Page 12

1.2K 66 3
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                              ©   
              *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                      *12*
Murmushi ya yi mai cike da nishaɗi, babu shakka maganar Salmah gaskiya ne, ya yarda domin shi aka yota haka kuma domin ta aka yi shi, ada bai taɓa kawo zasu yi zama na jin dadi irin haka da Salmah ba, amma cikin lokaci kalilan sai Allah ya juya lamarinsa, tasbihi ya yi ga Allah cikin nuna masa zallar farin cikin da yake ciki. "Na yarda da batun ki Ummuna, ki yi alkawari komai tsanani baza ki rabu dani ba, ni kuma na ina mai tabbatar maki da har abada KYAKKYAWAR ALAK'AR mu ba zai taɓa canza suna ba." "Na yi ma wannan alkawarin Hamma." "Than..." Bata bari ya gama rufe baki ba ta jefa bakinta cikin nasa.
      Wani irin salo take yi da harshen shi, tana juya masa ido, mamakin Salmah ya hana Yarima kwakkwaran motsi. Sai da ta gama kashe masa jiki sannan ta ja hannunsa yana bin ta kamar rakumi da alaka, cikin toilet ta kaishi sakale Yarima ya yi yana kallon Salmah, ruwa ta haɗa masu yana tsaye ta gama cire kayan dake jikinsa sannan ta ce "Hamma ka yi wanka." Ajiyar zuciya ya sauke ya dauketa sai cikin ruwan wankan, kafin su yi wanka sai da suka gama tsotse-tsotse da lashe-lashe, sannan suka fita kaya mara nauyi suka sanya, sannan suka nufi wajen cin abinci a can dinma ana yi ana soyewa har aka gama. YARIMA fa yau Salmah ta gama rikita shi  da salonta, domin da kyar ya iya fita sallar la'asar shi ma yana idarwa ya koma ciki. Soyayya kawai suke sha, alla-alla yake dare ya yi ya murji Salmah, aiko ana idar da isha'i suka duk'ufa domin dukansu sun yi kewar juna, a wannan dare basu samu rintsawa ba sai bayan sun yi asbah, sosai Salmah ta gaji biye masa kawai take, ko da suka yi asbah lallaɓata ya yi ya kuma yi a takaice dai sai karfe shida suka kwanta bacci, ba su farka ba sai shabiyu saura mintina, shima yunwa ce ta farkarkar da su, wanka suka yi sannan suka nufi bangaren Hajja.
   Da sallama suka shiga cikin falon, Hajja dake zaune bayi guda biyu suna matsa mata kafafu ta amsa cike da fara'a, zubewa Salmah ta yi jikinta tana kwasar gaisuwa "Hajjata ina kwana?" "Lafiya lau Salmatyy, fatan kin tashi lafiya?" "Lafiya lau Hajjata." "Ana ta zuwa kai maku break sai ace baku tashi ba?" Kallon Yarima Salmah ta yi a fakaice, shi kam ya jefa mata harara kasa-kasa ya wani haɗe rai "Hajja mun tashi tun ɗazun, fa gyara gidan mukaita yi." Salmah ta bata amsa tana nufa wajen da aka shirya masu abinci. Zuba masu ta yi ta dauki cup din tea zata kai baki, Yarima ya yi saurin amshewa yana kada mata kai, murmushi ta sakar masa da kansa ya rika bata tana ci har sai da ta koshi, bayan sun kammala Salmah ta fara lumshe ido don ita kam bacci take ji "ya dai Ummuna?" "Bacci." Ta faɗa da murya kasa-kasa. "Tashi mu je ki kwanta kanwata." "A'a Hamma a dakin Hajja zan kwanta.
Da kyar ya lallasheta ta bi shi bangarensu, duk wannan abin da suke yi Hajja tana jinsu, amma sai ta ɗauke kai kamar bata san suna yi ba sai dai duk da haka ta ji matuk'ar dadin ganin yadda suke kula da junansu, addu'a take yi masu na daurewar zaman lafiya.
A kwanakin da Yarima ya yi sosai suka murji juna, Salmah tana wahaluwa ahannun Yarima don shi bai san ya gaji ba, ita kuma tana daurewa ne badan komai ba sai dan kar ta saɓa masa, bata gaji da shi ba sai dai ba ya barin ta huta ne.
RANAR LAHADI yau ce ta kama Yarima zai koma domin kwana uku kawai ya dauko, zaune yake gaban Hajja yana sauraron abin da zata ce game da tafiyarsu da Salmah, sai da ta yi mintina biyar sannan Hajja ta muskuta tare da gyara zama ta ce "ba tafiya da Salmatyy nake gudu ba, bana son ka je da ita kana takurata ne, sannan yarinyar bata saba zama ita ɗaya ba kaga idan ka tafi da ita kafin ta saba da aiki." Shiru Yarima ya yi don tabbatas yana son tafiya da Salmah, babban damuwarsa shi ne yadda zai rika barinta a gida, amma tafiya da ita shi ne mafi a'ala domin a kwanakin can da ya yi shi kadai yasan yadda ya kasance. Amma sai dai baya ja da maganar Hajja don haka sai ya ce "to Hajja yadda kika ce haka za a yi." "Allah ya yi albarka! Wani zuwan idan Allah ya kaimu sai ku tafi kuma tare da su Zaituna don su rika ɗebe mata kewa." Murmushi ya yi ya ce "Muna godiya sosai Hajja da wannan karamci Allah ya kara nisan kwana." Bata amsa ba sai tashi ta yi ta wuce bangaren Maimartaba.
  Kwance ya yi saman gado tare da jawo Salmah ya daura kanta saman kirjinsa yana shafawa a hankali, domin yadda ta lafe a jikin nasa "Wai Ummuna yau kam lafiya?" "Me ka gani Hamma?" Salmah ta tambaya tana ɗago kai. "Abubuwa da yawa, ko dan Hajja ta hana tafiya dake? Sannan baki haɗa min kayan tafiya ba, ko baki da lafiya ne don jikinki da dumi fa." "Yanzu zan haɗa maka Hamma, babu komai lafiya lau zafin gari ne." Ta dire maganar tana mik'ewa.
       Babu bata lokaci ta haɗa masa duk wani abu da zai buk'ata, sannan ta haɗa masa ruwan wanka duk yadda yaso su yi tare ki ta yi, dole shi kaɗai ya yi yana fitowa ta taimaka masa ya shirya, kamar ko yaushe idan zai koma wajen aiki sai ya bi duk bangarorin ya yi masu sallama, yauma haka Salmah ta raka shi ya yi sallama da kowa, a bangaren Hajja Chub'ad'o ne Yarima ya ɗan jima, domin suna shiga Hajja ta kalli Salmah kallo irin na tsanaki, sai ta ga kamar akwai abin da ta hasaso a tattare da ita, amma sai ta basar domin kunyar da take ji yana nan, dan ma Salmah ce ta ba zata iya sakewa da ita ba.
     "Salmatyy lafiya kuwa?" Hajja ta yi tambayar bayan sun gama gaisawa. "Lafiya lau Hajja me kika gani?" "Babu komai Yar Hajja na yau duk kinkoma wata iri ce, kamar mara lafiya sannan jikinki da dumi." "Hajja nima ɗazun na yi maganar jikinta da dumi amma ta ce wai dumin gari ne." Yarima ne ya ba Hajja amsa yana tsare Salmah da ido. "Allah nifa Hajja lafiya ta lau fa." Maganar take tana turo baki cike da shagwaɓa. "Ai haka ake so tun da lafiya kike shi kenan." Hajja ta faɗa bayan ta tashi tsaye.
    Yarima na ganin Hajja ta shige bedroom yajawo Salmah jikinsa yana faɗin "zan yi kewarki Ummuna." Bata amsa ba sai da ta janye jikinta kafin ta ce "Ni haka Hamma, Please ka kular min da kanka." "Na yi maki alkawarin kula da kaina fiye da yadda kike tunani." Suna wannan musayar kalaman ne Hajja ta fito, dambu nama da na kifi wanda ta sanya aka yi masa ta mika masa tana mai yi  masa fatan alheri. Har wajen motar Salmah ta rakashi sannan ta koma, bangaren Hajja Chub'ad'o ta shige can kuryar daki gan gado ta kwanta tare da jawo bargo ta rufa, domin sanyi take ji sosai duk abin da take dama dauriya ce don kar ta hana Yarima tafiya, amma ita ɗaya tasan yadda take ji a jikinta, sam Hajja bata san Salmah na cikin bedroom a kwance ba ta yi tunanin tana wajen su Hamma ɗan Waziri, sai da ta shiga dakin zata ɗauki abu numfashin da ta ji kamar ana jansa da kyar yasa ta yi saurin karasawa "Hasbinallahu! Salmatyy me ya sameki?" Hankali tashe Hajja ta yi maganar bayan ta yaye bargon da Salmah ke ciki.
     "Hajja rufeni sanyi nake ji please." Murya na rawa jikinta kamar ana kada masa mazari ta yi magana. "Subhanallah! Zazzaɓin ne kenan? Sannu tun ɗazun sai da na yi magana kika musa min Allah ya sauwaka." Hajja na maganar tana ballo mata pracitamol. Da kyar Salmah ta hadiye maganin domin sam bata kaunar shan magani. Bayan ta gama sha sai Hajja ta fita domin jakadiya zata ba sako, shi ne ta shiga daukowa ta samu Salmah a haka, mik'awa jakadiyar ta yi tana faɗin "Salmatyy na ciki bata da lafiya, sam ban lura ba sai yanzu ga yi mijin ya tafi ɗazun." Murmushi jakadiya ta yi ta ce "Uwar gidana nifa tun satin can na so yi maki magana domin sai na ga kamar Salmah tana dauke da..."

Tofa! UMMREEMA kardai abin ne ya samu fa🤭na ga an fara ciwo, kuma dama Yarima gwanine sam baya wasa da wannan fannin.😹😹😹

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now