Page 5

1.2K 94 1
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                    ©
              *_ZULAYHEART RANO_*

*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

Addu'sr ku kadai nake bukata daga bakunan ku masu albarka, akan Allah ya biya min bukatuna na Alhairi , da sauran Musulmai baki daya.

Wannan page din sadaukarwa ne ga duk wani mai son littafin KYAKKYAWAR ALAK'A, kyauta na baku ku yi yadda za ki in kun ga dama ku ce kar kowa ya karanta sai ku dai, domin saboda ku kadai nake typing.

                       *05*

Bai jira jin amsar da Hajja zata ba shi ba ya yi gaba, girgiza kai Hajja ta yi cikin zallar takaicin halin Yarima, a tsanaki Salmah ta mike tana faɗin "Hajjata yanzu zan dawo." "A dawo lafiya yar albarka." Babu kowa cikin falon sai shi kadai a hakimce, dan nesa da shi ta zauna a kasa tana faɗin "Hamma gani." Shiru ya yi na kusan mintina uku sannan ya dube ta sai kuma ya dauke kai ya ce "ki rubuta min duk abin da kike buk'ata domin gobe zan tafi. Rasa abin da zai faɗa mata ya yi shi ne ya fake da ce mata haka.
      "Hamma ni fa bana buk'atar komai." Cikin tattausan lafazi ta yi maganar. "Ke ni kike fadawa haka? Umarni ne ba shawara ba don haka ki rubuto zuwa gobe idan ba haka ba ranki zai mugun ɓaci." Da masifa ya ke maganar, inda Allah ya taimaka mata babu kowa a falon daga ita sai shi "To Hamma." Cikin ladabi ta amsa. Shiru ya ci gaba da ratsa falon daga karshe ya mik'e ba tare da ya ce mata kala ba ya yi wucewar sa, girgiza kai ta yi cikin zallar tausayin kanta domin kuwa tasan tabbas ita ɗin abin tausayi ce "Allah ka karkato da hankalin Hamma ya fahimci KYAKKYAWAR ALAK'AR da iyayenmu ke son haɗawa." A fili ta yi furucin bayan ta fita daga ɓangaren Yawuro.
      Da ta koma ciki bata tsaya jiran komai ba ta shige bedroom, wanka ta yi sannan ta sanya kaya marasa nauyi  fita ta yi falo bata tsaya ko ina ba sai wajen cin abinci, don ba karya yunwa take ji sosai abinci ta diba sannan ta isa kan kujera, tana cin abinci tana jiyo hirar Hamma ɗan Waziri da Adda Ameena a tsanake, ji ta yi sun yi matukar birgeta don su ta kula suna son juna "ina ma a ce ni da Hamma Yarima ne muke zaune haka? Wallahi da sai na ce a duniya babu macen da ta kaini sa'a, Allah ka karkato da hankalin Hamma ya fahimci KYAKKYAWAR ALAK'AR da zai shiga tsakanin mu." Abincin da take ci ne ta aje don sai kawai ta ji ya fita kanta bata jin ci, bedroom din Hajja Chub'ad'o ta shiga da sallama.
     "Ummuna ashe kin dawo?" "Na dawo tun ɗazun har na yi wanka na ci abinci." "Iyye! Shi ne kika barni ni daya babu abokin hira." Murmushi ta yi har sai da kumatunta ya lotsa ta ce "ai Hajja gani duk da dai bacci nake ji wallahi na gaji sosai." "To kin ji fa ina maganar fira? Je ki kwanta Allah ya bamu Alhairi kin ji yar Hajja." "To Hajjata sai da safe." Salmah ta amsa tana mik'ewa tsaye ta. "Allah ya bamu Alhairi kar dai a manta da addu'a." "Ba zan manta ba Hajja." Salmah na gama fadar haka ta wuce.
    Washe gari da misalin karfe sha daya Hamma Yarima ya bar gari bayan ya tanadar wa Salmah duk abin da ta rubuta, haka da Yarima ya yi sosai ya faranta ran Hajja sai albarka take sanyawa Yarima, bayan tafiyar Yarima Salmah shiryawa ta yi ta nufi wajen kawayen ta suka kwashi hira yau da yake ta samu sake har da rakasu dibar ruwa ta yi. A hanyar su ta dawowa suna tafe suna Asiya ta dubi Salmah ta ce "Salmah Allah ina tausaya maki Auren Yarima." "Me yasa kika ce haka?" Yahanasu ta yi saurin jefa wa Asiya tambaya. "Haba yahanasu har sai kin tambayeni dalili? Kema kin san halin Yarima, koma dai na ce kusan kowa a garin nan ya san halinsa sam ba ya da sakin fuska kullum cikin hade rai." "Tab sannu Asiya ai kam bana jin idan Yarima ya auri Salmah zai ci gaba da wannan halin, karki manta duk girman kan namiji matukar ya shiga hannun mace sauke komai yake yi ko da kuwa ba ya sonta, balle Yarima yana son Salmah Allah ki bashi kwanaki kaɗan tsaf zata gyara masa zama." "Tom ina fatan haka ta kasance domin kuwa abin na Yarima tsoro yake bani." Salmah dake gefensu murmushi kawai ta yi ta ma kasa furta komai, sai fadawa tunanin halin Yarima musamman a wannan karon, kusan ya rage kashi hamsin cikin dari na muguntar da yake mata, ba wai ta ce  yana sonta bane a'a tafi jin dadin zuwanshi na wannan karon fiye da ko wanne zuwa da yake yi. "Ku yi min addu'a kawai shi kadai ne zai amfane Ni." A haka suka kusa zuwa kofar gidan su Salmah, sallama ta yi masu zata shiga kenan suka yi karo da Aliyu zai fito "Adda Salmah ina kika je Hajja tana neman ki fa." "Rafi na raka su Yahanasu." Ta ba shi amsa tana ci gaba da tafiya, bata haɗu da kowa ba har ta shiga da sallama.
    Adda Ameena kawai ke zaune a falon tana cin 'ya'yan itatuwa "sannu da hutawa." "Yawwa." Shi ne amsar da Ameena ta ba Salmah tana ci gaba da abin da take yi, tumtum ta jawo ta kishingide domin ta gaji idonta har wani lumshewa suke "hala daga rafi kike?" Adda Ameena ta jefa wa Salmah tambaya. "Wallahi Adda daga can nake duk na gaji ina Hajja?" "Ai sai ki yi ta yi kullum ana yi maki maganar zuwa rafi amma baki ji sai ki yi." "Allah ina jin dadin zuwa ne wajen na sanyani nishaɗi." "Hmmmm! Daga haka Ameena bata kuma magana ba, ita ma Salmah gyara kwanciya ta yi, Hajja ce ta shigo falon tana faɗin "wai Salmatyy ina kika shiga tun ɗazun?" "Rafi na raka su Yahanasu Hajja na dawo a gajiye bacci nake ji." "Ai Gara ki kwanta ki huta." To Salmah ta amsa sannan ta fara bacci.

****

Kwanci tashi asarar mai rai, kwanaki suna komawa makonni, yayin da makonni ke komawa watanni, yau dai saura kwana huɗu biki tuni har an fara shirye-shirye, tuni Yarima ya iso haka gidan ke amsan bakuna ta ko ina, yan'uwa da abokan arziki ma ba a barsu a baya ba. Sosai amare ke shan gyara a wajen Yawuro, bangaren angwaye kuwa tuni suka kammala da gyara inda za su a jiye matansu, domin dai a cikin gidan za su fara zama, gefe Salmah ya yi kyau sosai babban falo ne da bedroom guda biyu ko wannensu dauke da toilet, an shirya su tsaf da kayan daki.
      Yau ta kama Alhamis ce kuma ranar ne za a yi rufi kamar yadda al'adar su take, duk wani abu da za a yi rufi da shi Yawuro ta kawo komai da ake bukata, irin silipas, lalle, sabulun wanka da turare, a al'adar su idan har aka yi rufi babu mai kuma ganin amarya sai amintattun kawaye, sai k'anwar uwa ko k'anwar uba, su ne zasu sanya ma amarya lalle wanda ake kwaɓawa da turare sosai kuma kwana da lallen amarya ke yi, da misalin karfe takwas bayan sallar issha aka sanyawa amare lalle kamar yadda al'adun su yake. An sanya lafiya cikin kwanciyar hankali, washegarin da misalin karfe biyu dubban mutane suka shaida daurin aure YARIMA HAFIZ DA UMMU SALMAH, HAKA KUMA AL'AMEEN DAN WAZIRI DA AMEENA, daurin auren da ya bar tarihi a garin Ningi Maimartaba da Baba Waziri sai washe baki suke cike da murna yau sun auras da 'ya'yansu, bayan gama daurin aure  aka dafa ruwan zafi da turare da lalle aka yi wa amare wanka sannan aka dauke su daga dakin rufi aka kaisu dakin Hajja.

Lafiyayyen fura da nono da soyayyen naman shanu aka yi ta rabawa jama'a, mahalarta bikin, sosai Yarima ya sake cikin jama'a ana ta harkar arziki.

Assalamu Alaikum fatan kuna jin dadin wannan labari? Domin jin dadin ku shi ne nawa, yanzu muka fara don daga yau aka fara shiga cikin labarin sosai fatan za ku ci gaba da bibiyar wannan labari? Kar ku gajiya comment dinku nafi so fiye da komai.

Ni ce taku har kullum Zulayheart Rano

Vote me
Comment &
Shere on wattpad.

KYAKKYAWAR ALAK'ATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang