Page 19

843 42 0
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

*REAL PURE MOMENT OF LIFE* _P.m.l_

                         ©
     *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                    *19*

"Na roke ki Ummuna ki yi hakuri, ki bar batun nan kar wata matsala ta sameki, domin a wannan yanayin da kike ciki bai kamata ki rika sanya damuwa a zuciyarki ba, ki daina tunanin wata Nuwaira domin babu komai tsakanin mu da ita." Cikin sigar lallashi da kwantar da murya ya gama maganar.
       Salmah bata yi magana ba sai gyara kwanciya ta yi tare juya masa baya, domin bata bukatar wadancan maganganun nasa. "Ba ki ce komai ba Ummuna?" Yarima ya fada yana jawota jikinsa. "Please Hamm..." Bata gama rufe baki ba ya sanya bakinsa cikin nata, duk yadda taso ta kwace abin ya gagara dole ta sakar masa jiki yana yadda yaso da ita, bai barta ba sai da ya mantar da ita wancan maganar. Sakinta ya yi tana mai da numfashi.
       "Fatan kin fahimci magana ta?" Kasacewa komai ta yi don ya gama kashe mata jiki, gyada kai kawai ta yi ido lumshe, murmushi Yarima ya saki tare da shafo fuskarta, yana son sanyin halin Salmatyy domin ita macace mai hakuri da yafiya, kafin mutum ya ga ɓacin ranta da wahala. "Sai na dawo Ummuna." "A dawo lafiya Allah ya tsare." Ta fada tana niyyar tashi. "No! Kwanta ki huta kin ji My princess." Murmushi ta yi tare da daga masa hannu alamar bye.
       Ajiyar zuciya ya saki tare da gyara rigar jikinsa sannan ya fita, da kudirin sai ya nunawa Nuwaira kuskurenta, karfe tara da mintina ya isa office Bai jira komai ba ya fara aikin domin ya samu wasu File a kan teburin sa, sannan ga raguwar na jiya sosai ya yi aiki bai samu kansa ba sai karfe ɗaya, toilet ya shiga ya dauro alwala sannan ya nufi Masar dage wajen, bayan ya idar da sallah ne ya fito yana tafiya wayarsa ta fara kara, murmushi ya saki ganin sunanta ya fito ɓaroɓaro dauka ya yi tare da karawa a kunne "Barka da warhaka My princess." Daga daya bangaren Salmah ta amsa "Barkammu dai Hamma fatan ka wuni lafiya?" "Lafiya lau Ummuna fatan kema haka?" "Alhamdulillah! Ta bashi amsa.
       "Madalla Allah yasa kin ci abinci?" Yarima ya yi tambayar yana bude office. Murmushi mai sauti ta yi ta ce "Na ci Hamma, kaima da fatan haka?"  "Yanzu na dawo daga masallaci zan ci." Ya bata amsa daidai lokacin da idonsa ya shiga cikin nata, wani bugu kirjinsa ya yi har sai ya ji kamar zai faso ya sauka kasa, sam ya manta waya yake da Salmah kalma daya kawai ya iya tunawa ita ce, da Salmah ta ce "Hamma na barka ka ci abinci ban son ka zauna da yunwa." Kara kara wayar ya yi a kunne sai ya ji shiru hakan ya tabbatar masa da ta kashe wayar kenan, cike da ɓacin rai ya kara kallonta zaune ta yi ta sanya shi gaba tare da zuba masa ido kamar zata lashe shi.
      "Wai Nuwaira me ki ke nufi?" Ya yi tambayar cikin masifa. "Haba Prince wai ko da yaushe tsakanin mu sai fada, ka fahimceni don na ce ina sonka bai kamata kana min irin haka ba." Hararar da ya aika mata shi ya yi sanadin makalewar sauran maganar. "Ke ki saurareni da kyau ni nan Yarima Hafiz bani da ra'ayin yin nata biyu, tun wancan time din na fada maki amma kin ki ji ko? Wallahi zan yi maki walak'anci menene na kirana ɗazun da safe ina tare da matata? Na taba ce maki ina sonki? Tun wuri ki kama kanki da ni." Magana yake amma gaba daya hankalinsa na ga abin da yake cikin computer, sai dai duk wanda ya gansa a haka zai tabbatar babu wasa cikin lamarinsa. Shiru Nuwaira ta yi tana kasa yin magana domin gaba daya ta firgita daga Yarima, duk da irin soyayyar da take yi masa zata iya hakuri da shi, don zuciyarta bata iya jurewa cin mutunci.
    "Ka yi hakuri Prince ba zan kara kiranka ba, ka sani soyayyar da ita zan mutu domin kaine mutum na farko da na taba jin ina so shi yasa naso mu kulla KYAKKYAWAR ALAK'A amma tun da haka bai samu ba ina yi maka fatan Alhairi." Tana dire maganar ta ɗauki hand bag ɗinta ta fita, da kallo ya bita ko kaɗan bata bashi tausayi ba, don idan ya barta shi zata jawa bala'i yana zaman lafiya da salmar shi.

          *WACECE NUWAIRA?*
Asalin sunanta Nuwaira Mustapha Umar, Alhaji Mustapha Umar haifaffen garin Katsina ne sana'arsa ce ta kawo shi garin Bauchi, Nuwaira ita ce 'ya ta biyu wajen iyayenta yar gata ce gaba da baya, musamman wajen Hajiya Mariya da ta kasance mahaifiyarta, budurwa ce mai kimanin shekaru ashirin, ta yi pramary da secondary duk a BAUCHI, yanzu haka tana shekarar karshe a jami'a, sun fara haduwa da Yarima ne a bikin wata kawarta, tun da ta gan shi ta ji a duniya babu wanda take so da kauna sai shi, shi kuma tun nan wajen ya nuna mata yana da mayar da zai aura, a lokacin an tsayar masa da Salmah matsayin mata, ko da rana daya bai taba furta yana sonta ba amma ita ko da yaushe cikin bibiyar sa take. Wannan shi ne tsakanin Yarima da Nuwaira. Yana ganin Nuwaira ta fita ya rufe laptop din don sai ya ji ya tsani aikin gaba daya, kewar Salmah ya dirar masa don haka bai jira komai ba sai ya dauki key din motarsa ya nufi gida.
          Fitowar ta daga wanka kenan tana daure da towel a kirjinta gani ta yi an turo kofar da sauri ta kalli wajen, Yarima ta gani tsaye ya kafeta da da idanunsa masu saukar mata da kasala, a hankali ta taka har wajen da yake tsaye jikinsa ta shige tana fadin "Dawowa da rana Hamma?" "Eh Ummuna." Ya bata amsa yana taɓa sumar kanta. "Ai time din tashi bai yi ba fa meka dawo yi?" "Nazo jika maki sumar Nan ne naga kin yi wanka baki wanketa ba." Yana magana yana kara shigarta jikinsa, murmushi ta yi tare da zame jikinta daga nashi ta nufi gaban mirror tana fadin "Bara na gama kwalliya sai mu yi magana." Kafin ta gama rufe baki har Yarima ya yi sama da ita, a gado ya sauketa tare da rungumata ya ce "wani maganar kwalliya kuma ke da zaki sake wanka, bari har na samu nutsuwa sai mu yi tare."
        "Kai Hamma wai baka gajiya ne?" "Ta ya zan gaji da ba furena ruwa? Kin ga yanzu bebyn jikinki yana bukatar irin wannan abin don yana kara masu kwari, shi yasa kika ga bana wasa." "Babu wani nan kai dai ka cika wayau." Ta dire tana turo baki, murmushi kawai Yarima ya yi sannan ya shiga aikinsa, bai saurara mata ba sai da nutsuwa ta zo masa, da kansa ya yi mata wanka sai kukan shagwaba take masa shi kuma yana biye mata, bayan sun gama shiryawa sai suka nufi dining room suna cin abinci suna soyayya, a ranar Yarima bai koma office ba soyayya suka sha abinsu.
       Rayuwa mai dadi suke shi da Salmah, yanzu baya da wata matsala tun da ya yi ma Nuwaira kashe din karshe bata kuma zuwa office ɗinsa ba balle ta kira wayarsa, a kwana a tashi babu wuya wajen mai rai yanzu cikin Salmah ya shiga wata takwas, wata rana suna kwance bayan sun dirji juna Salmah tana kwance kanta na saman cinyarsa wayarsa ta yi kara yana dubawa yaga Number din Hajja Chub'ad'o.
        Da sauri ya dauka tare da tattaro nutsuwa, sallama ya yi baya sun gaisa Hajja ta ce "Ina Salmatyy?" "Gata nan Hajja." Yarima ya bata amsa yana mikawa Salmah wayar, amsa Salmah ta yi suka gaisa da Hajja tana tambayar ta ya jikin ba dai matsalar komai ko, eh shi ne amsar da Salmah ta ba Hajja sannan ta mikawa Yarima, suka ci gaba da magana inda ta ce "Kana jina ko? Ka kawo Salmah gida gobe don kasan dai al'ada ko?"  Dam! Gaban Yarima ya fadi da maganar Hajja, suna tsaka da soyayyar su za a raba su.

Vote me
Comments
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now