Chapter (09)Dole sai ya mutu😠

56 10 1
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(09)

Tana kokarin amar da yabar data shiga bakinta ,sameerah ce ta mika mata ruwa tare da yimata sannu ,saidai kuma abin yazarce saninsu ,domin kuwa bayan amar da ayabar sai yazamana tafara amayar da duk ruwan dake cikinta ,saida aman yalafa matane ,sameerah ta rikota suka dawo daki tana mata sannu ,ganin irin galabaitar datayi lokaci daya ,numfashi take sauke wa a hankali tareda amsa sannun da baiwar tata take mata ,kwanciya tayi domin tasamu ta dan huta kafin zuwa anjima .

Gimbiya meelah ce ta tashi daga barci ,lokacin maraice ,tana wani yacine fuska kamar ta hadiyi ashana ,takawa take cikin karairaya tana wani shan kamshi ,tafa hannunta tayi a bakin kofar ,wanda hakan yabawa bayin dasuke bakin kofar shigowa cikin sauri ,rabuwa sukayi kowacce tafa aikinta ,gyaran inda ta tashi dakuma gyaran bandaki da yimata wanka .
Bayan sun gama shiryata ne ta tafi zuwa turakar mahaifiyar tata ,wanda tana ganin yar tata ,ta bude mata hannu alamar ta taho ,
"laleh da gimbiyar daular saraham kuma farin cikin sarauniyar daular saraham ........."
haka tagama yimata kirari itakuma tana wani daga kai ,(nidai nace tohhh ).
Bayan sati guda ,amma har sannan jikin sarauniya safeenah babu dadi ,domin duk abinda taci sai ta amar shi ,ga zazzabi sosai ,sameerah ce takare mata kallo kafin tace ,
"ranki yadade inaga cikine dake domin alamun hakan sunnuna "
"ehh nima ina tunanin hakan ,inaga kije kikiramin ma'ikaciyar jinya ta dubani "
"ahah ranki yadade ,nifah banyadda da mutanannan ba ,dan wannan zubar da cikin da kikayi a baya ,AKWAI LAUJE CIKIN NADI akai ,inaga murufe zancen cikinnan har sai yayi kwari ya isa haihuwa "
"shikenan sameerah ,amma ni aganina bai kamata mu zargi wani ba ,akan hakan ,domin komai allah ne yake kaddarawa ,allah yazabamana mafi alkhairi "
Haka kuwa akayi babu wanda yasan da zancen cikin safeenah har saida yakai wata biyar kafin ta sanar da mai martaba shima dan ya kula da hakanne ,yayi farinciki sosai daya samu labarin hakan ,sai kuma abin yabashi mamaki akan mai yasa bata sanar dashi ba ,dabara tayimasa irin namu na mata akan cewa ,tana son yimasa bazata ne ,shida sarauniya zulaikah ,amma tunda shiyasani to yabari iya kar yafadawa kowa sai sanda ta haihu ,bai kawo komai a ransa ba ya amince da kudurin ta .
  Bayan cikin sarauniya safeenah yayi wata bakwai ne ta tambayi mai martaba akan zataje garinsu ,dafarko yanuna kin amincewarsa ,saboda cikin dake jikinta ,saidai dayaga hankalinta ya tashi sai ya amince ,tayi farinciki sosai daya barta ,inda sukafara shiri itada sameerah ,basu dau lokaciba washagari suka kama hanyar maihaifar tata cikin farin ciki .
Saida sarauniya safeenah tashafe wata biyu kafin ta dawo saboda lokacin haihuwarta ya kusa kuma yazo mata da jinya mai matukar wahala ,inda mutanen fada suka fara samun labari cewar sarauniya safeenah bata da lafiya amma ,anhana kowa damar dubata daga gidan sarautar.
Hakan yajawo gulmace gulmace kowa da abinda yake fada ,(uhmm gidan sarauta )
A bangaren sarauniya zulaikah kuwa zaune take a turakar mijinnata suna hira ,kallonta yayi kafin yace ,
"zulaikah yakamata kije ki duba abokiyar zamanki domin tun sanda ta  dawo daga garinsu bata lafiya ,sannan naji labari bakije kin duba dakinta ba tun sanda tazo gidannan "
"au gulmata aka kawo maka ko ?to ni zulaikah bata isa tasani abinda banyi niyya ba "
tana gama fada ta tashi fuuuu tabar turakar ,binta yayi da kallo kafin ya jijjiga kai .
Yau ta kama jumaa lokacin hantsi ,sarauta safeenah ta tashi da nakuda mai matukar wuya ,inda aka kira ungojama daga fada ,ita kanta tayi mamaki da taga uwar gijiyatata da ciki saidai bata nuna ba ,tafara bata taimako ,
sun sha wuya sosai kafin allah yabata iko ta haifo danta namiji ,saidai daya tashi fitowa tare yafito da mahaifarta ,wanda dama tasamu matsala sanadiyyar barin da tayi a baya ,gyara jaririn akayi wanda yafito sak jikin ubansa saidai kama dayayi da mahaifiyarsa ,itama taimako suka bata kafin kuma aka gyara mata jiki domin ta huta .
Labarin haihuwar sarauniya safeenah ne yafara zaga cikin masarautar inda kowa abin yabashi mamaki ,domin kowa bashida masaniyar samun cikinta bare kuma ace ta haihu .
A bangaren sarauniya zulaikah kuwa zaune take itada babbar baiwarta suna hira ,sai ganin baiwa sukayi ta zube a gabansu tana haki ,
"ranki yadade kiyimin rai ,amma hakika naji wani labari yana yawo a cikin masarautar  nan "
"to menene ya faru ki fada mana "
cewar raleeyah ,
"uhmm dama labarine ya riski wannan fadar na haihuwar da sarauniya safeenah tayi a yau "
"ehhhhh me kikace haihuwa kuma tabbb "
sarauniya zulaikah batace komai ba ,sai yanzu tace ,
"me ta haifa ?"
"uhmm da namiji "
"iyeee ,namiji 😠😠,saboda bakin sakonki kije ki karbi bulala shabiyar a wajen sarkin horo ,(nace maganin munafiki )"
fita tayi jikinta yana rawa tayi waje ,raleeyah ce ta kalli sarauniya zulaikah kafin tace ,
"to yanzu menene abinyi akai ?"
"hmmm ,inaaa ai dole sai ya mutu ,hakan bazai taba yiyuwa ba ,wani ya kwace daular saraham daga wajena .
A can kuwa sashen sarauniya safeenah hankalinsu kwance ita da jaririn ta wanda yake cikin koshin lafiya ,labarin haihuwarsa ya zaga duk fadin duniya bama iya daular saraham ba .
Meelah ce ta shigo sashen sarauniya saraham din bayi suna take mata baya fuskarta kaman anyimata aiken mutuwa ,koda tazo bakin turakar aka bata izinin shiga saita dakatar da bayin da bakin kofa kafin ta shiga ,bata yiwa kowa magana ba acikin dakin ta wuce wajen jaririn wanda yake kwance cikin gado na alfarma dakuma kayan sarauta ,kallonsa tayi kafin ta tabe baki tace ,
"an tursasani nazo na ganka ,amma ba hakanne yasa ni zuwa ba ,domin babu wani mahaluki daya isa yamin dole ,nazone nayimaka gargadi akan ka tsaya iya matsayinka karka shiga gonata ,don kana ganinka na miji ,dan haka indan ka girma ka tambayi mahaifiyarka yanda ake zaman gidannan a zauna lfy ,kai ba kowa bane ,face dan bayan fili ,dan haka ka rubuta ka ajiye "
tana gama fada ta karewa dakin kallo kafin tayi wani zuyi ta fice .

tohhh nidai nace rayuwa .

    SADI-SAKHNA ce

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now