Page 4

1.3K 85 1
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                                 ©
              *_ZULAYHEART RANO_*

*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                         *04*

Tsugune Salmah ta yi akalla ta Kai mintina goma, har ta fara gaijiya don haka ta sanyaya muryarta ta ce "Hamma gani." Harara ya watsa mata sai da ya Yi minti biyu kafin ya bude baki kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Ina kallonki ai ko yanzu ma rashin kunyar za ki yi min? Wai Salmah me kike ji da shi ne da har kika raina kowa? Ko dan kin ga Hajja tana goyan bayanki?" Ya dire maganar yana mata wani kallo. Girgiza kai ta yi cikin nutsuwa ta ce "Ka yi hak'uri Hamma ba zan sake ba." "Ke din ce za ki ce ba zaki kara ba? Ai wannan ma magana ce duk wani abu da kike yi ina ɗaga maki kafa ne saboda KYAKKYAWAR ALAK'AR dake tsakanin iyayenmu, amma na kusa fara ɗaukar mummunar mataki akanki."
     "Ka yi hak'uri don Allah." Wannan karon ma da sanyin murya ta yi maganar. Ci gaba da danna wayarsa ya yi zuwa can ya ce "tashi ki wuce saura ki faɗawa Hajja wannan maganar." Mik'ewa tsaye ta yi kafafunta duk sun yi mata nauyi ta ce "sai da safe Hamma." Ɗago da kansa ya yi daga kallon da yake wa wayarsa wanda ya maida hankali kacokan akan ta, karaf suka hada ido kasa janye idonta cikin nasa ta yi domin wani irin abu taga yana fitowa daga idonsa yana shiga nata, ta bangaren YARIMA haka ya kasa janye nashi, lumshe ido ta yi badan ta gaji da kallon cikin idonsa ba, sai dan kar ta sanya kanta cikin matsala, a hankali ta ja kafarta ta bar wajen.
       Nannauyan ajiyar zuciya YARIMA ya sauke, wani irin tausayin
Salmah ne ya shiga zuciyarsa yana mamakin halinta, duk da shagwaɓaɓɓiya ce ta karshe amma tana da sanyin hali, duk walak'ancin da ya yi mata amma da zata tafi har da yi masa sallama "Allah sarki Salmatyy zan iya zama dake matsayin matar aure ko dan saboda sanyin halinki da KYAKKYAWAR ALAK'AR dake tsakanin mu dake." A fili ya yi furucin wanda bai san sun fito ba. Ya daɗe zaune a wajen yana tunanin Salmah sannan ya wuce daki.
             "Ummuna ai na yi tunanin a wajen Yawuro za ki kwana?" Cikin sakin fuska Hajja Chub'ad'o ta yi maganar. Salmah bata yi magana ba sai da ta isa kusa da kafar Hajja kanta ta aza bisa cinyar Hajja cike da shagwaɓa ta ce "Ai ni Hajjata bana jin zan iya kwana wani wajen, domin na saba da kwanciya jikin Hajjata." Shafa sumar kanta mai tsananin laushi da santsi Hajja ta yi ta ce "ga yi kuma kin kusa barin jikin Hajjar taki, tun da aurenki ya kusa sai kin zo tun za ki kwanta ajikin Hajjar ki." Shiru Salmah ta yi wasu hawaye suka taru a idonta, domin tasan maganar Hajja gaskiya duk ranar da ta tare gidan Hamma Yarima da aure tasan zata rasa da yawa daga cikin farin cikin ta, take abin da suka yi da Yarima  ya fado mata, lumshe ido ta yi ta bude bata son Hajja ta fahimci komai, don haka sai ta zame jikinta tare da mik'ewa tana fadin "Hajja wanka zan yi ina jin zafi yanzu zan dawo." Tana gama faɗa ta shige, a fito lafiya kadai Hajja Chub'ad'o ta cewa Salmah tana rakata da ido har ta shige bedroom, girgiza kai Hajja ta yi ta ce "Ummu Salmah farin cikin Hajja Allah ka nuna min auren Salmatyy da Yarima." Bata dawo falon ba sai da ta yi sallalo sun sha hira da Hajjarta sannan ta kwanta.
     Tsaki kawai yake bugawa wanda shi kansa ba zai iya cewa ga ga adadin su ba, amma dai da babuhun shinkafa empty aka ɗauko ana sanya tsakin da Yarima ya yi na tabbata zai cika koma ya fi bahun. "Lafiya kuwa Yarima?" Mtsww ya kuma jan tsaki a karo na ba adadi "lafiyar kenan, kaga yanzu fa already na kammala shiri amma wai Hajja tana faɗa min za a yi zama don tabbatar da sanya ranar auren nan, gaskiya na gaji wallahi ana matukar shiga hakkina, dole sai ina wajen za a sanya ranar aure?" A zafafe yake tambayar da gani ransa a ɓace yake. "Haba Yarima ka riƙa sanyaya abu mana don an ce sai an yi zama shi ne abin tashin hankali? Shi fa wannan abu da za a yi ba sai kana wajen ba, baka san hikimar Maimartaba ba da ya ce tafiyar ka sai gobe, ka bar shi matsayin goben Ina Ningi ina Bauchi da zaka tashi hankalinka yau da gobe duk na Allah ne,  ka saurara da kyau Ina baka shawara a matsayina na dan uwa a gareka wanda muke da KYAKKYAWAR ALAK'A da fahimtar juna ka sanyaya zuciyarka ka riƙa ambaton Allah zai kawo ma sauki." Wata ajiyar zuciya Yarima ya sauke mai karfi sakamakon sunan Allah da ya ambata kamar yadda ɗan Waziri ya ba shi shawara "to ɗan Waziri na gode da shawarar ka." "Amin." Dan Waziri ya amsa cike da jin dadin yadda Yarima ya sauko daga dokin da ya hau, yana son Yarima ya zama mai sanyin hali ko dan ya rika tausayin Ummu Salmah a zamantakewar aurensu, tabbas yasan hada ran da Yarima yake yana daya daga cikin abin da yake sanya Salmah damuwa, don haka ya dauki damarar sai ta shi kan hanya kafin aurensu da ita, sun daɗe suna hira koma dai nace ɗan Waziri na ba wa Yarima shawarwari.
    Kaya sosai Yawuro ta haɗa na godiyar an bada auren Salmah ga Yarima, Ameena ga ɗan Waziri, irin su gishiri, biscuit, goro da sauran su, domin a al'adar su ana haɗa irin wannan kayan ne a matsayin na godiya, kuma babu mai haɗawa sai waliyyin ango shi yasa aka hada a bangaren Baba Waziri, domin Yawuro ita takasance uwayen angwaye, Hajja kuma ta amarce. A ranar an yi kwarya-kwarya taro kamar dai ana biki dangi na kusa da na nesa duk sun haɗu, rarraba su gishirin da sauran kayan aka yi wa yar'uwa da jama'ar gari domin shaida an bai wa Yarima Salmah haka kuma an bai wa ɗan Waziri Ameena, gidan na cike sai dare kafin jama'a suka ta fi. Salmah da ta kunshe a daki ta ki fitowa domin kunyar mutane take ji sai a lokacin ta samu fitowa. Gaban Hajja ta zube tana rike ciki, da sauri Hajja ta dagota tana faɗin "lafiya kuwa Salmatyy?" "Cikina ke ciwo Hajja." "Kin ci abinci?" Hajja ta jefa mata tambayar. "Yo Hajja Ina fa Salmah ta ci abinci, ɗazun babu yadda ban yi da ita ba amma fir taki ci wai bata jin cin komai." Adda Hafsah ce ta yi maganar cikin takaici. "Oh! Allah Salmah wai ke kam kin fi son Kullum kina zama da ciwon ciki na rashin cin abinci? Kin ga tun wuri ki daina domin kar wata rana ki yi wa kanki illa." "Hajjata fa ɗazun na ci abinci." Ta dire maganar tana turo karamin bakinta. "Kin ci abinci shi ne kike ciwon ciki?" "Allah Hajja na c..." Bata gama rufe baki ba ta ji muryar su Yarima yar da Hamma ɗan Waziri. "sannunku da shigowa Hamma."  Adda Hafsah ta faɗa cikin ladabi. "Yawwa Hafsah kina nan baki tafi ba?" Dan Waziri ya yi maganar cikin daure fuska, wai shi a dole zai yi wa kanwarsa faɗa, shi kam Yarima ko kallonta bai ba ya samu waje ya zauna yana wani shan kamshi, da ga gani dai yau sarautar a kusa take.
     "Eh Hamma amma Yanzu da ya zo zamu wuce." "To gara dai domin dare na yi."  Sai da ya gama fadar sannan ya zauna yana gaida Hajja, mtsww Yarima ya ja siririyar tsaki haushi ne ya rufe shi ganin Salmah jikin Hajja "lallai yariyar nan ta cika shegen son jiki kullum a jikin Hajja, zai yi maganin ta." A zuciyarsa ya yi maganar. "Lafiya kuwa Ummu Salmah?"  Dan Waziri ya yi tambayar da kulawa. "Cikin ta ke ciwo kasan dai halin Salmah bata kaunar cin abinci yau tun safe bata ci komai ba shi ne cikin ya kulle." "Subhanallah! Sannu Salmah Allah ya sawwaka." Duk abin da suke Yarima yana ji amma ko kallon ida take bai ba balle ya yi magana, sosai Hajja ta cika da haushi domin bata son yana nuna halin ko in kula da harkokin Salmah. "Hajja gobe zan koma Bauchi." "Allah ya tsare hanya." Cike da haushi ta yi maganar,  Kamar yasan ya kai Hajja bango don haka sai ya mike tsaye yana faɗin "ke Salmah ki sameni bangaren Yawuro."

Team Yarima Hafiz
Team Ummuna Salmah
Zulaiha Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now