39

198 15 6
                                    

         KYAKKYAWAR ALAƘA

      39
Zulayheartrano89

  “Don Allah Hajja ki yi haƙuri.” Yarima ya fada baya da niyyar tashi.
Hannun Salmah Hajja ta ja suka bar masa falon. Mtswwww Nuwaira ta saki tsaki mai karfi. Da sauri Yarima ya dubeta don abin ya zo masa a bazata, haɗe rai ta yi tare da juyar da kai gefe ta ce “Tun da ba za ta hakura ba dole ne? Malam idan za ka tashi mu tafi gara ma ka tashi mun wuce.” Ta gama maganar tana wani jijjiga jiki. Babu yadda ya iya don baya mata musu a kan duk abin da ta ce, shi ya sa ya bita a baya kamar raƙumi da akala.
  Da safe suna karyawa lokacin tuni Hajja ta sanya Salmah ta gama haɗa duk wasu kaya da za su yi amfani da shi idan sun koma Ningi, Hamma Ɗan Waziri ya dubi Hajja tare da cewa “Ni kam Hajja gani nake kamar ba laifin Yarima ba ne, wancan shedaniyar matar tasa ce ta juyar masa da hankali.”
  “Allah nima Hamma har yanzu bana ganin laifin Bobbon Areef, ai da ba haka yake ba tun da ya yi aure ya zama haka.” Salmah ta faɗa tana ajiye kofin shayin da take sha.
  Sai da Hajja ta nisa da kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta ce “Idan ma asiri ta yi masa koma mene ne ya tarar da halin sa da ace ya riki bautar Allah da gaskiya duk da haka ba same shi ba, kuma ai ba shi ta yi wa ba Salmah ta yi wa a kan ya rika wulakantata, burinta ya biya sai dai wannan karon tun da har na san halin da ake ciki Salmah ta bar wannan gidan, ban yi wa Hafizu baki ba amma na tabbatar da sai ya yi nadama.”
“umm...” Kai ku tashi mu tafi haka na gaji da zaman garin nan haka ba komai a cikinsa sai ɓacin rai. Hajja ta katse masu maganar da suke niyyar yi, dole haka suka tashi bayan Salmah ta kashe duk wani kayan wuta da yake gidan sannan ta rufe bangaren kafin suka kama hanya.
  Motar su Zaituna da kaya daban don Hajja ta ce tare da su za a tafi, su kuma tasu daban.
  Tun da Yarima ya shiga ɓangaren Nuwaira ya kuma mantawa da komai, ya ma manta sun haɗu da Hajja a ɗazun Nuwaira ce kawai a gabansa
  ***
Karfe goma sha biyu a garin Ningi ta yi wa su Salmah, bayan motar ta yi fakin kai tsaye ɓangaren Hajja suka shiga, cike suka samu ɓangaren su Adda Khadijah da sauran yaran Hajja duk suna ɓangaren. Ba karamin jin daɗin ganin Hajja suka yi da Salmah ba, sai da suka yi wanka suka ci abinci da sallah, sannan Salmah ta shiga daki ta fara barci don kwata-kwata a can ba ta wani samun barci kullum cikin tunanin halin da take ciki take yi, daga addu'a sai kuka shi ya kawai ta sanya a gaba, amma yanzu za ta samu sassauci daga damuwar da take ciki.

  Ɗan Waziri ne zaune a gaban Yawuro yana yi mata bayanin abin da yake faruwa da Yarima, hankalinta ya tashi matuƙa da jin wannan labari don haka dole ta yake shawarar haɗuwa da Jakadiya, aikuwa a ƙanƙanin lokaci suka haɗu nan ta zauna ta zazzagewa Jakadiya komai da ake ciki “La'ila Ha Illallahu Muhammadur Rasulullah! Yanzu Yarima ne yake cikin wannan halin ba mu sani ba?” “Ke dai ki bari Jakadiya, yanzu ya kike ganin za a yi?”
  “Akwai yadda za a yi don Allah ba ya hana yadda za a yi, yanzu ba sai anjima ba zan isa ga Malam Liman don mu ji yadda za a yi.” “Haka ne, ki yi kokarin zuwa duk yadda kuka yi ina jiranki.” “Toh jakadiya.” Ta amsa tana fita.
  Jakadiya ba ta dawo sai bayan sallar magriba, a lokacin Yawuro duk ta kosa Jakadiya ta zo don ta ji halin da ake ciki. “Ina jinki Jakadiya Yawuro ta faɗa tana gyara zama.” “Toh Alhamdulillah! Uwardakina an samu nasara, tun da na yi masa bayani ya ce na ba shi lokaci ƙalilan, shi ya sa kika ga ban dawo ba sai yanzu bayan na yi sallah sai na koma, alal hakika Uwardakina Yarima yana cikin wani hali kamar yadda Malam Liman ya sanar mini, sihiri ne mai zafi a jikinsa sannan akwai abubuwa masu yawa da aka burne a cikin gidansa, wanda su ne suka bayar da gudummawa wajen ruguza masa komai na shi, amma ya ce na sanar dake ki ƙwantar da hankalinki zai bayar da magani, sannan zai yi mana addu'o'i mu ma mu cigaba da yi. Tun yau da dare zai fara aiki, amma ya ce dole wasu magungunan da za a riƙa amfani da su a cikin gidan, yanzu uwardakina ya kike gani za yi? Tun da dai Salmah ta baro gidan?”
  “Haka ne amma babu matsala tun da ɗan'uwansa yana free, don haka ina ganin zai iya yin komai, ko da taimakon masu gadin gidan ne.” “Toh shi kenan Uwardakina, goben zan je na amso sai na kawo maki.”
  “Na gode sosai.” Yawuro ta faɗa cikin jin daɗi. Ai kuwa washegari Jakadiya ta fara amso magani, wanda aka haɗa masa na kwana bakwai kenan dai yanzu Ɗan Waziri zai riƙa zuwa Bauchi duk sati.
   Ba a samu matsala ba wajen samun haɗin kai ga masu gadi, domin suma suna cikin wani hali dangane da Yarima, tun da duk abin da yake yi masu yanzu ya daina, ga wulakanci da Nuwaira take yi masu hatta abinci su suke neman abinsu su ci, saɓanin da kafin ya yi aure uwa uba kuma yanzu ba Salmah a gidan.
  Shi ya sa suka amshi aikin tsakaninsu da Allah, har na sati guda ya ƙare Ɗan Waziri ya kuma kawo masu wani tare da ihsanin da ya saba yi masu.
******
Kusan dai yanzu hankalin Salmah a kwance yake, kullum tana tare da yaranta da yan'uwanta da kuma iyayenta, ta yi kiba madaidaci kyawunta ya kara fitowa sosai haka farinta Jikinta ya murje sosai.
  Sai dai ko kaɗan ba ta ji soyayyar Yarima ta raunana ba, tana jin kewarsa musamman kulawar da yake mata, tana kewar gangar jikinsa da soyayyarsa mai tsayawa a rai, lumshe ido ta yi tana sakin murmushi kamar Yarima yana kusa da ita
  “Umhmm! Kina nan kina sana'ar ko?” Ta ji muryar Hajja a kanta.
  Firgigit Salmah ta buɗe ido tana faɗin “A'a Hajja ba abin da nake yi fa, Aliyu ne ya gama bani dariya ya fita.”
  “Aliyu? Wanne Aliyun?” Hajja ta tambaya da mamaki don Aliyu dai yana makaranta, ta san dai tunanin Yarima take yi, shi ne za ta yi mata musu da wai Aliyu
  “Kai Hajja?” Salmah faɗa tana turo baki tare da tashi.

*****
  “Ummuna Salmah! Ummuna Salmah!!” Yarima ya faɗa cikin ƙaraji a firgice yana tashi ya zauna. Nuwaira dake kwance kusa da shi ta yi saurin tashi ta zauna tana kallonsa, zuciyarta cike da mamakin sunan da ta ji yana ambata.
  “Prince lafiya?” Ta tambaya tana dubansa.
  “Lafiya lau nuwaira.” Ya faɗa yana sauka daga kan gadon, kai tsaye falo ya fita bai kuma tsaya a falon ba sai ya fita harabar gidan, direct ƙofar falon Salmah ya nufa. Ya yi matuƙar mamakin jin kofar a kulle ya san Salmah ba gwana ce ta rufe ƙofa ba, sannan a irin bugun da ya kewa ƙofar da a ce da mutum da an buɗe masa, da ya gaji da bugu sai kawai ya koma sasan Nuwaira yana mamakin abin da ya hana Salmah buɗe masa ƙofa, ko fushi ta yi da shi ne shi ya sa ta yanke masa wannan hukuncin? To ai ban kamata ta ga laifinsa ba don shi ma bai san abin da ya dame shi ba kwata-kwata, sai ya ji baya son ganinta ko ya yi niyyar zuwa wajenta sai ya kasa.
  Mafarkin da ya yi ɗazun ya fara dawo masa kamar yanzu yake yinsa, mafarki ya yi wata ta bi Salmah da wata zungureriyar wuƙa za ta caka mata, har ta zo daf da ita ta daga wuƙar za ta caka mata, sai ga shi ya zo aiko da sauri ya je ta hankade matar kuma ya ƙwace wuƙar, juyawar da zai yi sai ya ga Salmah ta faɗi ƙasa a sume shi ne ya kwarma ihu tare da nufarta, bai kai gareta ba ya ja wata mata cikin shiga ta alfarma ta ɗauke Salmah ta tashi sama da ita, a daidai wajen ya farka.
  Jikin shi ya yi sanyi yana fatan Allah Ya sa mafarkin da ya yi kar ya zama gaskiya. Nuwaira dake biye da shi tun lokacin da ya fito har ya gama tsayuwar shi a kofar Salmah, sai da ta ga zai juyo shi ne ta koma dakinta tana dariyar mugunta don ta san tuni Salmah tana gidansu, ita yanzu neman mafita kawai take yi, don dole ta san abin yi alamu sun nuna aikinta yana niyyar warwarewa.
  “Lafiya kuwa kike ta kai kawo?” Yarima ya mata tambaya yana kallonta.
  “Bab babu komai.”
Ɗaga kafaɗa ya yi alamar ko a jikinsa ya ce “Ki haɗa kayanki zuwa da safe za mu tafi Ningi, dama bamu taɓa zuwa dake ba.”
  “Ningi? Me kuma za mu je yi a can?”
“Tambaya kike yi ko neman sani?” A masifance ya bata amsa. Ganin yana neman koma mata asalin Yarima ya sanya ta ja bakinta ta yi shiru, shi ma ganin haka ya sanya ya wuce bedroom dinsa. A lokacin ƙarfe ukun dare bai kwanta ba sai kawai ya shiga toilet ya yo alwala abin da rabonsa da yi har ya manta, sallolin nafilfili ya fara bai daina ba har sai da ya ji an kira sallar asuba, yana gabatar da sallah ya haɗa kayan da zai yi amfani da shi sannan ya fita, kasancewar ba a bedroom ɗaya suka kwana da Nuwaira ba, sai ya nufi na ta zaune ya sameta ta hada kai da gwuiwa tana nazarin yadda za ta yi, dama yanzu suka yi waya da kawarta Rauda har sun gama tsara yadda za su yi, idan gari ya waye za su je wajen wani boka dake kan tsauni.
  “Kin yi sallar asuba?” Firgigit ta farka jin muryar Yarima.
  “Na yi.” Shi ne amsar da ta ba shi, alhalin kuma ba ta yi ba.
  “Ok kin gama haɗa kayan? Don yanzu zan je na yi wa Salmah magana tare za mu tafi.”
Murmushin takaici kawai ta yi ba tare da ta amsa ba.
   Yau ma kamar jiya haka ya gaji da bugu ba tare da an buɗe ba, don haka sai ya nufi wajen masu gadi yana tambayarsu ko ina Salmah ta je, take suka ba shi amsa da “Ranka ya daɗe ai yau kusan sati huɗu kenan da Hajiya mai babban daki ta zo ta tafi da ita.”
  “Hajiya mai babban daki ta zo gidan nan?” Ya yi tambayar da mamaki don ya gane Hajja suke nufi.
  “Eh.” Suka tabbatar masa da haka.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now