Chapter (21)zan ci amanar mijina😥!!

49 7 2
                                    


(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

chp(21)
"Nikuma???, Sareenah bakyajin mai yace wai,wai zan kasance masu tarar baki a gobe"
"Eh naji fahreeyah, yakamata ki daina damun kanki akan wannan rayuwar daki ka tsinci kanki hakan ba komai zai haifar ba illah cutar da zuciyar,idan har hakan zai baki wuya inaso ki rufe idonki kana ki dauki akanki a matsayin bake bace a yanzu fahreeyah, banason naganki cikin damuwa haka,dan Allah karki kasance cikin wanda basa yarda da kaddara a rayuwar su,kinji?"
"Inaso nayi kokarin hakan Sareenah, saidai zuciyata ta kasa aminta da hakan kwata kwata"
Takarisa maganar cikin kuka da karayar zuciya ,
"Zaki iya fahreeyah ni nasan zaki iya"
Dahaka Sareenah ta cigaba da karfa fa mata gwiwa akan abin har takai ta fara kwantar da hankalinta, mutane ne suka fara zagaye su, Wanda ganin hakanne yasa Sareenah janta daki suka bar wajen.
Kaman yanda aka tsara kuwa haka abin yake tafiya domin washa gari zalziliyyah tazo ta tafi da wanda zasu kasance masu tarar bakinnasu wanda zasu iso da maraice, fahreeyah ce ta marairaice zata fara kuka, inda Sareenah tacigaba da bata hakuri da karfafa gwiwa har ta amince da yadda da kaddar tata,
Kwalliya aka fara musu tareda kara yimusu bita akan aikin dazasu gabatar,ba abinda yake a cikin zuciyar fahreeyah illah fargaba da kuma bakin cikin cin amanar mijinta da take shirin yi,bayan angama ne ta dan koma dakinsu kafin lokacin dazasu shiga cikin fada yayi.
Zama tayi a gefen Sareenah tayi shiru kamar mai tunanin rasa wani muhimmin mutum a rayuwar ta, zabura rayi jin dafata da da Sareenah tayi,
"Yanzu har yanzu baki cire abinnan a ranki ba fahreeyah?"
"Ahah Sareenah bahaka bane,ina jin tsoro a cikin raina kuma ina jin zafin yanda dazanci amanassa a wannan ranar Sareenah 😭😭😭"
"Wa zakici amanar, fadamin"
"Mijina, Sareenah zanci amanar mijina a yau,idan kaddara tasake hadani dashi da wane ido zan kalleshi?"
"Toh wata sabuwa,amma meyasa baki taba fadamin ba har saida lokaci ya kure, yanzu bansan wane irin taimako zan miki ba a halin yanzu"
"Karki damu yar uwa banaso ma nasaka ki cikin wani Hali nagode da taimako na ma da kika yi a baya, yakamata na fidda ran sake kallon sa ma a karo na biyu a rayuwata, kuma bana da tabbacin zai amince dani idan ya kalleni a matsayin baiwa a halin yanzu,bari na tafi kar zalziliyyah tazo nema na"
Batare da ta tsaya sake jin wani abu daga wajen Sareenah ba ta juya tareda fara tafiya cikin kayan ta da aka mata kwalliya da su,suna daukar hasken rana a jikinsu.
Fadar BAHMEER ce ta cika da mutane da kuma masu busa sarewa da algaitu, Wanda duk wanda yagani yasan cewar bako mai muhimmanci za'ayi a cikin masarautar.
Yariman masarautar HAIRAAN ne ya babban tattaki domin zuwa ga masoyiyar sa gimbiya
NAMEEMAH kasance war dama ita kadai ce a gida anyi auren yayarta da dadewa.
Duk wanda yaga gimbiya Nameemah a wannan ranar yasan tana cikin farin ciki da zuwan masoyinnata.
Masauki aka fara kai kowane bako daya taho tareda yariman, sannan kowa aka kaimasa wacce zata dauke masa kewa a lokacin .
A bangaren su fahreeyah kuwa lokacin da aka kaisu ga masaukin bakin sai yakasance kowacce an kaita inda zata kasance saura fahreeyah kadai,kasancewar dama sauran bayin zumudi suke da kwanan dazasuyi da bakin shiyasa kowa yasamu inda zaije itakuma aka barta ita kadai, zalziliyyah ce takalleta tareda cewa jirani yanzunnan na dawo mu tafi,kiyi hakuri baki samu aikin dazakiyi ba,
"Toh bakomai"
Tsayawa tayi tana jiranta ta dawo daga inda tace ta jirata take ta dawo,ita kadai take murmushi jin cewa ba da Wanda za'a hadata su a Daren kamar yanda aka tsara,tsayawa tayi da murmushin da takeyi hade da murmushi,jin muryar da ko a mafarki bataso sake jinta,
"Uhm fahreeyah me kike anan ke kadai? Dama shugaba zilziliyyah tace narakaki dakin dazaki yi aikinki Dan haka kizo muje ko"
Tsayawa tayi tana kallonta batare da ta motsa kafarta domin Binta ba,
"Wai ba magana nake mikiba ne kike jina batare da kin taho ba,ko Dan kinga ina lallabaki iyee?,"
Saukar da kanta tayi daga barin kallonta saboda haka kawai take tsoron kirisar kamar ajalinta,ganin alamun da kirisah ta ganinne a fuskar fahreeyah ne ya tabbatar mata da cewa,hakarta ta fara cimmah ruwa kamar yanda ta tsara.
Tafiya take tana wani kwarkwasa yayinda a bangaren fahreeyah kuma tafara binta a baya kaman rakumi da akala,tafiya sukeyi ta wani siririyar hanya mai tsayi Wanda zai sada su da inda take burin kaita.
A gaban wata kofa suka tsaya,wanda ko daga ganin yanayin yanda aka kebance dakin daga sauran dakunan zaibawa mutum damar cewar dakine na musamman a wajen.Kallon kallo suke tsakanin fahreeyah da kirisah yayinda kowa da abinda yake sakawa acikin ransa,shirunne daya fara alamun zaiyi yawa yasa kirisah gyaran murya kafin tace,"uhm dama wannan dakinne inda zilziliyyah tacemin na kaiki,sai a bashi nishadi kamar yanda yadace ,dan shine dama aikiniki koh?",
Had da juya tafara tafiya,har saida takai karshen hanyar dazai sadata da barin wajen kafin tajuyo takara kallonta ,"ohh namanta ban fadamiki yanda akeyi ba,kodayake tunda gar kika shiga matakin manyan bayi ai nasan kin iya komai bakya bukatar wani maimaici,sai anjima allah yabada sa'a,"tafada tana daga mata hannu tareda yimata dariyar mugunta.
Saida alamun wanzuwar Kirisah yabace daga wajen kafin fahreeyah taza wani ajiyayyayen numfashi mai dauke da ajiyar zuciya tukunna ta maida kallonta izuwa kofar dakin da aka bata a matsayin inda zatai aikin ,har ta rike marikar kofar zata bude sai kuma wani tunani yazo mata tare da faduwar gaba ,sakar zuci tafayi ""to idan kuma abinda kirisah tafada mata ba gaskiya bane kuma fah ,kawai tayi mata haka ne dan batasonta ,kuma tana nufinta da mugunta?"""sakin hannun kofar tayi cikin sanyin jiki tareda juya zata bar wajen ,wani tunanin ta sakeyi akaro nabiyu cewar"""idan kuma dagaske ne zilziliyyah ce ta aikota fah,sannan kuma idan aka gane ta bijirewa umarnin da aka bata wane hukunci zata fuskanta a wajen shigabar bayi (zilziliyyah),""saddakarwa tayi kawai tayi ,tareda juyawa tabude kofar dakin tasa kanta a hankali,saida takarewa dakin kallo a haka kafin karisa shiga tareda maida kofar dakin ta rufe.

Sady-sakhna😍 ceh

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now