Page 2

1.8K 104 10
                                    

👉🏽💍 *KYAKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                     ©
     *_ZULAYHEART RANO_*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                   *02*

Shiru Yarima ya yi domin yasan saboda shi Hajja ta fitittike tana wannan fadar, ya rasa dalilin da kullum suke samun matsala da Hajja ta dalilin Salmah, mik'ewa ya yi jiki babu kwari yana faɗin "Allah ya ba Hajja hak'uri ba nufina saɓa maki ba ne." Ko ɗago kai Hajja bata yi ba balle ya saran zata amsa, hasalima hira take yi da ɗan waziri. Fitar sa bai zame ko ina ba sai ɓangare Yawuro, da kannansa ya fara cin karo gaba daya suka fara kwasar gaisuwa, amsa daya yake basu shi ne "lafiya." da irin yanayin da ya shigo yake amsa masu.
    Yawuro dake kishingide ta amsa masa sallamar fuska sake cike da annashuwa ta ce "Barka da shigowa Magajin Sarki takawarka lafiya dan gidan Yawuro da Waziri yi gaggawar faɗa min mai ya batawa Magajin Sarki rai?." Don jin dadi kirarin da Yawuro ta yi masa har bai san lokacin da murmushi ya kubce masa ba, zama ya yi daf da kafanta yana gaidata cikin girmamawa. "Lafiya lau Magajin Sarki fatan an zo lafiya ya hanyar?"
"Hanya Alhamdulillah Yawuro ta." Ya bata amsa cike da ladabi, hira suka shiga yi abin su cikin nishaɗi bayan an cika masa gaba da abin motsa baki, suna cikin hira ne Ya ɗan Waziri ya shigo. Zama ya yi kusa da Yarima yana faɗin "iyye ma ɗan gidan Yawuro yanzu duk wannan alatun kai aka haɗawa?" Yarima bai yi magana ba sai Yawuro da ta yi masa harara tana faɗin "yawwa shugaban masu surutu, kaima zauna ai dama nasan kuna tare ku kun ki girma." Murmushi Yarima ya yi ya ce "Yawuro ai komai ya kusa zuwa karshe fa ke dai yi mana addu'a." "Kullum cikin yinta muke, ka ga Magajin Sarki ka yi azama ku gama kar a rika jiranmu, Allah yasa waccan shagwaɓaɓɓiyar ta gama shiryawa?" Karamin tsaki kawai Yarima ya ja domin gaba daya ya tsani a yi masa maganar meeting din nan. "Yawuro ai yanzu na baro zata shirya mu din ma daga nan can zamu nufa." To sai ku bada himma.
    Sasan Hajja kuwa Salmah na shiga dakin kwananta, a maimakon ta shiga wanka kamar yadda Hajja ta bukata sai  zubewa ta yi akan rantsatsen gadonta tana furta washhhh! Lumshe  dara-daran idonta  ta yi tare da buɗewa a hankali ta sauke su kan katon pic din da ke manne jikin bangon, tsira masa ido ta kamar yau ta fara ganinsa, kaf zuri'ar su bata taɓa ganin mai kyau irin nasa ba domin shi komai na asalin Fulani babu inda ya bar shi. "Sai ta ji tana son karyata wanda suke cewa tana kama da shi don ita ko kadan ba taga ta inda ta yi kama da shi ba duk da ita dimma fara ce, amma tasan  shi kyau shi na musamman ne. Hannunta ta daura saman kirjinta wanda ke bugawa a hankali. A kalla ta share mintina kusan sha biyar a kwance ba tare da ta sani ba, hasalima ta manta da wani maganar meeting.

            *WACECE SALMAH?*

Salmah matashiyar budurwa yar shekaru goma sha shida, fita ce wajen Alhaji Abdulmumin wanda ake kira Waziri da Hajiya Aysha wacce ake kira da Yawuro, Salmah ita ce 'ya daya mace da iyayenta suka haifa, duk yayyinta maza ne, Babanta Abdulmumin kanine a wajen Sarki Abdulkarim Sarkin Ningi, Abdulmumin da Sarki Abdulkarim 'ya'yan wa ne da na kani, Sarki Abdulkarim ya gaji sarauta ne a wajen mahaifinsa wanda ya mutu shekaru talatin baya, a lokacin mahaifin Waziri Abdulmumin shi ne ya yi wa Sarki wancan Waziri, babu jimawa tsakani shima Allah ya yi masa rasuwa, tun kafin rasuwar tsohon Sarki da kansa ya nema ma Abdulkarim da Abdulmumin matan aure 'ya'yan limamin garin wanda suka kasance yaya ne da kanwa. Hauwa'u da Maryam, Sarkin yanzu Abdulkarim shi ya auri Hauwa'u ya yin da Waziri ya auri Maryam, an yi auren babu dadewa Allah ya amshi kwanan Sarki da Waziri, inda bayan rasuwar su aka naɗa Abdulkarim a matsayin Sarki, shi kuma Abdulmumin a matsayin Waziri, sai da suka shekara da yin aure Allah bai basu haihuwa ba, a cikin shekara daya da rabi ne Hajja Chub'ad'o kamar yadda jama'ar gidan suke kiran ta da shi, domin suna ne na girmamawa a al'adar Fulani ta samu ciki karku so kuga murna da farin ciki da wannan zuri'a ta shiga sosai Hajja ta samu kula a wajen ahalin gidan babu ma kamar Yawuro da take ji kamar cikin a jikinta yake, kwanci tashi har Allah yasa ranar haihuwa ta zo inda Allah ya sauki Hajja lafiya ta samu k'aton danta wanda ya dauko Asali da kyau irin na Fulani, ranar suna Yaro ya ci suna *HAFIZ*  wanda ake masa lakabi da YARIMA, gagarumin taro aka yi wanda ya burge kowa, tun da aka haifi Yarima Yawuro ita ke kula da shi komai ita ke masa ita ta fara kiransa da suna magajin Sarki,  wata biyar tsakani Yawuro ta haifi itama da namiji mai suna *AL'AMEEN* a na kiran sa da *DAN WAZIRI* Yarima da ɗan Waziri tare suka taso, Hajja Chub'ad'o tafi kula da dan Waziri fiye da Yarima domin ɗan Waziri akwai sanyin hali da sakin fuska saɓanin Yarima da kullum fuska daure da Yawuro da dan Waziri  kawai yake hirasai ko iyayensa maza. Bayan haihuwar su Yarima Hajja Chub'ad'o ta haifi su Khadijah, Hafsah, Ameena, da Suhaila. Ya yi da Yawuro tai ta  haifan maza Habibu, Umar, da Usman, sai Ummu Salmah karami Aliyu. Tun aka auras da gimbiya Khadijah da Hafsah.
    Tun da aka haifi Salmah Hajja ta ke nuna mata tsananin kauna, domin ita Hajja da kanta ta zabawa Salmah suna ita ke kula da duk lamarinta, tun kafin a yayeta Salmah ta koma bangaren Hajja. Salmah ta samu kyakkyawar tarbiyyar gata bata da kyaliya tana da son jama'a bata ɗauki kanta a wata mai matsayi ba, duk da ta fito cikin gidan sarauta kuma yar gata gaba da baya musamman wajen Hajja da Maimartaba. A wannan shekarar ta kammala secondary School ɗinta Kuma tuni ta yi sauka kuma ta haddace littafai da dama, nutsatsiya ce kuma kyakkyawa mai cike da kwarjini.

A al'adar a gidan sarki maza suke zurfa karatun boka, ya yin da mata iyakar su secondary, shi yasa tun da Salmah ta kammala secondary Bata samu ci gaba da karatu ba.

*******************
       Zaune akan wata kujera irin ta alfarma, kyakkyawan farin tsoho ne mai cike da haiba da kwarjini, gefen sa na dama wani ne mai kama da shi sai dai bambancin shekaru, amma kai da gani kasan yan'uwa ne irin na jini, a gefensa na haggu kuwa Yarima ne da ɗan Waziri su ke zaune, gaba kadan Hajja ce da Yawuro sai sauran yaran dake zaune a babban dakin da ake yin taruka masu muhimmanci, gaba daya ahalin gidan suna cikin dakin idan ka ɗauke mutum ɗaya, duk sun yi shiru suna sauraro daga sarki, Baba Waziri ne ya dubi Ameena ya ce "Ameena ina Salmah ne?" "Baba tana ciki ban san me take yi ba." "Je ki kirata ya zata maida mu shashashai kullum idan za a yi taro ita ce karshen zuwa  sai kace ita ta haifemu ba mune muka haifeta ba?" "A'a Waziri a yi wa Salmah hakuri kasan dai yadda take kila shiryawa take shi yasa." "Shiryawa wane irin shiryawa ne sai yanzu bayan tasan akwai taro?" "Kai waziri ka yi hakuri Salmah dai yarinya ce dole sai ana hakuri da halayyar ta." Wannan magana ta fito ne daga bakin Sarki. Dole kowa ya yi shiru domin Sarki ya rufe bakin maganar, amma fa tabbas Yarima ya cika ya yi tam a ransa ya kudiri sai ya saɓa mata fiye da tunani tun da ta ɓata masu lokaci, haka Yawuro tana jin haushin yadda kullum idan za a yi taro Salmah ke ɓatawa mutane lokaci ga yi babu damar yin magana yanzu sai a hau kareta, saɓanin Hajja da ko a jikinta, sallama ta yi cikin sanyin murya sai mutum ya saurara da kyau sannan zai ji.
    Da sakin fuska Maimartaba ya amsa "Barka da isowa Ummuna Salmah, tsugunawa ta yi tare da gaida kowa sannan ta isa kusa da Hajja ta zauna tana faɗin "Barka da hutawa Hajjata." "Yawwa yar gidan Hajja an fito lafiya?" "Lafiya lau." Ta ba Hajja amsa, tana ci gaba da lura da kallon da suke aika mata da shi ita sam ba ta su take ba shi yasa bata damu ba. "Ya ɗan Waziri ya bude taro da addu'a kamar kullum sannan ɗan Waziri ya fadi makasudin taro, wanda ya yi sanadin buguwar kirjin Salmah da Yarima a lokaci guda..."
     

*Wai me Sarki ya ce ne da har gaban Salmah da Yarima ya fadi? Domin jin amsan sai kun biyo ni.*

*Da gaske fa sunan labarin KYAKKYAWAR ALAK'A, ARADU NA TABBATA LABARIN ZAI MATUKAR BURGEKU, AMMA SAI KUN BINI A HANKALI*

'''TEAM YARIMA
TEAM SALMAH
YAR MUTAN RANO
ZULAYHEART RANO
MOMMAN FAWZAN'''

   *YAR MUTAN RANO CE*✍

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now