
"Bakomai,wannan itace y'ar ki koh?(yah fada yana mikawa fahreeyah hannunsa,itama kamawa tayi tana yi masa Sannu),da rabon haihuwarkine,kiyi hakuri da abinda na aikatawa iyayenki"
"Ba komai Baaba,komai yah wuce"
Satin su fahreeyah daya a garin bardugu suka koma sardaham,bayan fahreeyah tayi ta rokon ummah ta tabisu amma taki,tace zata zauna a wajen mahaifinta tunda ita kadai ce mace.Tayarda zata dinga kaimusu jiyara su ma sai suzo insunyi niyyar zuwa.
Shekarar y'ay'an fahreeyah biyu ta yayesu saboda yanayin girmansu dakuma ishashshen abinci.
Yau amam a sashen nasreemah yake,bayan yaci abinci suna dan taba zance kafin yafita,fahreeyah ce ta shigo da sallama hannunta dauke da abeeh,dakuma akwati a hannunta,samun waje tayi ta zauna tareda yimusu barka da zama.
Nasreemah ceh tafara yimata magana tareda cewa,
"Ummin feena wani waje zakijene,kuma da abeeh nah kadai za'aje?"
"Ahah babu inda zamuje"
Ajiye akwatin tayi a gefen kujerar data zauna,kafin ta koma kujerar da nasreemah take kai,hannunta ta rike acikin nata kafin tace,
"Tunda ga ranar dakika gane matsayina a wajen amam baki taba yimin muguntaba,kin jure zama a kusa dani lokacin dana ke kan nakuda,Sannan kin rike su abeeh tamkar y'ay'an dakika haifa ba,Sannan yan uwankima sun rikeni tamkar yanda suka haifeki,babu abinda zan iya sakamiki dashi yar uwata,abu dayane nasan inada halin yimiki yanzu saidai bazan biyaki abinda kikaminba da kuma wanda zakimin a gaba.........nabaki shiraim(abeeh) halak malak har yakoma ga mahaliccinsa inaso yakasance d'a a gareki kuma ko ina za'a je inaso a nunaki amatsayin mahaifiyar sa,sannan ban yadda wani ya gorantamiki bake Kika haifeshiba.
Dan haka ga kayansa nan nabakishi ko a shari'ah yanzu zai amsa sunan d'ankine"
Koda tagama bayanin ba iya nasreemah ceh ta girgiza da maganar fahreeyahn ba harda amam wanda shima baisan da maganar ba sai yanzu.
Ganin basuce komai ba yasa fahreeyah aje abeeh akan cinyar nasreemah tana murmushi kafin takara cewa,
"Nayarda dake nasan zaiji dadin kasancewarsa danki kuma zaiyi alfahari dake,sannan banson kiji a ranki wai d'anane bazakiyi masa wani abuba"
Ficewa tayi daga parlorn batareda tasake jiyowa ta kalli abeeh dinba,bayan ta tafi andade kafin nasreemah ta sauke wani numfashi kafin ta manne yaron a kirjinta kaman zata mayar dashi cikinta,wani nayayyan kuka tasaki kafin tace,
"Hubby kaganifah an bani kyautar d'a an bani d'a nima,kuma dama mafi soyuwa ne a gareni,ina sonsa sosai,zanyi komai dan farincikinsa dakuma tarbiyyantar dashi,Allah yabani shi lokacin da bansan zan sameshiba"
"Bakomai kiyi shiru haka hubby saboda tasan zaki kasance uwa ta gari shiyasa ta baki shi,ina miki fatan allah yatayani riko,ita kuma allah yasaka mata da alkhairi"
"Ameen ameen Ameen"
Cikin kankanin lokaci labarin kyautar d'an da fahreeyah ta bata,saboda duk inda aka zauna saita bada labarin abinda fahreeyahn tayi mata,ita kanta safeenah godiya ta musamman tayi mata,bare kuma safeenah wanda tayi godiya har ta gaji.
****       ****          ****
Bayan shekara biyar

Fahreeyah ceh a zaune tana karatun littafin addini,tayi yar kiba ta murje kaman ba itaba,feenah ce tashigo da gudu hadeeyyah na biyeta a baya,
"Ummi kinga abeeh ko yana mana dariya dan ammeeh(nasreemah)ta je dashi anguwa shine yakemana dariya"
"Bawaninan kune da tsokana,kuma shima watarana ai kuna tsokanarsa idan naje daku anguwa bandashi,maza kuje gun ammeeh taku ku cemata inta shirya zamuje dauko ummah munneer mu dasu ummah,kuyi sauri"
Wa'adin shekarar da aka dibawa neelah yacika su nasreemah sunje sun daukota,itakuma zulaikha ta haukace sosai har an kaita gidan mahaukata,duk wanda yaga neelah sai yah tausaya mata saboda halin data shiga.
Haka aka hadu a sashen safeenah kowa na farinciki na dawowarta da kuma hadin kan yan uwa,ba abinda take sai murmushi dakuma danasanin abinda ta aikata.
Washagari mijinta yazo suka tafi tareda danta zuwa garin da take aure bayan ta nemi yafiyar abinda ta aikata.
Fahreeyah ceh a zaune tana kara nazarin karatun litattafai bayan masu kulada su feena sun kaisu wajen kwanciyarsu,Sallama amam yayi tareda zama akan gadon kusada ita,
"Faryah tah,tazama babba ta kara girma,amma a wajena tananan kaman wanda take bin fonnee domin suyi wasa"
"Nima zaujee na yah girma Amma yana nan a kaman wanda yake guduwa baya zama a gida saboda yana tsoron fahreeyah"
Rungumeta yayi a jikinsa suka fada kan gadon suna dariya,
"Hmm yarinya zaki sani a bayane nake gudu amma yanzu babu zancen gudun,saima nema danake ana cemin an gaji"
"Yaushe nace nagaji"
"Tunda baki gajiba fari a fara sabon shafi"
Jan bargon gadon yayi ya rufesu suna ta dariyah😍😍😍😍😍❤❤❤❤❤❤

TAMMAT BIHAMDILLAH

ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFINNAN MAI SUNA WATA RAYUWA,WANDA NA BATAWA RAI YAYI HAKURI,SANNAN IN BAKAYIN COMMENT KUMA ANA TAFIYA DAKAI A LITTAFINNAN,TOH KAYI COMMENT DIN BANKWANA.

JINJINA GA DAUKAKIN MASOYAN WANNAN LITTAFIN NAGODE MUKU SOSAI,SAI MUN HADU LITTAFI NA GABA MAI SUNA:
(GIDAN GANDU )
ALLAH YASA NASAMU HADIN KANKU,
PLEASE AYI
COMMENT
LIKE
SHARE
NA BANKWANA MAKARANTA,NAGODE ALLAH YAH TAIMAKEMU.❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 29, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now