Chapter 03(Inada mafita 🤔)

166 13 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist)🌄🌄🖌️🖌️

Written by ❤️♥️"sadi sakhna"❤️♥️

💎💎.....WATA RAYUWA....💎💎

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

(03)
Razana tayi da kuma alamar tausayi sosai akan fuskarta,ganin kafar abun tashiga tarkon da akayiwa kananan dabbobin dasuke rayuwa a wajen,karisawa tayi tazauna a kusa dashi,amma da sauri taza da baya ganin yana mata gurnani,murmushi ta masa ganin yanda yayi sai ya bata dariya,yayinda shikuma murmushinnata yabashi mamaki ganin bata da tsoro sai ma dariya datake masa,itakuma a bangarenta kallonsa takeyi ganin ya karu fiye da yanda ta ganshi a shekarun baya,dagawa tayi tana kallon fuskarsa yanda ya tsaya yana kaa saikuma ta tuna da halin dayake ciki,sauri tayi cike da tausayi takai hannunta izuwa kafarsa domin cire masa karfen dake jiki,kana tace"kai kanason zuwa wajen ruwa ko?"uhummmmm"shine abinda yace bayan tamasa magana,jin abinda yace yasa ta tambayeshi"lahhh dama ka iya magmana?"kallonta yayi yasake cewa "uhummm"murmushinta ne yakara fitowa ganin ba abinda ya iya cewa banda uhumm din,bayan tagama cire masane sai kuma taga yakasa tafiya da kafar,lahhhh bazaka iya tafiyaba?to ni bansan gidankaba bare na kaika kuma idan na barka anan masu tarkon zasu kamaka,bata gama rufe bakiba ta ga ya hura wata iska mai kalar jikinsa da bada wani layi mai haske ya shiga cikin dajin,ganin hakan ne yasa tagane so yake ta kaishi wajensa,murmushin tasake kafin ta daukeshi duk da yamata dan nauyi a hannunta ,ba kaman da ba da kadan yafi kuliya/mage girma.Tafiya tafara yi akan layin daya hada doimn ta kaishi masaukinsa ,sun danyi tafiya kafin ta fara tambayarsa amma ganin bashida amsa sai uhummm yasa itama tayi shiru tana shafa gashinsa mai matukar laushi da kyau,bata ankraba kawai ta ganta a gaban wani dan gida mai kama da bukka a tsakiyar dajin,baki tasake a bude tana kallon wajen matukar shagala da kyan wajen,zillewar da abin yayi a hannunta yasata dawawo daga tunanin data tafi kana takalleshi saidai abin mamaki shine abin tafiya yake tamkar ba abinda yasame shi,dagowa yayi yana mata gwalo bayan ya dire a kasa,alamar dama yana iya tafiya kawai dan ta rakoshine yasa yanuna baya tafiya,abin kara bata dariya yayi saidai kuma dataga rakoshin datayi sai itama ta cimbine fuska,suna cikin hakanne wani mutum yafito daga gidan ya nufo izuwa wajen su,gabadya ilahirin jikin ta tsayawa yayi da aiki na wani lokaci sanadiyyar arba datayi da mutumin daya fito daga dakin,saida ya fito ya buga hannunsa akusa da fuskartane yasata dawowa cikin hankalinta,"uhmm menene ya razanaki haka bayan kecec kika zo da kanki?uhmmm"maganar yamata cikin natsuwa dakuma murmushi"uhmmm ni dadddd....dama nnnna...rakoooo wannan abinne gidansu"duk maganar datakeyi tanayine cikin tsoro dakuma in iyina,dariya taji a gefenta irin yara masu mugunta wanda tana juyawa taga abinda tarakone yake mata dariya,juyawa tayi tna kallonsa irinna zaka sani ne,murmushi mutumin yayi ganin dramar dasuke yi da abinnnasa,kome ta tuna kuma sai kuma ta juyo zuwa wajen mutumin ta nutsu kaman ba ita ta ke kallon abunba yanzu,shima kalonta yake kafin yajuya zuwa cikin dan gidan nasa tare da bada mata ta shigo,har yakai ga bakin kofa amma bata biyoshiba kaman yanda yfadaba,hummmm ajiyarzuciya yayi kafin yace"kina tunanin zan cinyeki ne ,ai yakamata ki shigo gidan abokinnaki ko dannaga da alama tunda yasaka kika rakoshi so yake kiga gidansu,"duk maganr yana yinta ne kallonta hade da murmushi a fuskarsa,saida tatsaya tai jumm kafin ta fara taka kafarta izuwa ga bakin shiga kofar gidan,koda shigarta sai hankalinta ya kai ga duk wani abu dayake dauke ackin dakin domin bakaramin tafiya yayi da hankalinta ba ,ji datayi ana shafa ta takasa shiya dawo da hankalinta daga inda yatafi,zuyawa tayi ta kalli abokinnata,hankalintane yakai kansa gabadaya kafin tace" yasunanka"? "bazai amsa miki ba saboda baya magana bansaniba ko zaiyi nan gaba ,sunanshi FONEEYAN"sunanne yamata dadi sai ta yanke sunanan ta hanyar cewa FONEE sunanaka da dadi zaka bini gidanmu iyee?,ganin hankalin ta yatafi ga fonee dinne yas yatashi ya shiga izuwa wani daki dake gefe da inda take zaune,bai dade da shigaba ya fito da kofi a hannunsa ya mika maata ,da farko kamaan bazata amsa ba saikuma tasaka hannu ta karba amma batare da ta kai bakinta ba magana yafara mata ganin yanzun tayi shiru bakaman dazu ba data fara magana,"uhm bakuwar fonee baki fadamin sunanaki ba"?"uhm ni...suanana fariyatul sharmeelah amma anfi kirana da fareeyah,"suananki mai dadi sosai"ganin bazata tambayii nasa sunan bane yasashi cemata"tohh nikuma sunana saheel,"kallonsa take tare da tunani azuciyarta wanda batasan ma sanda tambayar data masa ta fito fili ba"amma yaaya saheel meyasa kake rayuwa anan kai kadai ban taba ganin mai irinnnn wannan giadn ba a garin bardugu,sannan kuma shima fonee bantaba ganinsa mai irinsa ?kenan ba agirinnan kake ba?"kalllonta yayi kafin yacec"uhm lallai kin iya tambaya ,to ni ba dan wanna yankin bane amma anan muke rayuwa da fonee sannan yanda kika ganshi nima haka na tsince a jeji kafin nazo nana bansan wane kala bane ,ammma tunda kuna da irin wannan dabbobin watakil zakiga masu shigensu ko?"har fariya ta bude baki zatayi magn saikuma tatuna da mai ya kawo ta cikin dajin dazu,wanin zaburar tashi tayi kana jiknta ya hau barii cikin tsoro da firgita,"menene?"shine abinda yafada amama kafin tabashi amsa har ta fice daga gidan da sauri ta nufi hanya da nufin komawa daga inda tafito,magana ta jiyo a babyanta ana cewa ba nan bane hanyar,juywawa tayi ta kalli saheel ne da fonee a hannunsa yana taho inda take,saida yazo kusa da ita kana yace"kin dadene za'amiki fada a gida kina tsoro"ehhhhhhh"shine amsar data bashi da sauri,ganin yanayin amsar ta ma ya kara tabbatar masa da cewa dadewar datayi ya tsoratar da ita sosai,"manene yasa kika zo jejin da har kike nuna alamar tsoro a tare dake?" ehh dama nazo diban itace ne kuma gashi na dade ban komaba gidaba"yanayin data shigane ya kara nuna masa cewa akwai wani abu boyayye a rayuwarta wanda zaiso yaji menene,saidai yanzu ba lokacin tambaya bane.Fadamata yayi akan ta jirashi yana zuwa kafin ya juya zuwa hanyr da suka fito da hanzari,baidade da tafiyaba sai gashi yadawo dauke da itacen a hannunsa a daure,kana yace mata ta nuna masa hanya suje ya rakata,tafiya suke amma ba wanda yace komai acikinsu ita tana tunanin mai zata fuskanta a wajen aryana yayinda shikuma ke tunanin menene lababrinta,dahahka har suka iso bakin layin dazai sadata da gidansu,inda taja ta tsaya tare da shaida masa sun iso kusa da gidansu,karba icen tayi ta nufi gida bayan tace masa ta gode ,inda shikuma batare da yace mata komaiba kawai ya bita da kallo har ta kule ma ganinsa.
A cikin gida kuwa ba irin tozarcin da huda bata ganiba awajen aryanan sanadiyyar rashin dawowar fahriya daga inda ta aiketa da wuri.Fahriyance tashigo gidan cikin sanda dauke da icen da saheel ya bada tana muzurai,abinda ta ayyana a ranta shine yafaru domin kuwa aryanan rufeta tayi da duka matsananci,tana dukantane tanan fadin"har nice zan aikeki ki yimin abinda ranki yakeso,ko kin manta matsayinki ne, to uwarki ta fadamiki ke bakomaibace face baiwa wadda bata da ikon kanta kuma tunda kin ga ke kina da taurinkai to kijira nan da wani wata mai zuwa zan sayar dake ga fataken dasuke zuwa duk bayan shekara ,inkuma kinga akwai wanda zai sanja min abinda nayi niyyah to ki kawoshi.Duk da dukan yataba uwar da yar amma kalmominta na karshe sun fi komai tayar musu da hankali a cikin zancennata domin ba karamin girgizasu yayiba,cikin halin ko inkula da abinda ta fada ta juya izuwa dakinta tan cigaba da fadar duk abinda yazo bakinta.Bayan gama wannnan cakwakiyarne huda taja yar ta daki domin bata irin abinda ta boye don irin wannan ranar wato guntun abinci,domin tasan koda wa take takama yau daga ita har yar ta bazasu samu guntun kanzon da take basuba na kasan tukunya idan angama abinci,koda isarsu dakin sai huda ta zaunar da fahriya akan guntun buzun dayanke dakin wanda ko kare aka sakamasa dakyar ya kwanta akai,ba abinda fahriya take sai aikin kuka da jan zuciya,shiru uwar tayi tana kallon yar domin bata dama tagama cire abinda ke cikin ta kafin suyi magana,saida ta dau lokaci tayi shiru kana huda ta fara gyaran murya tare cewar"duk kwanakin baya dana ce miki cewa nina jawomiki wannan rayuwar kin amincewa da magan ta kikayi fahriya amma ko kinaso koba ki so nasan nice na zawo miki wannan rayuwar dakika tsinci kanki aciki,wanda gashi har tana nema tafi tawa rayuwar tsanani,kaicona dasan zuciya daban tuno yanayin da zan saka rayuwarki ba,saidai duk da haka bazan gaji dacewaa kizama mai jajircewa a rayuwarki,sannan ki tsare mutuncinki dakuma yarda da duk wata ,kaddara data zo miki a rayuwa wannan shine iya abinda zan miki,kuka take amma hakan bai hanata maida martanin maganar da mahaifiyarta ta kemata ba "ahaha ummi kidaina fadin haka da sannu komai zaizo da sauki kuma zan kasance mai tuna maganarki a koda yaushe,namiki alkawarin hakan.Dahaka suka cigaba da tattaunawa har zuwa lokacin da suka kwanta.
Duk da kuncin da bayin allan ke ciki hanasu fawwalawa allah dukkan rayuwarsu ba,a bangaren fahriyah kuwa yazamana yanzu kullum itake debo ruwa sannan kuma da itace,duk da hakan na bata wahahla amma hakan baisata damuwaba sanadiyyar haduwa da foneee da take a jejin dakuma wani sa'in saheel wanda take ganin a matsayin shima wani wani mai muhim, kullum yauma a zaune take a bakin rafin domin ta debi ruwa,yayinda kuma saheel na gefenta shida fonee suna ta nishadi,saboda yawan haduwa dasuke har yakai ga sun san lokacin da ta ke zuwa diabn ruwa da kuma itacen kuma da lokacin da idan takai a tare da su zata iya fuskantar kalubalen aryana,basu jima a zaune ba fahriyah ta fara yunkurin tashidomin lokacin tafiyar ta yayi,saidai kafin ta kai ga tashi saheel yamamta magana ta hanyar cewa ta koma ta zauna yanason yin magana da ita,fuskanta ne yai kicinkicin alamar idan ta dade zata karbi hukuncin a gida,lurada hakan da yayine yasa yace mata,"kin yarda dani ?"shiru tayi da jin tambayarsa kafin tace"ehhh" "to shikenana idan kin yarda dani,to kicire damuwar dadewar dazakiyi anan wajen acikin ranki,sannan idan kin yarda dani inason ki,bani dukkanan tarihin rayuwarki,dakuma yanayin hakin kuncin dananga kina fuskanta a kananan shekaru,"a ynanayin da yake mata maganan da alamar rashin wasa kamar kullum ya tabbatar mata dacewa da gaske yake yi ba alamar wasa a lamamrinsa,hakanne yasa ta bude baki,tafara bashi lababrinta tundaga farkon abinda tasani har karshe,saidaid kuma ta tsinci kanta da kasa bashi lababrin haduwa abinda yafru a gida bayan haduwarsu ta farko,daga bayane da ta tuno yanda ta amince tacewa ta yarda dashi da farko,yasata kawai bashi labarin kmai batare da boye ko kadan ba....................."inada mafita idan zaki amince"abinda yafito daga bakin saheel bayn jin labarinta.

written by ❤️❤️SADI-SAKHNA❤️❤️(the legendary novelist)🌄🌄🖌️🖌️

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now