31

1.5K 86 33
                                    

👉🏼💍 *KYAKKYAWAR ALAƘA* 💍👈🏼

                  ©
  *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad uarename zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*😅😅😅 Wannan fa Happy Sallah ne gareku masu kaunar wannan labari, ku sani har abada ina sonku, dimbin godiya gareku masu yi min text a WATTPAD da whatsApp, wollah nasan kuna kaunar labarin nan, ku sani har karshen rayuwa ina sonku da kaunar ku, domin ku ku kadai na yi wannan typing, don na faranta maku kamar yadda ku din ma kuke faranta min, i love You fisbilillah*

*Wannan page din sadaukarwa ne ga wattpad fan's*😍😍😍

Bismillahir rahmanir rahim.

*31*

Karfe goma sha biyu su ka isa garin Bauchi, kasancewar babu wani abu da za su ci sai dambun nama da Hajja ta ba su, shi yasa ba ta zauna ba sai ta ba su Zeenatu umarnin su yi masu girki, ita kuma sai ta shiga gyaran gidan, da yake ba wani datti ya yi ba, tun da akan gyara sai dai ba kullum ba, a kankanin lokaci har ta kammala da gyara ko ina fes, sannan ta fara yi wa Khairat wanka ta shiryata, sannan ita din ma ta yi wankar.
Kwalliya ta tsantsara cikin wasu riga da siket yan kanti, kayan sun matukar amsar jikinta, ta bulbula turare a jikinta, da hula wanda ya shiga da kalar kayan ta rufe gashin kanta, daukar Khairat ta yi su ka koma falo, daidai lokacin da su Zeenatu su ka shigo da kulolin abinci.
"Sannunku da ƙoƙari har kun kammala?" Salmah ta yi masu tambayar da kulawa.
"Eh! Mun kammala."
"To ku je ku ci abinci sai ku yi wanka da sallah sai ku huta gaba daya." Salmah ta dire maganar tana zuba jeelof din shinkafa wacce ta ji kayan lambu sai tashin kamshin daɗi take a plet.
Cike da ladabi su ka amsa sannan su ka bar falon.
Hankali kwance ta kammala cin abinci, sai da ta daurayo bakinta kafin ta dawo falon tare da jawo wayarta, ta fara aikawa Yarima da sako.
Lokacin Yarima kam yana zaune akan kujerar da yake hutu a ofishin sa, abin duniya duk ya dame shi, gaba ɗaya Nuwaira ta rikirkita masa lissafi, ya rasa hanyar da zai bi don ya samu sassauci.
Ɗazun da misalin ƙarfe sha biyu lokacin ne Nuwaira ta yi masa kira, ya yi mamaki da ganin video call ta yi masa, haka nan jiki a mace ya dauki wayar, abin da ya fara gani shi ne ya bala'in ba shi mamaki, Nuwaira din ce zaune gabansa cikin wani irin shiga wacce da shi da babu marabar su kadan ne, wani barbaɗaɗar riga ce a jikinta, ko breaz babu balle Pant, sai wani zuro harshe take tana lasan laɓɓanta uwa wata mayya, kirjinta dake a waje ta ci gaba da bankaro masa.
Ai take ya nemi nutsuwarsa ya rasa, ji ya yi mazantakar sa ta motsa, kishin ruwan da yake ji tun bayan tahowarsa Bauchi ta dawo sabuwa dal, bai san lokacin da ya kashe wayar ba gaba ɗaya, kwata-kwata kasa motsi ya yi, sai tashi ya yi ya koma kan kujera.
Alamar shigowar text ya yi a wayarsa, da kamar ba zai duba ba, don ya san babu mai wannan sai Nuwaira, sai kuma ya ji yana muradin son ganin me text din ya kunsa.
Da sauri ya mike zaune bayan ya bude text din, ganin Number din Salmah, hannu na rawa ya soma kiranta.
Ringing biyu ta ɗauka, duk da a waya su ke magana amma ya tabbatar cike da fara'a take magana.
"Ummunah." Yarima ya kira sunanta da wani irin murya.
"Na'am Hamma." Ta bashi amsa da sansanyar muryarta.
"Ina kewar ku ke da Hajjata ina Areef?"
"Mu din ma muna kewarka Hamma, ga Khairat tana bacci, Areef na wajen Hajja."
"Masha Allah! Ina mai cike da farin cikin jin iyalina su na lafiya, Ummunah tun da na baro ku bana cikin jin dadi, a yanzu haka maganar da na ke yi maki ni kaɗai na san halin da nake ciki."
"Ayya Hamma sannu, ka bar tashin hankalin ka haka fa, ka riƙa daurewa da rashin mu."
"Ba zan iya ba Salmah."
"Yanzu dai na san kana office ko? To ina son idan aiki ya yi ma sauki ka koma gida, ka samu ruwa mai dan zafi ka yi wanka da shi, za ka samu sassauci."
"A'a Ummunah ba wannan ne maganin matsala ta ba, maganin matsala ta tana gareki, ke ce kawai za ki iya sama min lafiya."
"Kai dai ka je gida kawai." Ta faɗa tana dariya.
"Shi kenan dama na kammala aiki, sai kuma gobe bari na tafi gidan." Ya faɗa yana miƙewa.
Dariya Salmah ta kyalkyale masa da shi, sannan ta katse wayar.
Mika hannu ta yi tare da ɗaukar Khairat da ta buɗe ido, "Hajjata kin tashi? Zo ki sha kafin bobbo ya shigo." Salmah ta faɗa tana sanya ma Yarinyar nono a baki.
Sam ba ta ji shigowar sa ba, sai kamshin turarensa da ya cika falon, a hankali ta ɗago kai tare da zuba masa ido fuska dauke da murmushi.
Shi kam Yarima matukar mamaki ne ya gama kashe shi a tsaye, har ya sanya ya kasa ƙarasawa cikin falon, har ga Allah bai taɓa tunanin zai shigo ya iske Salmah ba, abin da ya ba shi mamaki shi ne ganin tun da ya shigo harabar gidan ya ga komai ya sauya, bai gama jin mamaki ba sai da ya tunkari hanyar falo ya ganta a buɗe, ga wani daddadar kamshi nafitowa daga falon, har a haka bai yi tunanin Salmah ba ce, don bai kula da motar da ke pake a wajen parking motoci ba.
Da nutsuwarsa ya bude labulen falon, kafin ya yi yunkurin yin sallama sai ko idanuwansa ya sauka kan matarsa Salmah da diyarsa Khairat.
"Hamma tsayuwar fa?" Salmah ta faɗa lokacin da take shiga jikinsa.
"Hmmmm! Ummunah dole na kasa yi komai, wai dama kina gidan nan duk hirar da muke yi?"
"Eh! Mana dama cewa na yi zan baka mamaki."
"Ai kam kin bani."
"Mu je ka yi wanka, ga abinci can ya kammala."
"A'a." Ya faɗa yana makale kafada kamar wani yaro karami.
Ware ido Salmah ta yi ta ce "Why?"
"Ni ke na fi buƙata kafin wanka." Ya faɗa yana shagwabe murya.
"Haba in dai Salmah ce ka samu, ka yi yadda za ka yi da ita." Ta faɗa tana yi masa fari da ido."
Bai iya cewa komai ba, sai kara matseta da ya yi cikin jikinsa, yana mai jin sabon soyayyar ta na ratsa ko ina a jikinsa.
A wannan rana an dirji zallar madarar soyayya tsakanin Yarima da Salmah.

*****

Kwanci tashi babu wuya a wajen mai rai, a yanzu haka bikin Yarima da Nuwaira kwanaki ne suka rage, shirye-shirye kawai suke yi, musamman bangaren ita Nuwaira, wacce kullum take cikin shaye-shayen maganin mata da sauransu.

Kamar yadda al'adar masarautar su Yarima take, to akan Nuwaira ma ba a canza ba, domin kuwa Hajja ta ce ana gama daurin aure dole ne a kai Nuwaira can Ningi, don ganin yanayin zaman.

Ko a fuska Salmah ba ta taɓa nuna wa Yarima wani abu game da batun aurensa ba, abu guda ta rike shi ne addu'a, domin ta san addu'a ba ta fadi kasa banza, kuma ai addu'a shi ne makamin mumini, sannan zuciyarta ba ta taɓa raya mata Yarima zai manta da KYAKKYAWAR ALAƘAR dake tsakanin su ba.

Duk yadda Hajja ta zo Salmah ta dawo gida lokacin auren Yarima amma fir Salmah ta ki, dole Hajja ta barta.

****
Ranar asabar da misalin karfe biyun rana dubban mutane suka shaida daurin auren Yarima Hafiz da Nuwaira.

Lokacin da labarin daurin aure ya riski amarya Nuwaira ba karamin jin dadi ta yi ba, haka Ango Yarima.

Ita kam Salmah da karfin addu'a ta samu bugun zuciyarta ta daidaita, Allah ya sani tana da zazzafar kishi, sai dai ta iya yin ta don danne shi, amma a yau sai da Salmah ta yi hawaye, in da Allah ya rufa mata asiri, babu kowa a gidanta, daga ita sai su Zeenatu.

Toh Salmah Allah ya sanyaya maki.
Shin me kuke ganin zai je ya dawo?
Da wanne shiri amarya za ta shiga gidan ango?
Duk sai kun biyoni a hankali don jin yadda za ta ka ya, ni ce dai taku har kullum yar Mutan Rano.

VOTE
Comments
& Share.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now