Chp(40)ku kama ta!!!

59 9 0
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(40)

Komawa dakin da su fahreeyahn suke takoma,har sannan suna abu daya yanda tabarsu dazu,tsugunnawa tayi daidai wajen ds yarima amam yake,
"Naji duk abinda yafaru a wajen su saheel a waje,hakika abinda nafada maka ya tabbata nacewa komai nufi ne na allah,kuma gashi kinga ni yanzu,dan haka ku daure Wannan jarabawar dasannu zata gushe kamar ba'a taba yiba,ke kuma Y'a ta kicigaba da kokari allah yasaukeki lafiya,haka kema nasreemah naji abinda yafaru dake,karki damu komai mai wucewa ne kinji,ni zan tafi kar asan da zuwana nandin,dan babu tsaro idan zaman fahreeyahn yafita cikin fadar a yanzu,zan turo sameerah ta kawomuku ruwan addu'a,a tabbatar cewa an shafa mata kuma tasha sosai,kema inna Kainata sannu da kokari allah yasaka da alkhairi"
Dukkan su kowa jijjiga mata kai yayi tareda jin dadin maganganun ta.
Lokacin da ta isah sashennata kiran sameerah tayi ta shaida mata duk abinda yake faruwa kaman yanda saheel din yafada mata,itama ba karamin Mamakin abun tayi ba.
Cikin sauri kuwa safeenah tahada duk abinda yakamata ta bata dan ta kaiwa inna kainatan.
Washa garin zuwan safeenah wajen fahreeyah sai yazama abu yakara gaba gaba saidai haryanzu babu alamar fitowar kan jinjiri daga jikinta saidai wuyar da take sha,duk abinda ake kuwa amam yana makale da ita wani lokacin yayi kuka wani lokacin kuma yah karfafa mata gwiwa,itama nasreemah a bangarennata kasa tashi take ta bar dakin ko nan da nan ne,sai yazama dole tukunna.
A wajen safeenah kuwa ba abinda yake ranta saina takawa su zulaikha burki wanda,tahakanne hanklinta zai kwanta kawai.
Aikawa tayi aka kira mata nameemah wanda itama take zaune taki tafiya saboda abinda mijinta yayi mata,daki suka shiga ita da sameerah da nameemah wanda babu wanda yasan abinda suke fada aciki.
A wajen zulaikha kuwa yanzu tafara tantamar akwai wani abu,ganin nasreemah tayi kusan kwana uku bata zo wajenta ba,wanda a lokacin baya saita shigo wajennata kusan sau uku a rana.
A zaune take a baje akan kujerar parlorn,rike da wani magani a kulle a takarda,neelah ceh ta kalli maganin a hannunta,wanda tayi shiri yau zata koma gidanta itama,
"Maganin damuke ta nemane,yanzu gashi nasaka an karboshi,saidai bansan yanda zamuyi ya isa ga wanda muke hari ba........."
"Ni nan zan isar mukushi inda kuke so yaje"
Dukkansu juyawa sukayi a kidime dakuma Mamakin ganinta a dadai lokacin.
A can wajen fada kuwa ana zaune su waziri da galadima da sauransu sun gewaye sarki wanda yake kan kujerarsa ana ta sasanta matsala kaman yanda aka saba,sameerah ce ta kutso ciki fadar tana haki kaman wanda aka biyota a bayanta,
"Mai.......martaba,sashen sarauniya Zulaikha......,uhm uhm sarauniya safeenah ma tana can tace nazo na kiraka da sauri"
Kowa mamaki yayi can kuma,sai sarki huruddeen ya mike tareda cewa dakaru guda biyu su biyoshi,dan ya je ganin abinda yake faruwa.
Bayan sarki yabar fadar jikin wazirine ya yi sanyi haka kawai bai yarda da abinda sameerah taceba,tashi yayi yah tafi gida domin shaidawa mai dakinsa wato uwar zulaikha.
Lokacin da sarki huruddeen ya iso bakin shiga parlorn zulaikha ne yayi arba da safeenah a bakin wajen,alama tayi masa da hannunta akan yayi shiru kafin ta nuna masa ya matso inda take,har yabude baki zaiyi magana saikuma kunnesa yajiyo muryar zulaikha dadai lokacin dazata mayar wa nameemah amsar maganarta....................
Menene dalilinki na zuwa,sannan kuma kice zakiyi mana aikin damuke son aiwatarwa,mai kika sani game da abunda yafaru?"
"Maganar da kukayi lokacin da muka shigo da yar uwata nasreemah ita nasani"
Neelah ceh takalli nameemah da mamaki kafin tace mai kika ji a maganar?"
"Naji komai,yarda kukayi amfanin da yardar nasreemah har kuka saka ta ta zubawa amam maganin dazai kashe kwayoyin halittarsa,duk naji komai,amma karku damu saboda ita babu abinda taji a maganar taku,domin cewa tace nashiga tana zuwa tayi mantuwa,ina tsaye duk naji abinda kukace"
"Amma duk da kinji abinda muka fada nida NEELAH kuma yah cutar da auren yayarki meyasa kikazo yimana aiki?"
"Saboda nice nake son yarima amam itakuma ta aureshi,toh dana ganta tana zaune dashi gwara kowa yarasa,ku kuma idan nayi muku aikin,da sharadin idan mulki ya dawo kanku bazaku manta daniba,dan haka ku fadi me kukeso na aiwatar,cikin sauki zanyi batareda kowa yasaniba"
Murmushin mugunta zulaikha tayi tareda jin dadin maganar da nameemah tayi,
"Haka akeson mutum karya bar kota kwana,yanzudai tsrinmu nagaba shine kawar da amam a doron kasa,dan naga kaman tsarin hanashi haihuwar bai gamsu mutane ba,zasu iya dora shi mulki duk da haka,daga baya kuma idan muka yi magana da babana zamuyi kokarin kawar da shikansa sarkin,sai babana ya hau,idan lokacin manneer shikuma ya girma sai ya karbi sarautar yacigaba dayi"
"Toh itakuma sarauniya safeenah fah"
"Hahaha wannan karamar alhakice,bukatata nagama da manyan tukunna,daga baya saina dawo kanta,sai tayi da tasanin haihuwar d'a na miji akaina,............"
Katsewa tayi da maganarta ganin mai martaba tsaye akanta idonsa yayi jawur dan bakin ciki da kuma tashin hankalin abinda yaji da kansa,safeenah kam mai raunin zuciya kuka take kaman ranta zai fita sai sameerah ceh ta riketa.
Zulaikha ceh ta kalli nameemah wanda take mata Murmushin gefen baki na alama lokacinta yakare,maida kallonta tayi kan mai martaba wanda yadauke Kansas daga kanta yana runtse ido,cikin murya dakyar yayi wa dakarun dake bayansa magana,
"Ku kamata ku kaita kurkun jinin sarauta daga itah har neelah,ku tsaresu a wajen sai gobe zasu amsa abinda sukace"
Juyawa yayi ya fice,itama nameemah bin bayan su sarauniya safeenah tayi sukabar wajen.
A wajen su inna kainata kuwa dasu nasreemah basu ma san mai ake cikiba,hankalinsu gabadaya ya tafi ga fahreeyah wanda nakekan nakuda har sannan,daga baya kanma,nakudar tsaywa tayi kaman wanda aka ce tatsaya,har ta samu ta kwanta bacci mai nauyi,suma ganin hakanne yasa suka dashi daga inda suke kowa yafara wani dan uzirinsa,ta dade tana bacci har duhu yafara shiga.
Can wajen darene da misalin 1:00am,amam yaji tanajan hannunsa,tashi yayi da sauri yaganta a kasa wanda bai ma san sanda ta sauka ba,saukowa yayi inda take ,
"Yah amam inaga haihuwar tazo dan inajin kaman kai a wajen cinyata"
Tashi yayi zai fita kiran inna tayi saurin rikeshi tareda cewa,
"Karka kirata ta wahala Dayawa,inkarikeni ma ina ganin zan iya"
Dawowa yayi ya riketa kam,itama ta rikeshi tareda tattaro duk wani guntun karfin jikinta,wani irin nishi tayi,kaman almara saijin kukan jinjiri sukayi a kasan fahreeyahn,kallonta yayi kafin ya kalli jinjirin dayake gabanta yana cewa,
"Yanzu kam yakamata a kira inna dan ta gyara ki,dan bansan yanda zanyi ba"
Daga masa kai tayi kafin ya fita da sauri.
Dakin nasreemah ya kwankwansa inda suke kwance itada innan,suna kallonsa nasreemah tayi saurin cewa,
"Nakudar cf ta dawo?"
"Ahah haihuwa tayi yanzunnan"
Dasaurin su suka nufi dakin da taken,har wani na riga wani zuwa,turus sukayi a bakin kofar har yarima amam din sabods abinda idon su yagane musu,kam sukayi kaman an dauke ran dake jikinsu tashi daya,har aka rasa wanda zai fara yin gaba dan karisawa cikin dakin.
Itama fahreeyahn a nata bangaren kallonsu take,idonta yana kaman zai rufe saboda tsabar galabaita da tayi ,kafin du iso gareta kuwa har ta fadi a wajen sumammiya.
  Toh mesuka gani haka,saimun hadu a chapter ta baba inshaallah.........

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now