32

163 14 6
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAƘA* 💍👈🏽

*ZULAYHEART RANO*
_Wattapad Username Zulayheartrano89_

       Story
*AYSHA WAZIRI.*

                 Page 32
Bayan daurin aure Yarima ya samu Baba Waziri a kan maganar yana son ya taimaka a bar Nuwaira ta zauna a gidansa dake Bauchi, ba sai an kaita Ningi ba. Da farko Baba Waziri bai amince ba sai da ƙyar bayan Yarima ya tsara shi da daɗin baki sannan ya amince, ya kuma yi masa alƙawarin zai yi wa Hajja cikakken bayani wanda zai gamsar da ita.
  Ba karamin farin ciki Yarima ya yi ba, domin ya san tabbas idan har a ka kai Nuwaira Ningi gidan sarki babu shakka sai ta muzanta, don ya kula kaf gidan babu mai kaunarta sai shi. A haka suka yi sallama.
  Yarima da abokansa suka cigaba da gudanar da harkokin biki.
   A gidan sarki babu wanda ya zo wajen bikin, sai yan daurin aure su Baba Waziri, matan kam ba su zo ba kasanceawar suna na su taron a can Ningi.
*****
  “Haba Baban yara? Maganar gaskiya ni ban ji daɗin wannan hukunci ba, ya ga al'adar mu yau kawai da tsakar rana sai a rusa mana a kan wata can?” Cikin faɗa Hajja take magana ta ma manta da waye take magana, domin yadda zuciyarta ke mugun tafasa da zafin maganar.
  “Ina baki hakuri saboda an yi maki laifi, amma ki sani hakan da aka yi shi ne daidai, ni wallahi ban ga abin tayar da hankali ba.”
  “Hmmm!” Shi ne kawai abin da Hajja ta faɗa cikin zuciyarta kuwa ita kaɗai ta san tanadin da ta yi wa Yarima da matar da ya aura.
   ********
Bayan magriba aka kawo amarya Nuwaira gidan Yarima Hafiz, wacce aka sanyata a part din da ke fuskantar part din Salmah, an zuba kaya sosai masu kyau da tsada, babu shakka daki ya yi kyau sai fatan Allah Ya sa a zauna lafiya. Yan kawo amarya babu wanda ya zauna, shi ya sa a karamin lokaci gidan ya kasance shiru. Bayan yan kawo amarya sun watse ne Yarima ya shigo, da kallo Salmah ta bi shi ganin yadda yake ta wani washe baki, kowa ya kalleshi yasan yana cikin farin ciki.
Sosai Salmah ta yi ƙoƙarin danne duk wani abu da yake damunta, ta taimakawa Yarima ya shirya domin zuwa wajen amarya Nuwaira.
  Fatan alheri take ta yi masa har sai da ta ga ya shiga ɓangaren. Da sauri ta koma ciki ba ta tsaya a falo ba kai tsaye bedroom ta shiga tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya, tana son Yarima tana matuƙar kishin sa, sai dai a yau ta tabbatar Yarima ya zama na su su biyu, abin da ko a mafarki ba ta taɓa kawo shi ba. Haka tai ta kuka har dare ya yi nisa.

Shi kuwa Yarima zuciyarsa wasai ya shiga ɓangaren Nuwaira baki ɗauke da sallama, Nuwaira dake zaune a kujerar falo sai ka ce ba amarya ba, wacce aka sani da zama cikin bedroom kanta lulluɓe da gyale don tsananin kunya, saɓanin ita dake zaune a kujerar falo tana taunar cingam, zuciyarta na tuƙuƙi ganin har lokacin Yarima bai shigo ba, bayan kuma ta ji shigowsar gidan, shi ya sa ta fito falo tana zaman jiransa.
   Jin sallamar sa da sauri ta miƙe ba tare da ta jira komai ba ta je ta rungume Yarima tana faɗin “Barka da shigowa ango.” Wani irin gingiringim ya ji, tun da yake bai taɓa ganin amaryar da ta yi haka ba ko a cikin littafi ba, amma yau ga shi ya gani a wajen matarsa ta aure, take ya tuno lokacin da aka ɗaura auren shi da Salmah, ya tuno yadda yarinyar tai ta yi ko iya daga kai ba ta yi balle ta lalle shi, amma ita wannan don tsabar rashin kunya har tana iya rungumar sa a ranar farko da suka kasance a matsayin miji da mata, lallai ya yarda Nuwaira ba ta da kunya. Amma a fili sai ya yi yake yana faɗin
  “Barka da hutawa amarya.”
  “Barkammu dai, mu je ka yi wanka.”
“A'a yanzu na fito wanka a sasan Salmatyy, don ke dai ki je ki yi sai dauro alwala mu yi sallah.” Yarima ya ba ta amsa yana raba jikinsa da nata. Sororo ta yi tana kallonsa, cikin ranta ita ɗaya ta san tanadin da ta yi wa yarinyar sai ta shayar da ita Maɗaci mai matuƙar ɗaci, sai kuma ta sanya Yarima ya manta da yarinyar, don ta lura komai na shi sai ya sako yarinyar.
  Wankar ta je ta yi sannan ta shirya cikin wasu watsatsun kayan barci ta shafe jikinta da wasu turaruka masu masifar kamshi, ba ta nufi dakin Yarima ba sai kawai ta nufi firij ta dauko wani haɗi wanda kawarta ta kawo mata, sosai ta sha abin ta sannan ta nufi ɗakin.
  Lokacin da ta shiga Yarima ya fito daga toilet kenan, jikinsa sanye da jallabiya ganin Nuwaira cikin shigar dake jikinta take tsigar jikinsa ya tashi yar, da sauri ya nemo nutsuwar sannan ya fara magana  “Kin yi alwala?”
“Ummm.” Ta amsa tana nufa wajen da yake, ba ta jira komai ba ta shige jikinsa kafin ya yi wani yunkuri har ta fara fitar da shi cikin nutsuwar ta da salonta, ga masifafen kamshin turarenta da kuma abin da take yi masa take ya nemi nutsuwar ya rasa har ma bai san lokacin da ya biye mata suka lula wata duniyar ta daban ba, duniyar da ma'aurata kawai ne suka santa a wannan ranar sun sha soyayya, har kamar zuciyar Yarima zai zauce saboda yadda ya ji Nuwaira.
  
Bayan komai ya lafa sai Yarima ya fada tunanin yadda ya samu Nuwaira, take zuciyarsa ya tuna masa da lokacin da ya fara sanin Salmah a matsayin mace a ranar yarinyar har suma sai da ta yi, wanda da kyar aka samu ta farfaɗo, amma bai ga haka daga Nuwaira ba.
  “Oho! Ni dai wallahi na shiga uku da wannan masifa, a ce ranar daren farkon ka da mijinka har sai ya zauna yana wani tunani, kuma tunanin ma ba na kowa ba sai na wancan yarinyar ” Mtsww ta saki tsaki sannan ta nufi wajen da yake ta rungumo shi ta fara shafar sa, ai kuwa ta samu nasara domin take tarkonta ya kama kurciya.
Kwana suka yi aikin abu guda, kamar yadda ita ma Salmah ta kwana kuka da sallah tana addua'r Allah Ya sassauta mata kishi.

Rano!

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now