Page 21

827 46 1
                                    

*KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* _P.m.l_

                        ©
    *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

A yi hakurin rashin ganina kwana biyu hakan ya faru ne sanadin lalacewar wayata, yanzu din ma aron wayar na yi wajen sister na na yi maku typing domin jin dadin ku, idan komai ya daidaita zaku ci gaba da juna, duk da gobe ma zan yi kokarin  ganin na yi maku typing.

Zulaiha Haruna Rano tana yi maku fatan Alhairi😍😍😍

                        *21*
Yif! Suka ga Yarima ya faɗo falon ko sallama bai yi ba, sai cewa ya yi "A wani hali Ummuna take?"  "Barka da zuwa Magajin sarki." Jakadiya ce ta yi furucin tana tattaro duk wata nutsuwa nata. Bai amsa ba don ba shi ne abin da yake son ji ba, sai tura kai bedroom din Hajja ya yi don yasan tabbas Salmah na ciki "Kai ina zaka shiga nan?" Hajja ta jefa masa tambaya. Har lau dai ya kasa magana domin ba a cikin nutsuwa yake ba babban burinsa shi ne yaga a wani hali Salmah ke ciki, don haka sai kawai ya shige ciki a rikice ya karasa inda take.
   Rungumeta jikinsa ya yi ji yake kamar ciwon ya dawo jikinsa, musamman yadda ya ga ta galabaita "Sannu Ummuna." Da raunananniyar murya ya yi furucin. Girgiza kai Salmah ta yi cikin azaba don ita daya tasan abinda take ji, kyakkyawar riko Yarima ya yi mata yana mata addu'a, gefe Dr ya koma yana kallon ikon Allah. "Please Dr ɗan bamu waje." Yarima ya yi furucin fuska a hade. Domin dai Yarima yana da mugun kishi, da yana da yadda zai yi ko kumbar Salmah babu wanda zai gani. Nannauyan numfashi Salmah ta sauke tare da damke Yarima ta furta "Ya Allah!" Ta gama furucin daidai da fitowar kan jariri, hamdala Yarima ya yi da kansa ya karasa ciro kan jariri, katon Yaro lafiyayye tubarkallah.
   Su jakadiya suna waje sun yi tsuru tun da suka ga Dr ya fito, cike suke da tunani yadda Yarima ya kori Dr kamar shi din ma Dr ne, haushi da takaici kamar su kashe Hajja, da tana da halin shiga inda Salmah take da sai ta kori Yarima, don yau taga sabon salo wai *Kiran sallah da usur* tun a tarihin gidan bata taɓa ganin wanda matarsa ke nakuda yake shiga ba. Kukan jariri ya sanya jakadiya da Dr saurin shiga dakin, mika masu Yaron Yarima ya yi ya maida hankali kan Salmah dake maida numfashi.
    "Sannu Ummuna." Gyada kai kawai ta yi. Jakadiya ce ta amshi Yaron tana goge masa jiki, sam bakinta yaki rufuwa ta ce "Lallai Yaron nan wato jiran ubansa yake shi yasa tun jiya ake ta fama, amma yanzu da zuwan ka har ya fito." Murmushi kawai Yarima ya yi ba tare da ya ce komai ba,  fita jakadiya ta yi da Yaron  ta bar Dr yana kara duba Salmah, kun dai san yadda ake kaunar Salmah a gidan sarki ko? To haka da aka fita da jariri farin ciki da murna kowa ke yi, musamman ma Hajja da Maimartaba sun kasa ɓoye murna da farin cikin su. Kowa sai ɗaukar Yaron yake yana santi to Yarone tubarkallah! Ciki kam Dr na gama duba Salmah ya yi wa Yarima sallama don a lokacin bacci ya kwashe Salmah.
      Tuni su Zaituna suka tsaftace wajen babu mai cewa an haihu, sai kamshin turare kawai dakin ke yi, bayan Dr ya gama duba Salmah sallama ya yi wa Yarima sannan ya fita, shi ma Yarima bai jima ba ya fita domin bacci sosai take, ko da ya fita falo bai ko kalli inda suke ba ya fice, su din ma basu kula da fitarsa ba don suna can suna murnar haihuwar da ganin Yaro, Hajja ce kadai ta kula don haka tashi ta yi ta shiga dakin kwance ta samu Salmah tana bacci, murmushi ta yi ta shafi fuskarta tana tuna lokacin da ta fara ɗaukar Salmah a hannunta, yau ita ce ta haifi ɗa, lallai Allah shi ne abin godiya.
      Jakadiya ce ta yi sallama tana dauke da Yaron, kwantar da shi ta yi sannan ta haɗa ruwan wanka tas ta wanke Yaron ta shirya shi tsaf cikin tattausan kayan sanyi ta feshe shi da turare mai kamshi wanda Maimartaba ya aiko da shi. Har a lokacin Salmah bacci take yi, don haka sai jakadiya ta ɗauki jaririn ta nufi wajen su Maimartaba da Baba Waziri, fuskar Maimartaba taki boyuwa da farin ciki babu lokacin da ya ɗauki jaririn, addu'oi na neman tsari ya ke tofe Yaron da shi sannan ya ɗauki dabino da zamzam wanda tuni ya tanajesu ya tauna ya sanyawa Yaron abaki tare da ruwan zamzam, huɗuba ya yi masa da sunan Baba Waziri wato " *Abdulmumin* (wannan shi ne al'adar gidan sarauta, matukar babban Yaron sarki ya haihu to sarki da kansa zai sanya masa suna.) Bayan ya gama ne ya mikawa Baba Waziri shi ma ya tofesa da addu'oi daga nan jakadiya ta koma da shi ɓangaren Hajja, a lokacin Salmah ta tashi daga bacci har Hajja ta haɗa mata shayi.
     Tana gama shan shayin ta shiga wanka da taimakon jakadiya ta gama wankan, sannan ta fito kimtsa kanta ta yi har a lokacin ko kalar Yaron da ta haifa bata sani ba, don Salmah fa akwai kunya tana gama kimtsa jikinta ta kwanta, da sauri jakadiya ta ce "Uwardakina ya zaki kwanta har yanzu fa baki ba shi ya sha ba?" "Kai jakadiya don Allah, wallahi ni kam bacci nake son yi." "Bacci? Aiko dai ki fara ba shi kafin ki kwanta don ma Yaron nada hakuri ko kuka bai yi ba har yanzu." Ta dire maganar tana daura mata Yaron a cinya. Gaban Salmah ne ya fadi ganin Yaron tubarkallah da shi mai tsananin kama da Yarima, ɗauke kai gefe ta yi bata son su Hajja su fahimci tana kallonsa "Bismillahir Rahmanir Rahim." Salmah ta furta tana sanya masa nono a baki. Murmushi jakadiya ta yi tana yaba hankali irin na Salmah, a hankali Yaron yake sha idonsa tar a fuskar Salmah, murmushin farin ciki ya kasa barin fuskarta.
     Tun da Yarima ya fita bai dawo ɓangaren ba sai da karfe biyar, Salmah tana zaune plet ne a hannunta mai dauke da farfesun naman kai, bayan ta gama cin tuwon dawa da man shanu wanda ta bade da yajin daddawa, Hajja ce ta sanya aka yi mata wannan hadi, kuma sosai ta ji dadin hadin, sallamar Yarima ce ta sanya ta daga kai tare da amsawa, bai zauna ba sai da ya ɗauki jaririn yana fadin "Sannu Ummuna."  "Yawwa." Ta amsa tana kallonsu domin sun burgeta. "Ya kike kallonmu?" Ya yi tambayar bayan ya zauna.
     "Gani na yi kun yi kyau sosai." "Allah ko? Ai ma ban iya ɗaukan Yaro ba fa." "Amma ga yi ka ɗauki wannan tsaf kamar ka iya." Murmushi ya yi yana ciro wayarsa da ga aljihu ya fara ɗaukar Yaron pic, sosai ya dauke su photo sun yi matukar kyau, sannan ya kwantar da Yaron ya jawo ta jikinsa tare da rungumeta yana shafata "Yau kin bani farin ciki Ummuna tun da kika haifa min kyakkyawar Yaro Allah ya baki lafiya." "Amin Hamma wai fada maka aka yi ne?" Ta gama tambayar tana kallonsa. "A'a Ummuna haka kawai jikina ya bani baki da lafiya, shi ne musabbabin zuwa na, ashe kuwa baki da lafiyar maimakon ki fada min."
    "Saboda aiki ya sanya ba a fada maka ba don hankalinka yana iya tashi." Murmushi ya yi yana shafa fuskarta ya ce "Da yake Yaron yafi son ubansa ya fara kallonsa ai sai ya ki fitowa, next time Kar a Kara yi min haka na fi son na tari Yarona da kaina." "An daina Hamma." Salmah ta ba shi amsa. Ya yin da Yarima ya kara ma'kaleta sam ya manta jego take yi, muryar Hajja suka ji tana rangaɗa salati da sauri Salmah ta janye jikinta cike da kunyar yadda ta gansu da Yarima "Tashi ka fita." Hajja ta dire maganar fuska daure tana nuna masa hanya. Ta shi ya yi jiki babu kwari ya bar sasan.

Vote me
Comment
& Shere on my wattpad.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now