Chp(41)hakan bazai yiwuba

78 9 0
                                    

The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(41)
Ba komaine yasaka su amam cikin kundin mamaki ba saiganin yaya uku rus dasikayi a gaban fahreeyah suna ta zabga ihu,musamman ma yarima amam wanda yatafi yah barta da d'a guda daya kuma yadawo yatarar ds y'ay'a har guda uku.
Saida fita sukayi daga cikin Mamakin ganin uwar gayyar wato fahreeyah ta zube a kasa kamar bata numashi,taimakon gaggawa inna kainata ta shiga yi bata,saida ta farfado kafin amam ya dauketa zuwa bandaki kaman yanda innan tace yayi,khaleesah ceh ta dauki yaran itada nasreemah sukayi hanyar dakin nasreemah domin gyarasu,bayan an raba su da jikin mabiyyar da suka zo duniya a cikinta.
Inna tadade a bandaki tana gasawa fahreeyah jikinta,da kuma ruwan magsnunuwa saboda wahalar da jikinta yah sha.
Bayan sun fitone fahreeyahn ta zauna a akan gadon itakuma ta fita da sauri zuwa dauko wani abun.
Amam neh yah kalli fuskarta wanda tayi fayau saboda wuyar data sha,murmushi tayi masa lolacin da suka hada ido,wanda shima Murmushin yakeyi,
"Mai zan kira da wannan matar data yi kewar rashin mijinta harna tsawon sama da shekara guda,amma kullum burinta shune yaushe zata ganshi?,sannan mai zan kira wannan uwar wadda ta dauki cikin y'ay'anta har na tsawon shekara biyu,ta jure wahalar su batareda ta kasaba har ta haifesu?"
"Ka kirata da matar shamam"
Nasreemah ceh ta amsa masa tambayar tana Murmushi hannunta rike da na mijin itakuma khaleesah tana rike da matan guda biyu,fahreeyah ceh itama ta kalli amam din bayan su nasreemah sun saka mata y'ay'an akan cinyarta suna mata sannu,
"Ni mazan kira kishiyar data hana idonta bacci har na tswaon kwana uku ta tsaya akan kishiyarta wadda take kan nakudar haihuwa kawai dan soyayyar da take mata?"
"Itama ki kirata da matar amam,domin nikadaine keda wannan kalar matan da babu kamansu"
Dukkansu dariya sukayi da kuma Mamakin amsarsa,kafin fahreeyah ta dora dacewa,
"Kuma nakirata da yar uwata,wanda nakeji da ita har cikin raina,babu abinda zan iyah saka muku dashi ,duk wadanda suka kula dani lokacin da bazan iyah komai ba sai dai godiya,hakika inada masoyan da babu wanda yasamu ya irinsu a ganina".
Dukkansu kowa murmushi yayi harda sarauniya zulaikha wanda bayan fitar inna kainata daga wajensu ne ta fada mata halin da ake ciki,karisawa kusa da fahreeyah tayi tareda rike fuskar ta a hannnuta,
"Keh alkhairi ceh a cikin wannan nahiya,y'ata,babu abinda zan cemiki sai godiya dakuma jinjina,haka kema nasreemah (tafada tana riko hannunta dama tana zaune a gefenta,wanda har yanzu bakinta bai rufuba saboda farinciki dakuma murna da take ciki,ganin ba iya karshen rayuwarta ba kenan),kema ina miki Godiya,sannan kuma ina baki hakuri akan cutarwar dasu zulaikha suka miki keda mijinki,kuma naji hukuncin dakika yanke na zama da amam duk da kinsan bazaki haihu ba,wannan abin ayaba mikine sannan da jinjina miki"
"Ahah ummah kibar fadin hakan,nice yakamata na bada hakuri a gareku bisa halayena duk hakan ya faru,sannan sanadin yar uwata kuma abokiyar zamana,fahreeyah itace sanadiyyar fito dani daga duhun dana fad'a,ta nunamin haske batareda tayi tunannin ni kishiyarta ce ba,wannan abune da bazan taba mantawa ba,kuma a yanzu zama dasu shine babban abinda zai kasance yana sakani farinciki ba wai samun haihuwa ba"
Itama fahreeyahn rikota tayi tana tayata kukan datake,ganin hakanne yasa safeenah ta katsesu tareda yi misu bayanin abinda yafaru jiya,tsakanin itada zulaikha,dakuma shirin da suka hada itada nameemah,kowa Mamakin abin yayi tareda fatan allah yasa yatsaya iyah hakan.
Acan kuwa fada zulaikha ce a daure itada neelah dakuma waziri sunyi tsumu tsumu,ga mutanen fada sun taru kowa yana jimamin abinda yafaru,tambayar zulaikha yasakeyi akan tafada masa abinda tafada jiya agaban kowa,
"Yanzu mai martaba har zaka yarda cewa nice na fadi abinda kake zargina dashi?,idan har za'a ce nice na illah ta yarima amam da guba,shekara daya da wuce,toh ai bincike yanuna cewa haka aka haifeshi baya haihuwa,in kuma kana ganin karya nake toh akira masa nan magani su sake fadan abinda suka gani a bincikensu ,idan kuwa yazamo haka aka haifeshi toh kaine kafara tsufah bakaji abinda akace sosai bah"
Shiru sarki huruddeen yayi ,kafin ya aika akira masa sarauniya safeenah ita da yarima amam,cikin sauri kuwa dogarai guda biyu suka tafi kiran da aka umarcesu dayi.
Sun dade sai gasu ,saida suka sunkuya cikin girmamawa kafin suka isar da cewa suna kan hanyar shigowa fadar.
Lokacin da su safeenah suka shigo itada amam,har masana maganin masarautar ciki harda inna kainata,duk ankirasu domin sake tambayarsu abinda suka gani a binciken rashin lafiyar amam din.
Cikin hadin baki suka bada shaidar cewa,a yanda rashin lafiyar yake yanuna cewar bashida kwayoyin halitta, da haka aka haifeshi,kuma cikin gaskiya haka binciken yanuna.
Murmushi zulaikha tayi itada waziri,kafin tace,
"Kagani koh,na fadamaka cewar ai bakaji dadaiba,inaga kaman tsufah ne yafara kamaka,amma yaushe zan cutar dashi kuma harda wani kashe masa kwayoyin haihuwa,yanzu kagane cewar amaryarkace take hada komai kenan,dan haka saika san hukuncin dazaka dauka"
Takarisa maganaar tana kukan munafurci,dukkan fadar kowa tausayinta ne yakamashi,inda dogaren dake kusa da ita suka sunkuya domin since igiyar karfen dake hannunta,
"Dakata!!!!,daga yanke hukuncin tukunna,ai bamu gama buga wasan ba"
Safeenah ceh tafad'a tana Murmushin gefen baki,alamun da abinda take takama dashi,tafa hannun ta tayi sau uku.
Aikuwa saiga su nasreemah da nameemah da kuma khaleesah dukkansu rike da jinjiri a hannunsu,saikuma khairiyyah wacce tariko fahreeyah suka shigo cikin fadar,amam neh ya matsa kusada fahreeyahn ya gyra mata kujera a wajen tareda zaunarta wanda har tafara haki,saboda tafiyar da tayi daga sashen amam din zuwa cikin fadar.
Kowa idonsane yakai kan mutanen da suka shigo fadar musamman jariran da aka shigo dasu da kuma matar da yarima amam din ya zaunar akan kujerar.
Sarki huruddeen ne ya kalli safeenah tareda tambayar ta meyake faruwa,bata amsa masaba,sai yaron da ta karba a hannun nasreemah ta nufi inda mai martabar yake,
"Wannan yaron da wa yayi kama?"
Saida yakarewa jinjirin kallo,kafin yace ,
"wannan yana kama da dankinki sosai,da alama y'an uwanki  wata haihu koh,.........kai amma yana kama da amam,dan wannan hancin kuma yana kama dana mahaifina"
"Kadauki amsar dadai,tabbas jinina ne,kuma dama zaiyi kamada babanma,tunda shima jininsane,a takaice dai wannan yaron d'ane ga d'anka amam da kuma fahreeyah wacce ka gani akan kujera a zaunar da ita,harma da sauran jinjiran dasuke hannun su nameemah,jiya allah yasauketa ta haifi y'ay'anta guda uku,bayan daukar cikinsu da tayi na tsawon shekara biyu"
Kowa mamaki yayi da abinda safeenah tace amma babu alamar sun yarda da abinda tace.
Murmushi safeenah tasake yi kafin tace,
"Nasan ba lallai kowa yah yarda ba,amma ba abinda yagagari allah,yanzu kowa zaiji labarin abinda yafaru,.....................bayan ta gama basu labarin abinda yah faru tsakanin amam da fahreeyahn,harma da kuma abinda su nasreemah sukaji su zulaikha suna fada.
Zulaikha ceh tayi wani kara,cikin daga murya tace,
"Hakan bazai taba yiyuwa ba ,bazai yiwuba,ba haka natsaraba,sam.............hahahahahaha.

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now