(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)
💎💎💐💐WATA RAYUWA 💎💎💐💐
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
(The legendary novelist),🌄🌄
(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
💎💐 ..... WATA RAYUWA....💎💐phone number:09035784150
telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0
whatpad :@SAKHNA03
......Dedicated to proficient writer association........
chp(18)
Shiru tayi a tsaye bata da niyyar shiga cikin dakin saida zalziliyyah ta ne takula da cewa ita kadai take tafiyanta wanda takee bayan ta bata ma biyota ba ,juyowa tayi takalleta tareda cewa ,
"Menene kuma yatsaida ke haka? Kibiyoni na nuna Miki inda zaki zauna ko a wajen zaki kwana iye?"
"Ahah dama naji kince wai zamu dunga shakatar da wasu .......nikuma ina da aure fah gashi....."
" Ya'isa haka yan mata , me kike tunani,kina da zavi? to kicire hakan a zuciyarki ke baiwa ce yanzu Wanda zata bada jikinta don bakin masarautar nan suji dadi,Dan kimanta da cewar kintaba rayuwa a baya bare kuma aure ,idan kuma bahakaba zaki fuskanci hukuncin da bakya tsammani"
Jikin fahreeyah ne yayi sanyi game da jin furucin shugabar tasu, Wanda har aka kaita wajen dazai kasance muhallinta kukane yake zuba daga idonta saboda rashin mijijnta datayi Wanda tasan a yanzu yayi mata nisan da bata tsammanin zata iya cimmasa .
Wani daki zalziliyyah takaita mai girma ,saidai daga gani akwai mutane masu Dan dama dasuke rayuwa a ciki, saboda abubuwan kwanciya da kuma shirgi na masu dakin da idonta yayi arba da shi ta ko'ina,muryar zalziliyyah ce ta saka ta dawo da hankalinta daga barin kallon dakin zuwa kallon shugabar tasu,
"Toh wannan shine rukunin dakin dazaki dunga zama ,shi wannan wajen shine muhallin Wanda zasu dunga taryar bakin dasuke tsaka tsaki,wato ba masu matsayi sosai ba, yanzu bari naje ina da abinyi,zamu kiraku training idan kinyi s'a zaki iya shiga rukunin bayi masu tarar manyan baki,"
Duk magananr da takeyi har tayi ta gama fahreeyah bata tanka mata ba, saboda zabar jimamin halinda ta tsinci kanta a ciki.
Dudduba dakin tafarayi kozata samu wajen da ba kayan wata a gurin ta zauna,wani waje tagani mai a gefen kayan wata ta wajen barin dama a dakin, saida ta fara dan gyara wajen kafin ta zauna,jin kamar jikin ta yayi tsamine saboda tafiyar dasuka yi a hanya ya sata dan kishingida ko zata samu dan hutu kafin jiran mai rayuwar zata zo mata dashi kuma in an jima.
Can cikin baccine taji ana zungurar ta kafa,hakanne yasata tashi a razane domin ganin mai ya,wata mace tagani a tsaye a kanta tana mata wani irin kallo na rashin mutunci,yayin da matan dasuke bayanta kuma suka fara magana cikin dariya,
"Yau zaki san taka wajen KIRISAH,duk abinda ya faru dake kinyiwa kanki"
Ita wacce suka kira da Kirisah dinne tafara hura hanci cikin fushi tareda cewa
"Ba magana nake Miki ba?ko keh kurmiyace ba zaki ban amsa ba iyee?"
"Uhm ban.......san .wajenji bane,dazu zalziliyyah ta kawoni, kuma na ga,bakowa a wajen ne shiyasa na zauna"
"Kutt harni kike cewa dan kinga ba kowa a wajenne kika zauna?t to barikiji nafada miki,cewa nan duk wajena ne, domin ni waje daya yayimin kadan, kuma duk abinda bayanke a dakinnan akeyi,tashi kibani waje,kinyi sa'a ke bakuwa ce dakin fuskanci hukunci daga wajena"
Tashi fahreeyah tayi tareda matsawa can gefe a dungun dakin ta zauna tana mai da numfashi sakamakon wani zazzabin daya fara ziyartar jikinta a karo na biyu,zawo rigarta take tana sake rufe dukkan jikinta saboda sanyin da take ji yana ratsata,a dunkule a wajen da take baccin wahala yadauke ta.
Washa gari da wuri ta tashi saboda baccin kasan datayi saidai bataji zazzabin a jikinta ba kaman yanda ta kwana da shi jiya da daddare,yunkurawa tayi ta tashi saboda jikinta ba karfi,mata tayi arba dasu sun cika dakin masu irin kayan ta sak, saidai kaman wanda ita suke jira da gansu,haka taga sun fara tashi a tare kowa tana nufar hanyar waje,itama binsu tayi dan dama tanason ta rage marar ta saboda fitsarin daya ci karfinta sosai,wani wajen ta kula dashi suna shiga dakayansu wasu kuma na fitowa jikinsu a jike, jikinta ne yabata cewar bandaki ne dan haka kawai sai ta nufi wajen,ta saka kai zata wuce kuma sai taji maganar wata a bayanta tana fadin
"Baiwar Allah naga kina shirin shiga wajen wanka amma ba kayan dazaki sanja,ko ba'a baki kaya kala biyu bane?"
"Ahah an bani yanzu fitsari zanyi ne"
Murmushi tayi mata kafin ta ce
"Kuma fitsari a wajen nan, Hala ko ke bakuwa ce?"
"Ehh ni bakuwa ce"
"Ayyah to zo muje Nara kaki wajen fitsarin toh"
"To nagode"
Bin take a bayanta har suka je wani wajen amma ginin wajen sa masu matsakaicin girma ne, tsayawa tayi tareda juyowa ta kalli fahreeyah,
"To nan shi ne wajen bahaya da fitsari,wancan kuma da kika gani wajen wanka ne"
"Nagode baiwar Allah"
"Kikirani da Sareenah"
"Toh"
Saida tashiga tagama abinda zatayi kafin ta koma inda aka kaita da sunan shine dakin ta, sake zama tayi wajen da ta kwana,saikuma ta ji ana shelar zuwa cin abinci, itama binsu tayi a baya domin ganin wace hanya zasubi.
Wajenne Shima kaman tsarin dakunansu,wato filine kowa yasamu wajen da zai zauna kawai.
Bayan sun gama zama ne aka fara binsu da abinci a kwano ana raba musu,duk wanda yagama sai ya kai kwano zuwa wani waje daban kafin ya fita,ita dai duk abinda suka yi binsu take tana aikatawa kawai, wajen wanki ne kawai bata bisu ba saboda kayan ta sabine babu datti a jikinsu tukunna.
A haka dai suka gama al'amarinsu na ranar har zuwa lokacin da wani daren yasake shiga inda shima zazzabin ta yasake lallabowa daya ga dare yafarayi,haka ta gama sheshekar zazzabin ta har bacci ya dauketa.
Washa gari bayan sun tashi, fahreeyah bata sha wahala ba wajen gano dukkan al'amuran da suke gudanarwa a kullum.
Saidai yau shugaba zalziliyyah ta kirasu zuwa training lokacin dasuka gama cin abinci,da koyarwar gyaran jiki aka fara nuna musu,sai kuma kwalliya da kuma karairaya domin birge duk wani da na miji,sabin bayin da'aka kawone aka fara yiwa kwalliya don ganin nasu zubin,tun ana fara kwalliya zalziliyyah ta kalle ta tareda cewa
"Fahreeyah na maida ke rukunin masu tarar manyan baki"SADI-SAKHNA ce

YOU ARE READING
Wata Rayuwa
AdventureLabari kan karamar budurwa data samu kanta cikin kangin rayuwa,!!!! Faryah karki taba barina ke tawace har abada,hakika nayi dacen samunki, Toh amma yazaiyi daya bude ido yarasata a duniyarsa? Sannan ita yazatayi da WATA RAYUWAR data tsinci kanta? W...