Chapter(17)An gudu ba'a tsira ba

50 10 0
                                    

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

chp(17)

Saheel ne a zaune a bakin gidansu gefensa kuma fonee ne a zaune shima.Dukkansu damuwace kwance akan  fuskarsu ,da alama sun rasa wani abu mai muhimmanci a garesu ,saheel ne yayi ajiyar zuciya kafin yace .
"ina kika shiga faryah ? ina kika shiga sarauniya ta ?,hakika kin kasance wani bangare na jikina a halin yanzu ,rayuwa babu ke zaimin wuya a rayuwata ,kaman yanda na fada a baya ke tawace ,kuma da sannu zamu hadu duk daran dadewa sannan ............"
bai gama surutun dayake ba yaji motsin mutane a bayansa ,yana juyawa yayi arba da dogarai a bayansa ,dauke kansa yayi daga kallonsu kafin yace cikin muryar fushi ,"meyake tafe daku ? waya aikoku wajena iyeee ?😠"
sukuyawa sukayi alamar ladabi a gareshi kafin sukace ,"takawarka lafiya sarki dan sarakai ka gaji sarauta gaba da baya da girman daukakar ka yariman da babu kamar sa ..................tohh yadai ?? 😊😊,me kukace reader ,show me your perceive😊😊.
                  。。。。。。。。。。
Farfadowar fahreeyah ne daga doguwar suman da tayi ta tsinci kanta a cikin wani keji na itace tare da wasu sauran yan mata guda biyu da kuma wasu samari suma guda uku ,kallonsu take tana rarraba ido yayinda suma ita suke kallo alamar wuya a tattare dasu .
Babu abinda yake tashi acikin kejin sai numfashin su dayake tashi mai cike da wuya acikinsa ,bayan anyi tafiya mai nisane sukaji antsaya,wani mutumine yabude su tareda mika musu wani ruwa acikin gora mai masifar datti ,wawar karbar ruwan akeyi har ana ture wasu gefe ,kallonsu ta tsaya tanayi wanda tashinta kenan daga suman datayi bata gama gane mai yake faruwa ba ,saidai lokacin da taga ana kokuwar ruwane tagane cewar ashe fah itama kishirwa taci jikinta sosai ,saida suka gama kokuwar kafin suka dan diga mata a makogaranta itama ta shaida dan ruwan.
Bayan sun gama hutawane kuma aka sake cigaba da tafiyar da bawanda a cikinsu yasan lokacib tsaywarsu.
Darene yafara kama waje yayinda hasken rana yafara hada nasa yanasa domin ya tattare yabawa dare shima yaci tasa kasuwar ,a dadai lokacinne kuma zazzabi yayi dirar mikiya a gaba daya ilahirin jikin fahreeyah ,wani irin jijjiga takeyi sakamakon karfin zazzabin daya fi karfin tunaninta ,wata yarinyace bazata wuce sa'arta ba ta matso kusa da ita tareda tambayarta ,
"baiwar allah mai yake damunki haka ?"
"b....bansaniba n...nnn...nima ,amma jiki..........jikina zai...kkk...kama ....da wuta "
"ahah mai yayi zafi haka ? ko zazzabi ne yake damunki ?
"ehhh "
tafada hawaye yana zubowa daga cikin idonta ,saboda azabar ta ke ji a cikin ta ,matar ce ta dauki ta dauki wani dan tsummanta ta kara yafawa fahreeyah akanta saboda ganin karkarwar datake yi ,
"nagodee baiwar allah da taimakonki saidai bansan sunanki ba ?"
"ahh sunana LEEMAH ni y'ar cikin garin barduguce ,nice wacce kikaga suna dukana har suka kamaki "
"ayyah to me suke nufi damu dazasu kamamu ?"
"nima bansaniba ,amma daga gani ba nufine mai kyau ba saidai muyi ta addu'a "
"shikenan na gode da kulawarki "
"nima nagodee ki kula da kanki allah ya sawwake "
"ameen "
Haka suka ci gaba da tafiyahar sujayi kwana biyu a hanya ,wani gari daban suka fara hangowa tun daga nesa mai girman gaske,gofar garin aka bude musu domin basu damar wucewa ,kalle kalle suka farayi ganin abubuwa iri iri acikin garin har akazo wani waje mai tarin mutane ,korosu aka farayi daga cikin kejin ana jerasu kaman kaji ,saida aka gama jerasune wasu mutane sukazo suna kallonsu da alama zana zasuyi daga ciki ,wani babban cikinsune ya fara magana da cewar ,
"umarnine daga masarauta kaman yanda yake ,zaku bada bayi biyu ga masarauta a kowane kawowa kafin ku wuce inda zaku je "
"ehh mun sani zamu fitar da haraji kaman koyaushe,saidai kuyi mana uzuri ,domin zamu baku wanda suka gaji sosai saboda bazasu iya tafiya daganan zuwa masarautar saraham ba "
"shikenan ku nuna mana su ,babu komai idan suka huta za'a basu aiki "
mai bayinne ya jawo wani dan saurayi mai laushin jiki dakuma fahreeyah ya turasu gaban mutanen da suka zo ,
"wannan sune lagar tattu a ciki ,wanda bazasu iya doguwar tafiyarmu ba ,"
kallonsu suke kafin suka bawa wasu bakaken bayi dasuke tare dasu damar sakasu a wani kejin ,amma shi na karfene yana da zanen sarauta a jiki
tafiya akeyi saidai basa ganin hanya saboda yanayin tsarin karfen kejin ,kofar masarautar aka bude suka shiga har zuwa harabar wajen masarautar ,fito dasu akayi zuwa gaban UWAR BAYIN  masarautar aka durkusar dasu ,kallonsu take cikin kaskanci kafin tace,
" menene sunanku ? "
"ni sunana fahreeyah "
"ni kuma sunana KHAMEEL "
"to ita wannan macen (tafada tana nuna fahreeyah )ku kaita sashen DANDALIN BAYI ,shikuma ku kaishi wajen YAN BARGA ,kutashi ku bisu maza ,gakunan kaman a karya ku ".
Tisa keyarsu akayi kowa zuwa inda aka bashi yayi aiki.
Tafiya sukeyi fahreeyah na binsu abaya ,tana tunanin tashi daya rayuwarta tasake juyawa a karo na biyu ""an gudu ba'a tsiraba kenan "",ta fada acikin ranta ,wani doguwar hanya suka bi tana biye dasu a baya har zuwa wani katafaren muhalli mai dauke da dakuna a cikinsa da yawa.
Wata mata ce tafito daga cikin wajen ta zuba wani uban adoo mai daukar ido ,maraba tayi musu cikin rangwada da kalmasa harshe ,
"maraban ku da zuwa wannan dandali mai dauke da abubuwan shakatawa dakuma dauke kewa ,mai yake tafe daku ?"
"sakone daga uwar bayi ,tace a kawo miki wata sabuwar baiwa zata fara aiki anan wajen ,"
"shikenan zata iya shigowa domin baje tata basirar a wannan fagen "
"tohh maza ki shiga ta amsheki ".
Matarce ta jata zuwa cikin harabar muhallinnasu ,tsayawa tayi ta tareda zuyowa tana kallonta,
"yan mata baki bani sunanki ba ?"
"sunana fahreeyah "
"ohhh suna mai dadi tun daga sunanki ke mai kyau ce sosai ,gaskiya zaki haska idan kika goge nan gaba kadan "
"uhmm addah bangane abinda kike nufi ba fah "
"😊😊,baki ganeba ,ki bari nan gaba kadan zaki gane mai na ke nufi ,kedai ki biyoni kawai yar sheela 😊😊"
"uhmm amma addah ..........."
"daina kirana da wata addah ,kice kawai ZILZILIYYAH ,haka sunan yake "

SADI -SAKHNA ce

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now