Page 25

847 42 1
                                    

👉🏼💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A*💍👈🏼

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S* _P.M.L_

©
*ZULAYHEART RANO*
*My wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*25*

"Eh Hajja."

"Kuma har na wata nawa?" Hajja ta kara jefa mata tambaya.

"Yana wata na biyar ne." A hankali Salmah ta bata amsa.

"Kuma shine kike ba Areef nono, ko kin daina bashi ne?"

"A'a Wallahi Hajja Hamma ne ya hana a yaye shi."

"Madallah! Daga yau kam ya fita a nono, shi ma ya girma sai ki ji da abin da ke gabanki."

Gyada kai Salmah ta yi cikin gamsuwa da bayanin Hajja, sannan suka ci gaba da hiransu har aka kira yi sallah, bayan sun yi sallar ne suka ci gaba da hira har lokacin da Yarima suka shigo tare da Hamma ɗan Waziri, gaisawa suka yi da Hajja sannan suka fara hira, Yarima kam babu kunya ya ce wa Salmah ta tashi su tafi bangarensu.

"Kai Hamma tun yanzu?" Salmah ta yi maganar tana turo baki.

"Eh! Ina Areef ne? Ban gansa ba tunda na shigo?"

"Yana ɓangaren Maimartaba, ai kuma Areef ya riga ya dawo nan da zama." Hajja ta bashi amsa.

Tsaf Yarima ya gane nufin Hajja amma sai ya ce "kar ya yi kuka da dare fa."

"To shugaban marasa kunya, an yaye shi tunda so kake na yi maka dalla-dalla."

"Allah ya baki hakuri Hajja sai da safe." Ya dire maganar yana tafiya.

************

"Amma Hamma maimakon ka barni na kwana a wajen Hajja shine ka hana." Salmah ke wannan magana bayan sun fita bangaren Hajja.

"Ki kwana bangaren Hajja? Sai kuma Ni ki barni da wa?" Ya jefa mata tambayar tare da tsare ta da ido."

"Ka kwana kai ɗaya." Ta bashi amsa lokacin da suka shiga bangaren su.

Hmmmm kawai Yarima ya fada, tare da zama akan kujera. "Bari na haɗa maka ruwan wanka."

"Yawwa Ummuna diyar kirki, kamar kin san ina da bukata." Yarima ya gama maganar yana lumshe ido alamar gajiya tsantsa.
Bata fi minti uku ba ta dawo, tana sanar masa ta gama tare suka koma haka kuma tare suka yi wankan, suna yi suna soyayyar su suna fitowa shirin bacci suka yi, duk da Salmah a gajiye take haka nan ta biye wa Yarima har ya gamsu sannan bacci ya ɗauke su cike da farin ciki.

Washegari basu bar bangaren su ba sai kusan goma, don da suka yi sallar asuba bacci suka koma sai tara da mintina suka tashi, wanka suka kuma yi sannan suka shirya sai ɓangaren Hajja, da sallama suka shiga bangaren babu kowa sai Areef da keta wasansa, da sauri Salmah ta isa wajensa tare da daukarsa tana faɗin

"Barka da safiya Bobbon Nenne." Ta gama maganar tana yi masa kiss a kumatu.

Dariya kawai ya ke yi, sannan ya zame ya nufi Yarima tare da rungume shi, shima cikin zallar so da kauna ya manna shi a jikinsa, a haka Hajja ta fito ta samesu

Har suna hada baki wajen gaisar da Hajja, fuska sake ta amsa tana tambayar ya suka kwana "Lafiya lau muka kwana Hajja." Suka bata amsa.

"Wai kam Hajja Areef bai yi kuka ba?" Yarima ya yi tambayar yana ɗaukar Yaron.

"Ya yi amma kaɗan, kasan dole dama sai ya yi kuka domin an raba shi da abincin sa, sannan ya ki ya yi bacci sai da na kira Zaituna ta goya shi kana ya yi bacci, yanzu kam da safe break din sa biyu, tun shida aka hada masa tea ya sha, kuma da Maimartaba zai yi break tare suka yi."

KYAKKYAWAR ALAK'ADonde viven las historias. Descúbrelo ahora