Chapter (08)meyake faruwa ?

63 7 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

(08)

Gyara zamanta tayi saboda kar razanar da tayi ya fito fili ,saboda kar bayinta su rainata ,tunani tafara yi ranta cewa "tabbb gaskiya kyawun halitta ya bayyana a jikin baiwar allah nan ,don duk da izzar mulkina da kuma launin fata irin namu na kasar saraham ,tabbas bazan nuna wa wannan fatar kyau ba ,sannan .............tunanin da takeyi ta katse sakamakon muryar gimbiya safeenah da taji a cikin kunnenta ,
"barka da safiya sarauniya zulaikah dafatan nasameki lafiya ?"
yatsine fuska tayi kafin tace "zancen lafiyata ,kalau nake nida magajin masarautar nan dayake cikin cikina ,zuwanki bazai sa nakamu da cuta ba ,sannan ina miki barka da zuwa wannan masarauta wadda take karkashin ikon wata ,saidai mutum ya biyo a baya"
sarauniya zulaikah ce ta karisa maganar ta ,fuskarta dauke da wani mugun murmushi mai dauke da ma'anoni daban daban ,hannunta kuma akan cikinta tana shafawa cike da gadara ,sarauniya safeenah ce ta sunkuyar da kanta kafin tace,
"shikenan nizan wuce nabarki lafiya"
tana gama fada ta tashi kana tayi hanyar fita daga falon ,muryar zulaikah taji a bayanta tana cewa ,
"dama kuma inaso namiki dan tuni akan wani abu ,karki manta da kofar da kika shigo "
zuyowa tayi ,ta kalli zulaikah fuskarta dauke da alamar kanta ya daure da maganar ,ganin halin da ta shiga ne yasa zulaikah yin murmushi kafin ta juya zuwa babban falonta cikin takama.
Sarauniya safeenah ce zaune a gaban wani katon madubi dauke da kayan ado iri iri ,hankalinta ba akan abinda yake gabanta bane ,tunanin maganar da sarauniya zulaikah ta fada mata take ,sai can kuma ta watsar da komai ,ta tashi tana gyara alkyabbarta domin shiga turakar sarki ,jakadiya ce ta rakata inda aka sake shiryata domin jiran isowarsa.
Koda jakadiya ta ji alamun fitowarsa sai tabasu waje domin ganawa,zaune take fuskarta a sunkuye har yazauna a gabanta ,
"to ina miki barka da zuwa sabon waje sannan kuma sabuwar rayuwa "
"ina amsawa ya shugabana"
"hmm shikenan dafatan babu wata matsala da kike fuskanta ?"
"babu komai saidai rashin sabo"
"karki damu sannu zaki saba da hakan ,fatanmu shine allah yasa albarka a zamanmu "
"ameen ya allah ".
Daga haka labarinsu dakuma hirar su ta sanja salo ,nabasu waje domin su gana.
Haka rayuwar cikin masarautar ta cigaba da tafiya a tsakanin matan ,yazamana yanzu sarauniya safeenah tasaba da sabuwar rayuwarta ,wanda sanadin halinta na kwarai yasa da kadan kadan mutanen gidan da kuma bayi suka fara komawa karkashinta.
rayuwa suke ta kowa yayi harkarsa ,domin babu wanda yake shiga harkar wani ,saidai a bangaren zulaikah burinta da kuma tsarin da ta shirya yana nan a cikin ranta .
Abubuwa da dama sun faru a masarautar saraham ciki harda haihuwar sarauniya zulaikah da kuma barin ciki da da sarauniya safeenah tayi ,saidai abu yazo ba yanda aka zata ba .
Bayan doguwar nakudar da zulaikah tayi a dakin karbar haihuwa ne ta haifo yar ta mace ,sak kamarsu daya da ita ,lokacin da zulaikah ta kula da abinda ta haifa sai duk duniyar ta sanja mata ,amma soyayyar d'a da uwa ,hakan bai hana ta daukar yar ta ta rungume ba ,amma abinda yake cikin ranta yafi gaban kwatance.
Bayan kwana bakwai ne yarinya taci suna MEELAH ,inda sunan ya tara manyan mutane dakuma gagarimin taro ,sarauniya safeenah ma ta yimata murna ,saidai bata ga fuskar amsawa daga wajen uwar gayyar ba.
Lokacin da sarauniya zulaikah ta fahimci cikin dake jikin safeenah bakaramin girgiza tayi ba ,saboda a tunaninta zata haifi da namiji kafin ita,hada baki sukayi da wata baiwarta inda sukayi nasarar saka mata maganin bari a cikin abinci.
Haka abin yacigaba da faruwa inda har saida takai safeenah tayi bari uku a jere cikin shekara guda ,abinne yabata mamaki inda har saida takai ga tace ,"shin meyake faruwa dani "
Bayan abinda yafaru sai shigar cikin ya tsaya mata ,har ta shafe shekara biyar batare da tasamu cikiba .
Zulaikha ce a zaune akan kujera gefe kuma babbar baiwarta ce RALEEYAH kuma amintacciyar ta ,wanda duk wani shiri da ita ake kullawa ,sarauniya zulaikah ce tafara magana ta hanyar cewa ,
"gaskiya inaga abinda nake hasashe ya tabbata ,dan kiduba ki gani tsawon shekara biyar kenan har yanzu bata samu cikiba ,kuma dama maganin idan ya zubar da ciki fiye da sau uku ,to da wuya mace takara samun ciki "
"hakane ya shugaba ta ,hakika aikin mu ya yaci yanda muke bukata ,kuma dama nasara tana tare dage sarauniyar sarauniyoyi "
kantane yakara fasuwa dan dama hakan yana mata dadi yanda baiwar tata take zuga ta.
Har sun bude baki zasu cigaba da magana sai ga meelah ta shigo tana wani tamke fuska ,yarinya ce yar shekara biyar amma kuma kasaitar ta da jin kanta yafi na yar shekara goma ,dan a wajen gado mahaifiyarta har ta wuceta ,wannan hali na meelah yana yiwa zulaikah dadi ,dan tafiso taga jininta suna taka kowa yanda suke so ,zama tayi a gefen uwar tata ,inda raleeyah ta fara gaisheta tare da kirari ,ko kallon inda take meelah batayi ba bare ta amsa gaisuwar ta ,babu cin fuska dakuma zarafi da bayin basu fuskanta ba a wajen meelah ,wai hakan ma batakai ga girmanta ba.
Kallon uwar tayi kafin tace ,
"ummah zanje na kwanta idan mai karatu yazo ace masa yajirani har sai na tashi ,kar a tasheni dan hakan yana samin ciwon kai "
"shikenan shalele ki fito lfy "
zuyawa tayi tana wani taku kamar isassun mata ,wanda suka san takan rayuwa har ta bacewa ganin uwar tata ,saida tabar gun tukunna zulaikah ta juya tana kallon raleeyah gami da cewa ,
"kinji dai mai gimbiya meelah tace ,dan haka karki bar kowa ta shiga sashenta har sai ta bukaci hakan "
"angama mai girma sarauniyar saraham "
Acan bangaren sarauniya safeenah kuwa ,zaune take suna magana itada sameerah tana bare mata ayaba suna yar hira ,can bayan wani lokacine safeenah ta ajiye ayabar da sauri tare da barin wajen da sauri tana ...........

alkalami ya gaji sosai 😊 ku tara dani a gaba.

SADI-SAKHNAce

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now