Chp(33)tohh fahh!!

53 8 3
                                    

(The legendary novelist📝💚💚)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(33)

Dagowa yayi ya kalli mahaifiyar tasa wanda alamar tambaya da kuma damuwa suke kwance akan fuskar ta,Tunani yayi a ransa idan yasanar da ita wata damuwar zata sake sakawa a ranta,
"Ahah ummah ba abinda nace"
"Komadai menene yakamata ka kasance mai tawakkali da kuma juriya ga duk jarabawar da allah yayi nufinka da ita,sannan haihuwa ta allah ce idan allah ya gada mar zaka ga jininka a duniya toh ba mai hanaka ganinsa,kasaka wannan a ranka"
"Nagode ummah"
A wajen sarauniya zulaikha kuwa tagama kama nasreemah a hannunta dan yanzu sai yanda tayi da ita ,bata jin maganar kowa sai ta zulaikha dan a ganinta babu wanda yakaita sonta a masarautar.
Wasa wasa fahreeyah ta shafe wata uku a wajen inna kainata,sannan duk a zaman da sukayi bata taba ganin kasawa daga wajen innan dan kula take da ita kaman yanda innanta kainana take mata,tana cin abinci mai karin kumarin jiki sosai saidai kuma yanzu jin jikinnata take kaman ba nata ba yanzu,saidai dauriya da kawai takeyi,ga girman cikin ko yaushe karawa yakeyi kaman wanda take shirin haihuwa watan gobe.
Yauma a zaune take gari yafara duhu tana cin kayan marmari a filin tsakar gidan suna hira itada khaleesah,sallamar mutum sukaji batare da sun shirya ba,da sauri fahreeyah ta daga idonta suka hada ido da wani saurayi duk da duhun da yake wajen hakan bai hanata ganin haskensa ba da kuma kyawunsa.
Khaleesah ce ta amsa masa sallamar cikin kunya kafin tace,
"Yah saheel ka kariso ciki mana"
Gaban fahreeyah ne ya buga jin sunan da khaleesah ta ambata,wanda lokaci daya ya tayar mata da tsohon mikin dayale cikin ranta,tsabar tunanin data shiga batasan lokacin da suka bar wajen ba sai filin wajen kawai dlta gani.
Da tunanin mutumin fahreeyah ta kwanta aranta da niyyar gobe zata tambayi khaleesah.
Washagari kuwa suna zaune sai fahreeyah ta tambayi khaleesah,
"U hmm khaleesah jiya naji kince wa wanda yazo jiya yah saheel,shine yariman da ake cewa yabar masarautar su?"
"Ehh shine,yabar gidane saboda mai martaba ya gano cewar muna soyayya hakan yasa yayi fushi kuma yaki amincewa da zancen aurenmu,amma babban dalilin barin gidansa saboda sarki ya koremune nida mahaifiyata duk da halaccin da kakanni na da kuma iyayena suka masa amma yazartar hukuncin korarmu daga gidan sarautar,shikansa yarima saheel din bayan sun dawone shida yarima amam ne ya gane muna wannan kasar,tun daga lokacin muka cigaba da soyayya batare da kowa yasani ba"
Sauke ajiyar zuciya fahreeyah tayi sai a yanzu ta gane dalilin barin gida da yarima saheel  yayi,da kuma alakar su khaleesah da inna kainana da kuma gidan sarautar,tohh in saheel bashine wanda nake tunani ba a matsayin mijina to waye? Ta fada a ranta ,can kuma da taga wautar tambayar ta sai tace,
"Kut ta ya ya ma zai kasance har dan sarki watakila yana gidan yana jirana,allah ka nuna min sanda zan koma naga mijina da kuma ummah tah"
" Fahreeyah tunanine me kikeyi haka naga kin tsirawa waje daya ido?"
"Baby komai khaleesah,na gode da kulawarki har ma da labarin da kika bani"
"Zuwa yanzu yakamata ki daina wannan godiyar haka,shima saida ya tambayeni labarinki,kuma yaji tausayinki matuka,karki damu yah saheel yanada mutunci sosai,kuma yayi mamaki dayaji kema sunan mijinki saheel".
Haka rayuwar tacigaba da zuyawa inda cikin fahreeyah yashiga wata na takwas, duk wanda yaganta indai akwai guntun imani a kitjinsa toh sai ya tausaya mata saboda wani irin girma da cikin yayi kaman a daura shi akayi badaga jikinta yake ba,har yakai idan ta zauna sai an daga ta haka wajen zama ma sai an taimaka ta,
Yauma a Zauna suke an jingina kanta da filo khairiyyah da khaleesah suna matsa mata kafafu wanda saida suka sanja daga kalar na mutane tsabar kumbura da sukayi,shiru tayi kaman mai yin bacci tanajin hirar da suke yi tsakanin su khairiyyah da kuma saheel wanda kusan kullum sai yazo hira ai ta wasa da dariya,
"Fahreeyah yadai naji kinyi shiru ko jikinne?"
"Ahah kawai dai innayi magana sosai ne sainaji kaman kirjina yan cikowa"
"Sannu AI king kusa kema ki huta"
Duk hirar yi sukeyi itada khaleesah wanda ta ki yiwa saheel magana wai ita a dole suna fadan soyayya.
A cikin gidan sarautar kuwa abinne ya cakudewa bangare daya,domin nasreemah tasaka yarima amam a gaba saiya saketa saboda ita bazata iya da zama da shiba bayan ba hihuwa zatayi ba indai tana raye dashi.
Abune ya yi girma har yakaisu ga gaban mai martaba,labari aka aika ga masarautar su inda aka aiko wakili akan zancen,ganin fadan bazai yiyuba ne,mai martaba yabata damar komawa gidansu akan sai angyara lamarin tukunna.
Tafiya tayi dakinta ta hada kayanta tsaf kafin tayi sashen uwar tata wato zulaikha.
A zaune tasameta tana shan kayan marmari ,wanda yanzu basai anyi mata iso ba take shiga,
"Lah diyar albarka kice har yabaki takardar zaki tafi kenan....."
"Ahah mai martaba ne yace natafi gida sai an saita lamarin tukunna"
"Wane irin gyara lamari kuma amma kinsan dai ba warke wa zaiyi ba koh?koh haka zaki tsufah ba kiga jininki ba ke?"
"Ahah yanzu dai bari tukun naga abinda zasuyi,dan zance suke nima bazan komaba"
"Yafimiki dai wa zai zauna da juya yana gani"
Sallama tayiwa sarauniya zulaikha koh sashen safeenah bata jeba ta kama hanyar kasarsu da wakilin da aka aiko din.
Duk abinnan da ake yarima saheel bai saniba,saida yaje wajen su khaleesah yakejin abinda yafaru,ba karamin mamaki hakan yabashi ba ,wani tunanine yafado masa arai daya tuna cewar rabon daya saka amam a idonsa tun jiya dasuka hadu a wajen kilisa,tashi yayi bayan ya musu sallama yayi sahsen abokinnasa.
Sallama ya dunga yi amma shiru babu amsa,hakan yasa ya tura kofar yashiga har dakinsa,a kwance ya sameshi yah rufe har kansa da bargo.
Karisawa yayi ya yaye bargon tareda dafa kansa,zafi yaji tamkar garwashi wanda hakan yasakashi ya karisa yaye bargon,kallon kallo suke inda hawaye yafara zuba a idon yarima amam,can kuma sai ya rike kirjinsa yana sunkiyar da kai,
"Saheel kowa yah gujeni akan abinda banida iko akai,matata ta tafi,mutanen gari na nunani akan banda kwayoyin hallita,yanzu nakasa jurewa,a yau nayi kewarta dayawa,nasan da tananan bazata taba gujemin ba,ita din mace ce daya tamkar dubu,itace macen dana saka a raina bayan mahaifiyata saidai narasata saheel"
"Ya isa haka amam koma wacece inshaallah watarana zaka ganta,ka daina saka hakan a ranka sosai,bari naje na kira inna ta duba maka kirjin kar koh wani ciwone yasameka"
"Ahah inaso na fita na zagaya,banson zaman dakinnan haka,inyaso sai mubi ta can din kawai dama na dade bamu gaisa ba "
Cikin dauriya ya fito daga cikin bargon ya dauki wani magani yahsha,kafin kuma ya shiga bandaki,bai wani dade ba yasanja kayansa suka fita da saheel din zuwa sashen inna KAINATA............tohh fahh😄😄

SADY-SAKHNAceh❤❤❤
#comment
#vote
#share
#like

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now