Chapter(11)zan bar nahiyata

61 9 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(11)

sarauniya safeenah ce a zaune fuskarta dauke da damuwa hawaye na zuba a idonta ,duk da karfin hali irin nata a yau ta zubda hawaye saboda rabuwa da zatayi da danta da kuma zafin irin kiyayyar da mai martaba yake masa bayan a da ba haka yake masa ba .
Tsayawa tayi da kukan jin alamar shigowa turakar tata ,ko ba a fadamata ba ,daga jin yanayin takun tasan yarima amam ne ,goge hawayen idonta tayi cikin dabara kafin tajuyo da fuskarta izuwa gareshi.
Matsowa yayi kusa da inda take daune ,kafin ya ajiye jakar dake rataye a kan kafadar sa ,muryarta cikin rauni tafara fadin ,
"yanzu menene sunan abinda kayi amam ?dama sokake kadaina kallona ko ,menene yake damunkane haka ?"
"ahah ummah karkice haka ,duk da zan bar nahiyata ,bazan taba iya mantaki ba ,kunmin duk wani abu da d'a yake bukata a wajen iyayensa kuma sannan  inda rabo watarana zamu hadu ,inaso kicigaba dayimin addua ,kuma kobayan natafi in abba ya nemeni kice ina naiman afuwarsa "
"yanzu dagaske kake ? daka yi aure gwara ka rabu damu ?"
"kiya femin ummah amma haka zancen yake ,dana zau na kusada mace gwanda gawata ,haka nakeji acikin raina "
"shikenan ina maka fatan alkhairi "
"nagodee ummah ".
Haka tafiyar ta yarima amam ta kasance ,ya fita daga cikin nahiyar tasa batare da ko nadamar zabin da yayi ba .
          。。。。。。。。。。。。
Datunanin maganar da
mukayi da saheel na kwana a raina ,dan gaskiya abin yadaure kai sosai .
"Fahreeyah tunanin me kike haka naga kin zurawa waje daya ido uhmm ?"
"ba komai ummi kawai ina tuna rayuwarmune "
"kidaina hakan karna sake gani kinji ,bai kamata mai shekaru irin naki tafara tunani ba "
"shikenan hakan bazai sake faruwa ba "
"yawwa yar albarka "
suna cikin harar su mai dadi irin na y'a da uwarta saikuma sukaji dodon nasu ,wato muryar aryan ta kadamusu hantar ciki ,
"wane irin iskancine bazaku fitoba kuke wani kus kus a daki ,munafukai ,to kujo kowa ta kama aikinta ,badan kuji dadi na siyeku ba tohh "
fahreeyah ce tafara fitowa tana bin jikin bango ,kafin huda itama ta fito ,kallonsu take idonta kaman zai fita dan masifa kafin tazuya tana kwafah .
Dayake kowa yasan aikinsa babu wani bata lokaci huda ta fara shirye shiryen dora abinci yayinda fahreeyah ta dauki tulunta tayi hanyar rafi .
Tafiya take tana kalle kalle har ta kai ga wajen deban ruwan ,jikinta ne yayi dan sanyi ganin ba babu saheel shida fonee a wajen ,har tajuya zata tafi saikuma suka duro a gabanta suna dariya ,da alamar yimata bazata ,itama dariyar tayi tare da rungume fonee a jikinta ,kallonsu saheel ya tsaya yana yi fuskarsa dauke da murmushi ,ya ayyana wani abu a ransa dashi kadai yasan manufar sa .
fahreeyah ce takatse masa tunanin daya ke ta hanyar cewa ,
"yah saheel kaga fah fonee ya dauke min gyalena ya gudu koh "
"zama yayi a wajen da take zaune ,ta cunoo baki gaba ita a dole ta kai kara ,murmushi yasake yi kafin yace ,
"idan kina wani abu FARYAH ,kaman y'ar karamar yarinya ,idan kika barshima a zai dawo da shi ko ?"
shiru tayi amma babu alamar ta yadda da abinda yace din ,saidai kuma ko me ta tuna ?,sai kuma ta dawo da murmushi kan fuskarta tareda cewa ,
"uhmm dama zancen mu na jiya yahh saheel ,menene mafitar dakace kana da ita akan rayuwar tawa ?"
"kin yi magana da mahaifiyarki kaman yanda mukayi ?"
"ahah bamuyi magana da ita ba "
"tohh miyasa ?"
"babu komai ,kawai dai bansan yanda zan yimata zancenka bane ,kuma danaji kace idan inason rayuwata ta sanja ,dole sai nayi nesa da ita ,sai hakan ya sacemin gwiwa ,banason rabuwa da ita yah saheel ,ita din rayuwatace "
"ba rayuwarki bace ,da rayuwarkice kaman yanda kika fada to hakika zaki sanja wannan rayuwar taki faryahh ,kowa da kika ganshi akwai wani abu dayake yaki da shi a rayuwarsa,karki kasance mai jiran sai anmiki yaki a rayuwarki keda kanki zaki sanja komai faryah ,keda kanki ,sannan hakan bazai yiyu ba sai kin jure kinji ?"
jikinta ne yayi sanyi da kalamansa ,haka kawai takejin kaman akwai abinda yake shirin faruwa da ita ,batare da tace masa komai ba ta tashi ta dauki tulun ruwanta ta dora a kai ,kafin tace ,
"na gode da kulawarka da kuma bani shawara a kullum yah saheel ,sai gobe ,bari natafi karna dade "
"yau bakisan rakiyanne ?ko akwai abinda yake damunki ?"
"ahah bakomai ,zan iya tafiya ma "
"shikenan ki isa lafiya "
"tohh "
tafiya ta ke kwata kwata bata kallan gabanta ,saida tayi tuntube da dutsi kafin hankalinta yakai kan abinda dake ,ba komai ne yake dawowa cikin kwakwalwar ta ba illah maganganun da saheel ya fada mata ,tunani take a ranta to taya ne zata sanja rayuwarta ?.
Dahaka ta isa gida ta juye ruwan data debo a randar aryanar ,dakinsu ta shiga inda mahaifiyar ta ta ke zaune tana dan lashe kwanon da saka musu kanjon abincin datayi ,dagowa tayi da idonta ganin y'ar ta ta a tsaye a bakin kofar ,saida ta shigo ta zauna kafin ta miki mata nata abincin a wani dan kwano dayake gabanta ,dauka tayi itama tafara ci ,dan dama yunwace a cikin cikinta .
Bayan sun gama cine ,sukaji muryar aryana tana kiransu daga waje ,fitowa sukayi suna kallonta kafin tace ,
"yawwa inaso na fada mukune cewar ,anfara neman bayi a kasuwar shekarar nan,dan haka ke fahreeyah ki shirya dan nasa ka sunanki a cikin wad'anda za'a sayar min ,banaso nakara ganinki kin yi wani aiki ,sonake a ganki bulbul ko zakiyi daraja ,da daga gani za,a samu kudi ,hungo nan abincine kidinga ci kina koshi "
tafada tana mika mata kwano cike da abinci aciki ,da taga bazata karba ba dangwara mata a gabanda tayi gaba ,tana kara tabbatar musu da jawabinta ,.
Har tagama bayaninta tabar wajen fahreeyah basuyi ko motsiba saboda wata irin razana data bugi girjinsu saboda jin furucinta ,huda ce taja wani dogon numfashi mai karfin gaske ,wanda duk kamewar  da fahreeyah tayi saida tazuya da kallonta zuwa ga mahaifiyar ta ta .

          SADI-SAKHNAce 😊

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now