Page 18

951 55 0
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                         ©
     *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

'''Ina matukar godiya gareku da addu'oin ku da kuka yi min, Alhamdulillah na samu lafiya, ba zan manta da ku ba masu kirana da masu text, musamman yan kundin kaddarata fan's da Zahra surbajo Hausa Nobel ina jin dadin kulawar da kuka nuna min shi yasa na ce bari na yi maku typing'''

Masu cewa pure moment of life ta mutu to Aradu karya ne, gamu zaune a duniya, daram dam dam mulkin namadi a Kaduna

Wannan page din na yau sadaukarwa ne ga SADNAF

                    *18*
Jiki a matukar sanyaye Nuwaira ta fita daga office din, ko ta kanta Yarima bai ba ya mikawa sakataren sa makullin ya yi tafiyar da, da mugun gudu ya figi motar har kamar zai bangaje Nuwaira, yana parking bai tsaya ɗaukar komai ba ya fita daga motar. Tana zaune a falon ta zuba uban tagumi tana tunanin yadda har Yarima ya gota lokacin dawowarsa, kamshin turaren da ta ji ne yasa ta ɗago da kai, murmushi ta saki mai kyau tare da furta "Hamma! Cikin siriyar murya ta ambaci sunansa. Yana tsaye tare da harde hannuwa a kirjinsa ya karya kai gefe, fuska cike da annuri.
    A hankali Salmah ta isa gareshi tare da rungume shi ta ba shi welcome kiss, lumshe ido ya yi ya bude su fes a fuskarta ya ce da kasalalliyar murya "Ummuna salonki na kashe min jiki." "Hmmmm! Hamma ina ka tsaya ne yau kam ka dade?" "Ki bari kawai Ummuna yau aiki ya so ya yi min yawa yanzu ma da kyar na iya yaki ce shi." "Ayya sannu Hamma ai da ka kirani sai na taya ka." Ta yi magana tana kallon cikin idonsa. "Kuma fa haka ne, amma karki damu ke ce ma zaki rika zuwa office din da kanki."  Bata yi magana ba sai kara rungume shi ta yi ta daura kanta a faɗaɗɗen kirjinsa. Hannu ya kai kan cikinta tare da shafawa ya ce "fatan babyna bai takurawa Ummuna ba?" Baki ta turo ta kwace jikinta daga na shi, bata yi magana ba sai riko hannunsa ta yi zuwa kan kujera. A tsanake ta cire masa duk wani kaya masu nauyi dake jikinsa ya rage daga shi sai singileti da gajeren wando "Hamma food is ready, ko sai ka fara yin wanka?" Narke fuska ya yi cikin shagwaba ya ce "sai yadda Ummuna ta ce." Murmushi ta yi don wani lokacin sosai take mamakin yadda Yarima ba ya ko jin kunyar yi mata shagwaba.
    "Mu je ka fara yin wanka sai ka ci abinci." Da kanta ta raka shi toilet wanka ya yi da ruwa masu zafi yana fitowa ta taimaka masa ya goge jiki da towel sannan ya zura jallabiya, kai tsaye suna fitowa daga bedroom dining suka wuce inda ta shirya masa lafiyayyen girki, zama Yarima ya yi Salmah ta rika ciyar da shi har sai da ya koshi, amsan cokalin ya yi ya dibi abinci tare da kaiwa bakinta, da sauri ta juyar da kai alamar a'a da mamaki ya ce "Me yasa haka Ummuna?" "Bana jin ci ne Hamma." "Ban gane baki jin ci ba? Me kika ci to?" Ya yi tambayar yana tsareta da ido. Shagwaɓe fuska ta yi ta ce "Ban ci komai ba." "Baki ci komai ba amma kika ce baki cin abinci? Haba Ummuna ki daure ki ci ko kina bukatar wani abu ne?" Da kulawa ya yi tambayar. "Awara Hamma." Salmah ta fada tana kallonsa. "Awara kuma? A ina zamu samu awara da daren nan?" Bata yi magana ba sai tashi ta yi daga kujrerar ta nufi inda yake a cinyarsa ta yi masauki sannan ta ce "A cikin gari mana, Allah Hamma ita kawai nake jin ci." "Ko za a kira su Zaituna ne su sayo maki?" Makale kafada Salmah ta yi cikin sauri sannan ta ce "A'a Hamma sai dai mu je ni da kai, domin su Zaituna sun yi aiki sun gaji." Ya ya iya dole ya amsa don baya muradin ganin ta kwana da yunwa, don haka sai ya ce "Ok Ummuna duk yadda ki ka ce haka za a yi." Tashi ya yi ya nufi bedroom hijab ya ɗauko mata hijab sannan suka fita, cikin ikon Allah basu yi tafiya mai nisa ba suka samu ana soyawa, siyar mata Yarima ya yi sannan suka koma gida, sosai ya yi mamakin yadda ta zauna sai cin awara take tare da yaji, tana gamawa duk da bata cinye duka ba ruwa ta kora ta saki gyatsa, sannan ta gyara zama  "Sannu Ummuna." Yarima ya fada yana kara kallonta. "Yawwa Hamma." Salmah ta bashi amsa. Ya bude baki zai yi magana kenan aka yi sallar magrib.
     A tare suka tashi kowanne ya nufi bedroom ɗinsa don yin alwala, Yarima na gama alwala masallaci ya fita, ita kam a daki ta ta gabatar da nata, bai shigo gidan ba sai bayan ya isar da ishsha bai samu Salmah a falo ba, don haka sai ya shiga bedroom akan gado ya ganta kwance. Zama ya yi gefen ta yana fadin "Wayyo ni maraya, shi kenan ba ki jin tausayina yau kwana biyar kenan kafin na dawo masallaci kin yi bacci fa." Da muryar tausayi ya gama maganar. "Yanzu ya kake son a yi Hamma?" Ta yi tambayar bayan ta tashi daga kwancen. "A taimaka min in rage zafi." Ya fada yana kashe mata ido daya "Kai Hamma Allah baka iya samun waje ba, yanzu sai kabi duk ka gajiyar dani." Da sauri ya ce "Allah yau kadan zan yi kuma a hankali, kin jina ce Allah." Ya karasa maganar kamar wani marayan yaro. Dariya Salmah ta tuntsire da shi don sosai Yarima ya bata dariya, da wannan damar ya samu ya fara shafar ta, har sai da ya gama kashe mata jiki, sannan ya hade bakinsu wata duniya suka shiga mai dadi da sanya nishadi, sun manta ma akwai sauran mutane a tunaninsu su kai dai ne a duniyar, sosai suka faranta wa juna rai duk da Salmah ta gaji a haka ta biye masa, lura ya yi da hakan shi yasa kawai ya saurara mata.
     Tana kwance a faɗaɗɗen kirjinsa bayan komai ya lafa, a hankali Yarima ya kai hannu saman cikinta yana fadin "Ummuna har yanzu cikin yaki girma inga kina tafiya da kyar." Saurin buge hannunsa ta yi tana fadin "Allah ka daina." "Na daina Ummuna. Yarima ya gama maganar yana sama da ita, toilet ya nufa da ita tsarkake jikinsu suka yi, sannan suka kwanta rungume da juna a haka bacci mai dadi ya dauke su. Washegari da misalin karfe takwas Yarima ne ya gama shirinsa tsaf don tafiya office, wayarsa dake hannun Salmah ne ta yi kara, kallon screen din Salmah ta yi gabanta na faduwa "Nuwaira! Ta furta da murya mai sauti. Wani irin razana ne Yarima ya yi, don ya firgita da jin sunan da Salmah ta ambata, tattaro nutsuwarta tayi tare da kalkalo murmushin karfin hali ta ce "Hamma ga yi ana kiranka." Amsa ya yi tare da sanyata cikin aljihu, ganin haka da Salmah ta yi sai ta diga ayar tambaya, da sauri har da gudu ta koma bedroom a kan gado ta zube, wasu hawaye suka fara ce sauka kan fuskarta, haka kawai ta ji zuciyarta bata aminta da wancan Nuwaira din ba.
   Yarima na tsaye kamar an dasa shi, sai da kyar ya iya tattaro nutsuwarsa sannan ya bita bedroom din, sosai hankalinsa ya tashi da ganin yadda take hawaye, zama ya yi kusa da ita tare da jawota jikinsa da sarkewar murya ya ce "kukan me ki ke yi haka Ummuna? Ki bar yin kuka domin Nuwaira abikiyar aikina ce kuma kin ga yau kamar ban fita da wuri ba shi ne ta ki rani, karki bata KYAKKYAWAR ALAK'AR mu da zargi." A tausashe ya yi maganar, shiru Salmah ta yi ta kasa tsayar da hawayenta don tun jiya ta gama da wasu abubuwa, bude baki ta yi da yar ta ce " Yar wajen aikinku? Shi ne ta kira baka dauka ba?" Girgiza kai ta yi cikin wani irin yanayi.

Vote me
Shere
& Comments on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now