Chp(35)na yarda da kai

69 12 3
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(35)
Bai dade da tafiya ba yadawo a keken doki,tareda saheel ,Yana shiga yasamu inna ta gama shiryata tsaf,sallama yayi mata kafin ya dauketa suka fita.
A hankali suke tafiya har suka isa ga sashen yarima amam din,wanda saboda dare babu wanda yasan mai yake faruwa,saida saheel ya tabbatar komai yayi dadai kafin yayi musu sallama,a wajen fahreeyah kuwa iya zaman da tayi a cikin kkeken har ya gajiyar da ita,suna isowa kuwa daya kwantarta tafara bacci,gashi taji lallausar katifa dama.
Da safe tun kafin fahreeyah ta tashi har yarima amam ya sallami duk wasu masu aiki a sashensa,yasaka khairiyyah saboda zaman fahreeyah a wajen yazama sirri,tun asuba take bacci har wajen goma na safe hakanma saida amam ya yaye labulan dakin kafin ta bude ido,hada ido sukayi dashi yana mata murmushi wanda itama Murmushin tayi,
"Barka da tashi haskena ,da fatan kin tashi lafiya?"
"Lafiya kalau,ina kwana yah amam"
"Uhm uhm banason wannan amam din kisaja shi yanzunnan"
"Toh shikenan,nooreenah!!"
"Wow sunan yamin dadi,toh tashi muje wanka kizo kici abinci kar rana tayi yunwa ta kamaku koh"
"Toh"
Kokarin tashi take daga kwancen,inda yayi saurin daga ta sama yana mata dariya wai ta tayi nauyi,dukan wasa takai masa a kirjinsa kafin ta kara rungumeshi suka shiga bandakin.
Sun dade a bandakin kafin suka fito shima da ruwa a jikinsa da alama wani wankan ya sake yi,
"Faryah kinga kinsakani nasake wani wankan koh,gaskiya yanzu wankanki yakara wahala ba kaman da ba"
"Ka ganka koh,idan kasake cewa na kara girma,bazan sake yin wankan ba toh"
"Yi hakuri bazan sake ba"
Kama kunnensa yayi yana yi mata dariya,itakuma tana kara shagwabe masa,towel din kanta ya cire kafin yabude drawer gefen kayansa,babu abinda yake ciki sai kayan mata marasa nauyi irin na masu ciki kala kala masu kyau,zare ido tayi kafin tace,
"Yaushe Har aka kawo wannan kayan?"
"Abubuwa dayawa ma an sanja su saboda zuwanki,har kujerun falo dakuma dana zama,duk ankawo wanda zaki iya amfani dashi,sannan khairiyyah mah tana waje ta gama miki abinci irin wanda inna tace ki dunga ci"
Dan tsabar mamaki kasa magana tayi said hawaye daya zubo a kan fuskarta,rungumo shi tayi takara kankameshi,
"Duk wannan abun kayine danni?"
"Ba abinda bazanyi danke ba faryah,tunda narasaki narasa rabin haskena sai na wanda ummah take haska min,koda zan rasa komai indai babuke aciki toh hakan bazai dameni ba,sannan duk abinda zanyi bazan biyaki wahalar dakikayi da gudan jinina ba dayake cikinki,dan haka kisa a ranki komai nawa nakine"
Tun daga haka ya rufe mata baki sai kawai binsa da take da ido har yagama shafa mata mai da kaya,daukarta yayi bai zame ko ina ba sai kan kujerar da aka kawo saboda zamanta,khairiyyah ceh ta kayan abincin a dan tebur ta gama hada komai,
"Faryah ga abinci na baki a baki ko zaki iya ci uhm?"
"Ahah kace wani waje zakaje ina,zan iya ci dakaina,ba inda yake min ciwo yanzu"
"Toh shikenan gimbiya tah,to baby karka fitini ummahn ka saina dawo"
Ya karisa maganar yana sumbatar cikin fahreeyah wanda yayi wani irin girma na ban mamaki.
Bayan amam yatafine khairiyyah ta matso kusa da fahreeyah bakinta cike da gulmar taji karshen zance,
"Keh fahreeyah,au ranki yadade ya akayi haka ta farune,wai dama duk labarin saheel din da kike bamu ashe yarima amam kike nufi tab?"
Saida fahreeyah tayi dariya mai isarta kafin tace,
"Da farko karki kara cewa ranki yadade dinnan,inkinaso mushirya yanda muke a da,abinda yafaru dinnan kuwa haka nima naga yakasance.
Ya kuma naga kinsaka abincin kadan ki kara mana kawai?"
"Ahah wannan abincinki neh ni zan yi nawa idan inaso,aini gaba ta kaini,yau yarima amam harda cemin ya na kwana,kuma yacemin nayi duk abinda nakeso,kawai yana so na kuladake idan bayanan,kai aini babu wanda yafini jin dadi yanzu"
Haka sukayi ta hira bayan sunci abinci har saida fahreeyahn tayi bacci itama khairiyyahn taje ta kwanta ta huta.
Da haka ana tafe har aka shiga wata na tara ya cinye wata na goma shima yayi nisa yana shirin fita amma babu alamar haihuwa,yanzu har yakai ko tsayuwa fahreeyah bata iyawa dakanta sai an taimaka mata,ta rame sai cikin jikinta kawai ake kallo,tazama abin tausayi duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata,yanzu duk bayan kwana biyu sai inna ta zo dubata,yarima amam kuwa yanzu sai yayi sati bai fita ko ina ba,har safeenah tafara Mamakin rashin zuwansa sashenta wanda a da ba haka yake ba,ganin abin bazai kaita bane yasa ta kira saheel domin tambayar sa shima bai wani bata wata kyakykyawar amsa da ta yarda da ita ba.
Da dare mahutar bawa ,kowa ya kwanta a gidansa domin yah huta,amma a bangaren fahreeyah ba haka abin yakeba,domin a yanzu bata da ikon kwanciya saidai ta jingina kanta da bango ko kuma a kirjin amam,wanda shima yanzu tausayinsa ta ke ji,a lokacin baya ba abinda take buri daya wuce ta ganshi amma yanzu abin yajuya,domin gani take kaman ta zamar masa wahala,batada amfanin komai sai saka kowa yi mata aiki,tasan yanzu ta gama isar kowa da wahalarta.
Shiru dakin yayi inda amam ya dauka tayi bacci saboda shiru da tayi tana tunanin rayuwarta,dago kanta tayi dayake kan kirjinsa yana shafa kanta,shima kallon fuskarta yakeyi duk da baya kallon ainihin fuskar ta saboda duhun daya dan rufe dakin ,fitilar gefen gadon ya kunna kafin ya tambayeta,
"Bakiyi bacciba har yanzu ?ko fitsari zakiyi muje na kaiki?"
"Ahah kawai ina tunani ne"
"Tunani kuma,amma kinsan inna da tazo jiya tace miki banda tunani ina,dan yanzu ma numfashin ki koyaushe sama sama yakeyi,wanda hakan yana tayarmin da hankali"
"Kayi hakuri nooreeh,amma bayanda zanyine,......yawwa bani labarin mai yafaru sanda bana nan toh"
Tafada tana kawar da zancen dazun ganin yanda fuskarsa ta nuna alamun damuwa,
"Abubuwa da dama sunfaru kaman yanda suka faru a naki rayuwar kema,ciki harda tilastamin auren da akayi,da kuma rashin lafiyar dana kamu da ita,duk da nasan cewar kinsan labarin saidai nakasa fuskantarki nakara sanar dake abinda yake faruwa,nashiga cikin damuwa harma da wani duhu daya shiga cikin rayuwata a dalilin rashinki kusa dani,a baya kafin nasake haduwa dake nayi tunanin cewa a haka aka haifeni bazan taba haihuwa ba kaman yanda wasu suke fada,saidai yanzu na tabbatar cewa bayan na rasaki ne matsalar ta faru dani,ganinki da cikin faryah ba karamin farinciki nayi ba,zan iya yimiki komai ba tareda na ji alamar gajiyaba,koda zan gushe a yanzu toh zan kasance mai farinciki idan na tuna  cewa gudan jinina yataba motsawa acikin matata"
Wani irin kuka fahreeyah tasaka jin maganar da take fitowa daga bakin mijinnata ,da irin soyayyar dayake yi musu itada cikinnata, il
"Nagode da soyayyarka mijina saidai gashi na gaza taka wata rawa a rayuwarka tun bayan haduwa dani sai kai kadaine kake ta fama dani"
Rike fuskar ta yayi tareda jijjiga kansa,
"Shshshshs,ya isa haka wannan kukan na menene kuma"
Ganin bazata daina bane yasaka shi hade bakinsu waje daya da nufin yadaina jin karar kukanta a cikin kunnensa,wanda yake saka zuciyarsa harbawa cikin yanayi na marar dadin jin.
Saidai me..........tsumin dake binne cikin ransa ne yafara tasowa hadi da kuma kewar duk wani nau'i na jikinta a cikin ransa,kara zurfafa sumbatar yayi har yakai numfashin su yafara yin nauyi,kallon fuskarsa tayi bayan yajanye fuskarsa kadan daga nata.
Shiru sukayi babu wanda yace wani abu,ganin hakanne yasa fahreeyah ta dago fuskar amam din suna hada ido,zare ido tayi ganin sakon dayake kwance a cikin idanunsa,saurin tsinke kallon da suke yayi tareda kokarin kashe wutar fitilar daya kunna,kafin yafara magana cikin murya kaman mai jin bacci,
"Dare yafara faryah yakamata kiyi bacci yanzu kinga............."
"Ahah na kwanciya ceh abinda nake bukata ba yanzu"
Kallon ta yayi da mamaki jin yanda tayi saurin katse maganar sa da sauri,
"Ina bakason nashiga damuwa koh?"
Daga kai yayi batare da ya yayi magaba ba,
"Toh kallonka cikin wannan yanayin shine damuwa ta kuma shine zai haifarmin da abinda yafi tunani ma"
"Me hakan yake nufi kenan"
"Nasan kasan mai nake nufi,sannan inna tacemin hakan ma zai iya sauri kawo min nakuda da wuri"
"Amma faryah.............."
Saurin katseshi tayi tareda cewa,
"Na yarda da kai yah amam,nasan bazaka taba cutar dani ba,ko kuma wahalar dani"

Uhm masoya

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now