Chp(38)bantan uban can

60 9 2
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟

💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

......Dedicated to proficient writer association........

Chp(38)
Saheel ne yadago da fuskar nasreemah da take manne a kirjinsa har sannan,har sannan kuka take fukarta ta hade da majina da hawaye,
"Meya kaiki zuwa sashensu kullum har suka baki abu kika karba kika yi amfani dashi,har da cewa karki fadawa mijinki kuma dan wauta ke a dole zaki mallaki miji koh? Kika cutar dashi kema kika cutar da kanki yanzu iya laifinsu kika gani koh?"
Cikin shashshekar kukan ta fara magana,
"Ahah,dan allah da farko kaima kayi hakuri da zuga baba da mukayi akan soyayyarka da khaleesah ka yafemin ,sannan ni yanzu bazan iya kallon fuskar amam da irin laifin dana aikata masa,zan tafi gidanmu ne idan an dau wani lokaci zanzo na bashi hakuri na fita a rayuwarsa,hakika a yanzu nafi tsanar kaina fiye da komai sannan nayi tirr da halina,zan fita a rayiwar kowa zan daina mu'amala da mutane ,hakanne kawai kwanciyar hankalina,ko yanzu na dan samu kwanciyar hankali tunda ga matar sa nan tana da ciki,ko ba komai zai dinga ganin gudan jininsa,nayi farinciki kuma da ba a jikina ya fitoba nasan zai ta kallonsa a hakan har karshen zamansa dashi,na cutar da shi da yaws bana fatan sake kuma zama dashi"
Tashi tayi daga jikin saheel din tana gyara gyalenta dayake wuyanta,har sannan jan zuciya take saboda kukan da tasha,wucewa tazoyi zata fita daga gidan sai ji tayi anruko hannunta ta baya.
Kowa kallon abin yayi da Mamaki,itama zuyowa tayi dan ganin mai ya faru,fahreeyah tagani rike da hannunta gam kaman tana tsoron ta saketa ta bacewa ganinta,cikin sanyin murya kaman mai tsoron magana tafara cewa,
"Meyasa kika yanke wannan hukuncin?,kina tunanin shine dadai,bahaka bane,a labarinki sun fi cutar dake fiye da kowa"
Kowa Mamakin jin abinda fahreeyah ta fada sukayi,jijjiga kanta tayi da alamar karfafa abinda tace kafin ta jawo nasreemah ta matso har zuwa kusan tsayinta,
"Hakane yanda na fada,sun fi cutar dake ,sannan hukuncin da kika yanke na cewa zaki kulle kanki daga cikin mutane hakan zai zama cutarwar tayimiki yawa,saboda sunyi amfani da yardar dakika musu da zuciya daya suka cutar da rayuwarki da ta mijinki wanda ke a ganinki taimakonki sukeyi,karki sake cewa kinyi allah wadai da halinki,saboda halinki shine mafi kyau,domin kina yarda da mutum batareda kinyi tunanin zai cutar dake ko a'a ba,hakan dakikayi allah yana kallonki kuma shi zai kareki daga cutarwar mutane saboda kin mika lamarinki gareshi,yanzu da suncemiki ga magani kisakawa mijinki ya daina haihuwa zaki saka masa?"
Saurin jijjiga kai nasreemah tayi tareda kara rushewa da kuka,
"Ahah bazan taba iyawa ba,saboda ina sonsa sosai da ............sosai......ina sonsa....har cikin raina,yanzuma jinake kaman kowane lokaci zuciyata ...zata iya bugawa saboda abinda na aikata...."
"Toh karki kashe aurenki kaman yanda sukeso,ki zauna a dakinki,sannan ki kare mijinki da duk iyawarki tunda yanzu allah ya nuna miki wanda suka cutar daku,kiyi amfani da hanyar dasu ka bi na yardarki kema ki kare aurenki da kuma abinda kike so......"
Tarine ya sarkake fahreeyah saboda doguwar magana da ta dade tanayi,dukkansu kowa matsowa yayi kusanta da niyyar taimaka mata,hannun nasreemah ta rike da sauri lokacin da amam yadaga ta da niyyar kaita daki,cikin nishin magana tace,
"Karki tafi idan bana wajen,kiyimin alkawarin bazaki tafiba,dan Allah karna tashi naga bakyanan kinji"
"Bazan tafiba namiki alkawari,allah yabaki lafiya,ya kuma saukeki lafiya"
Murmushi fahreeyahn tayi mata kafin amam din ya tafi daki da ita domin ta huta.
Kowa shiru yayi a falon,har yanzu nasreemah tana share fuskar ta da hawaye yake binta lokaci zuwa lokaci,saheel ne ya kalli nameemah da take tsaye har sannan kafin yace,
"Yanzu iron wannan baiwar allah tayi miki kama da mai cin amanarki a wajen mijinki?"
Kaman jira take kuwa itama ta rushe da kuka wanda dama yazo mata iya wuya,
"Ahah batayi kama ba,tabbas da bakin wani a hada hakan sai yanzu na kula da hakan,macen dazatayi kokarin hana kishiyarta tafiya daga gidan aurenta ba'a samunsu sosai.nayi nadamar abinda yafaru,dan Allah ku yafemin"
"Ahah ba'a wajenmu zaki nemi yafiya ba saiki bari kinema a wajanta,sai ma kunji irin halin rayuwar data shiga dukkan ku babu wanda zata iya jurewa............cikin magana ta fahimata yagama basu labarin rayuwar fahreeyah tun daga kan haduwarta da amam yana matsayin saheel da aurensu har zuwa bautar da tayi a masarautar BAHMEER da kuma shiga kurku da tayi a dalilin nameemah har da kwantar da cikinta da inna Kainana tayi da haduwarsu da amam dakuma tsawon watannin cikinta da yayi a jikinta"
Ba iya tausayin fahreeyah ne yakamasu ba harda wani sanyi da jikinsu yayi na dan wani lokaci kafin suka sauke numfashi a tare.
Ba abinda yake fitowa daga bakinsu sai salati wanda sukansu basusan sunayi ba,ganin abin bana kare bane yasa saheel kallon nameemah yace,
"Ke yakamata ki tafi wajen mijinki tunda tare kuka zo dashi"
Batareda tayi musu ba ta kama hanya ta fita a dakin har sannan bata gama dawo hankalinta ba da jin labarin abinda yafaru.
Fahreeyah kuwa har sanda amam ya kwantar da ita a kan gadon,take jin wani bakon yanayi yana yanko mata kawai murmushi tayi masa tareda cewa ba abinda yasameta,kara kallonta yai kaman mai son gano wani abu yasake cewa,
Kalau kikeji ba wata matsala koh?"
"Ba komai nooree,saidai zancen zaman nasreemah dan Allah karkace komai in dai ba rarrashinta zakayi ba,kabari tukunna zuciyoyinku su huce tukunna,hakika nima naji zafin abinda yafaru a raina bare kuma kai da nasreemah wanda abin yafi shafarku sosai,duk nima ya shafeni amma ba kaman ku biyun ba"
"Yah isa haka kidaina wannan maganar tukun,ki kulada halin da kkke ciki ma ,dan ni ban yarda da yanda jikinnaki yake ba,dan naga sai gumi kike da sauke numfashi"
"Bakomai kaje wajen ummah,tun dazu kake cewa yau baka je wajenta ba"
"Shikenan,ki kula bari na fadawa khairiyyah tazo ku zaunz"
A wajen nameemah kuwa har ta isa sashen da aka saukesu tana ta tunanin yanda rayuwar fahreeyahn yakasance , ba abinda yake damun zuciyarta kaman irin hukuncin da ta bayar a yima ta,tun daga bakin dakin take jin magana saidai bata kawo komai a ranta ba ta shiga.
Mijinta tagani a kan gado yajuya bayansa,da alama kuma macece a kasansa yayi mata rumfah,har tayi niyyar yin ihu saikuma taji muryar sa yana cewa,
"Ni fah haryanzu ina burin na lasa zumar jikin yarinyar nan,da kikace sunanta fahreeyah,duk ke kika min cikas kuka shigo da nameemah"
"Lallai ma maza,yanzu duk abinda nake maka amma baka bar zancenta ba,yanzu dai kaji tafi karfin ka,saika nemi yanda zakayi,yawwa ya zancen y'antani dakace zakayi da kuma aurena,kasan bazan iya zama kuma da wannan matar taka ba"
"Zanga yanda za'ayi amma saidai kiyi hakuri ku zauna tare dan ina son nameemah sosai kawai..........."
Karar tangaran din da nameemah tafasa ne yadawo da hankalinsu gabadaya,juyawa yayi ya kallin kirisah da take kwance da kuma nameemah da idonta yayi ja tashi daya,
"Ke bake kika ce acan zata kwana ba?"
"NI.........ma bansan meyasa ta dawo ba....."
Bantan uban can,karku gaji reader a biyoni😂😂😂😂😂😂.

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now