Chp(31)kawai kuma??!!

51 9 11
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

Chp(31)
Shirye shiryen biki aka fara ba kama hannun yaro a masarautar sardaham din duk da sarauniya safeenah ba wani murnar bikin takeba amma hakan bai hanata bada gudummawarta dari bisa dariba.
Yaune yakama ranar daurin aure,tun safe yarima amam yake rike da kirjinsa saboda azabar ciwo dayake masa,yarima saheel ne ya kalleshi kafin yace,
"Amam lafiyar ka Kalau kuwa?tun dare naji kaman kana kiran wata a mafarki wai fahreeyah yau kuma na ganka rike da kirji kana cije baki,yakama ta ka fadamin idan wani abune".
Ta shi yayi cikin dauriya kafin yayi murmushi yace "babu komai saheel karka damu,bawani mai yawa bane kirjina ne kawai yake dan ciwo"
"Kawai kuma?amma duk wanda yaganka a wannan halin yasan kana jin jiki sosai,toh shikenan allah yayi mana da sauki"
Da haka suka gama shiryawa cikin kayan sarauta sannan suka nufi wajen daza'a daura auren a wani gari wanda yake gefen sardaham din.
An gama hidima ta biki har ankawo amrya daga garinsu an kaita sashen mijinta.
Saheel ne yakalli amam dayake kwance bashida niyyar tafiya wajen amaryar tasa yace,
"Abokina yakamata kadaina wannan halin haka tunda ka amsa yakamata kuma ka danne zuciyarka,duk da nasan bakason nasreemah amma ina mai tabbatar maka duk yanda ka daura ta haka zata bi,dan ita macece da batada ra'ayinta said wanda wani yafada mata,indai ba wani ne ya zigata ba bazaka samu matsala da itaba inshaallah"
Tashi amam yayi daga kwancen cikin sanyin jiki wanda sai a sannan ya tuna ashe kanwar abokinnasa yake aure,kallon saheel din yayi tareda tunawa yanda yake zaune dashi a cikin wuya da dadi tun lokacin da suka hadu bayan ya bar masarautar tasu,
"Kayo hakuri saheel abubuwane sun fara fin karfina"
"Ahah karkace haka,sannan karka yi tunanin wai dan tana kanwata na fada maka haka,navfadane saboda kana matsayin abokina,ko wacce mace ka aura ni mai baka shawarane amam,fatana allah yabaku zaman lafiya sannan kaikuma allah yabaka ikon jurewa"
Jijjiga kai yarima amam din yayi tareda yiwa abokinnasa Godiya kan kuma yanufi hanyar dazata kaishi sashen matartasa.
Da sallama yafara shiga da kinnata inda yasameta a tsakiyar gadon an lullubeta da adoo,tunanin cen da take ransa ne ya fado masa inda yayi saurin kawar dashi kana ya karisa gaban gadon ya zauna.
Lullubin dayake kanta ya yaye idonsu yana kallon na zuna,murmushi tasakar masa mai laushi kafin ta amsa sallamar daya sake yimata a karo na farko,hannu ya mika mata inda itama ta miko nata tasaka a cikin nasa.
Kokarin yaki yakeyi da tunanin dayake cikin ransa da kuma kirjinsa dayake bugawa akai akai,sai kuma a wani bangaren yana tuna hakkin ita wannan matar daya hau Kansas,sannan idan bayyi yaki da zuciyarsa ba toh said yaushene zayyi?,da haka yabawa jikinsa damar luluwa duniyar soyyaya da amaryar tasa wanda itama dama a wajen ta wannan ranar take jira domin cikar burinta.
Saida amarya tayi sati kafin ta fara fitowa daga sashenta inda tazaga surukannata wato su sarauniya safeenah da gaisuwar ta amatsayinta na surukarsu.
Bata dade a bangaren Sarauniya safeenah ba tafito tayi hanyar sashen sarauniya zulaikha saboda dama matar mijinnata ba wani surutune da ita ba,tunda ta yimata fatan alkhairi da kuma barka da zuwa wani abu bai sake hadasu ba.
A bangaren sarauniya zulaikha kuwa zaune suke itada yarta gimbiya neelah wanda tun zuwan da tayi auren kaninnata bata komaba sai gobe,neelah ceh ta kalli mahaifiyar tata kafin tacevcikin takaici,
"Yanzu shikenan duk abinda muka hada ya tafi a banza kenan ummah?"
"Bai tafi a banzaba,saboda indai ina raye toh bazan taba bari yaga dansaba"
"Toh ummah hana matarsa haihiwa zakiyi kaman na ummansa?"
"Ahah Har yanzu kefah bakya kawowa haske sosai,idan na juyar matarsa kuma mai akayi kenan,wata matar zai auro ai kawai ta haihu,shi zan juyar sannan nayita zuga matar tasa harma da mutanen cikin fadar,zanga yanda za'ayi sarki juya,sannan kuma.............."
Katsewa tayi da maganar ta jin wata baiwa tana yiwa gimbiya nasreemah iso zuwa cikin falon,komawa tayi ta fada mata,kafin ta shigo ta zauna akasan daddumar dakin.
Gaishesu tayi suka amsa cikin farinciki kaman duk duniya babu wanda yakaisu santa,
"Toh surukarmu wannan itace yayar mijinki gimbiya neelah,nikuma ki daukeni tamkar mahaifiyar ki kinji,saboda ita kanwar tawa kunyar amam din takeji ba lallai ne wata magana ta dunga hadaku ba,dan haka duk wani abu kowata matsala to kizo fadamin kinji koh"
Murmushi tayi cike da jin dadin yanda gimbiya zulaikha ta tarbeta,
"Inshaallah zan kasance mai hakan ummah,nagode sosai da kulawarki"
Tashi tayi tareda yimusu sallama,har takai bakin kofah zulaikha ta daga muryar ta tareda yimata magana,
"Am Y'a ta naceba,kinga wannan maganin,........ta fada tana nuna mata kullin magani guda biyu...
Wannan mai dakon ki dunga kunjugu dashi kafin yakusanceki,wannan kuma kidinga saka masa a abinci,amma fah karki bari yagani kinji domin sirrinmune na mata kinji?"
Takarisa fada mata fuskar ta dauke da murmushi,karba tayi cikin kunya tana murmushi itama tareda yin godiya ta tafi.
Zulaikha ce ta juya ta kalli yar tata kafin ta sheke da dariya,
"Amma ummah bazai mata komaiba ita din"
"Babu abinda zai mata amma shikam idan ya kuskura ya kusanceta sannan yasha wannan garin toh shi da haihuwa saidai yaji anayi badai shiba kam".
Gimbiya nasreemah kuwa tana komawa sashenta ta ajiye maganin cike da murna,bude garin tayi ta juye a ruwan lemon da ta hadawa amam din wanda taga yana sonsa sosai,kafin tayi sauri tashiga wanka aka gama shiryawa ana jiran mai gida yadawo a mallakeshi........Allah sarki bawan Allah.
Bayan wata shida da auren yarima amam,sai farin cikin sarauniya zulaikha yafara fitowa saboda tagama ganewa yanzu cewar kwayoyin hallitar yarima amam Na haihuwa sun gama mutuwa,saboda maganonin da take ta aika gimbiya nasreemah tana saka masa batare da ita tasani ba ,dan a ganinta taimakonta take bare kuma shi da baisan me ake cikiba.
Ana cikin hakan sai yarima amam ya kwanta jinya na ciwon mara tamkar bazayyi rai,manyan masu magunguna aka kira domin su duba lafiyarsa,ananne suka gano cewar kwaoyin haihuwarsa sun mutu,kuma babu alamar zasu sake tashi bare kuma har a samu haihuwa nan gaba,take kuwa labari yagama gari kaman jira ake,duk da cewar babu wanda ya sanar da wani amma labari saida ya yadu ko ina,inda wasu suke cewa ma dama haka aka haifeshi a juya,bashida kwayoyin hallitta.
Haka labari yacigaba da wanzuwa a nahiyar sardaham cikin ynayi marar dadi....
A bangaren nasreemah kuwa sugar da ake mata yafara tasiri a kanta inda har tafara gorantawa yarima amam cewar,dama yasan baya haihuwa ya aureta toh me amfaninsa.

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now