36

206 22 6
                                    

KYAKKYAWAR ALAƘA

       ©
ZULAYHEARTRANO

STORY AYSHA WAZIRI

36

Abin da ya cigaba da ba su Adda Khadijah mamaki, inda kuma su ka ƙara gasgata hasashen su, domin kuwa har yanzu da suke kwana ɗaya da yini daya a gidan Yarima ba su ji ko sau ɗaya ya kira Salmah ba. Sai dai cikinsu babu wanda ya kuma yi wa Salmah magana don sun san ko sun yi ba za su taba samun gamsashshiyar amsa ba.
  “Ni kam Wallahi na gaji da zaman waje ɗaya, bari na fita ko harabar gida ne na zauna tun da babu wajen zuwa.” Adda Hafsah ta faɗa tana miƙewa, su ma miƙewa suka yi tare da fita sai da suka gama zagaye gidan har ɓangaren su Zaituna suka shiga, sun ɗan taɓa hira kafin suka koma kujerun dake harabar shiga falon Salmah a nan suka yi mazauni, suna cigaba da hira hankali kwance.
  Wata hadaddiyar Mota ce ta shigo gidan, kai tsaye a harabar ajiye motoci ta yi fakin, Yarima da Nuwaira suka fito daga cikin motar, Yarima na sanye da riga jeans da T-shirt kayan sun matukar amsar jikinsa, musamman wani kyau da ya ƙara. Ita kuwa Nuwaira jikinta doguwar riga ce wacce ta kama mata jiki sosai, kai ko dankwali babu, sai sumar da ya zubu kafaɗunta kallo ɗaya za ka yi wa suman kasan yar kanti ce, don ba ta yi kala da ta mutane ba. A tare suke jerawa ko kusa bai kalli gefe Salmah ba don shi kwata-kwata ma ya manta yana da wata matar balle kuma 'ya'ya, har a je ga batun 'yan'uwa. Shi yanzu a duniya Nuwaira kawai ce yake iya kallo.
  Jikin Salmah rawa ya kama saboda tsabar kaɗuwa, tabbas da a ce ita ɗaya ce da tuni ta shige bangarenta, amma yanzu idan ta miƙe kamar ta fito fili ne ta sanar da su damuwarta, don haka sai ta dake tare da ɗauke kai gefe tana wasa da 'yan yatsunta.
“Prince waɗancan kamar kannanka?” Nuwaira ta faɗa tana nuna mashi su Adda Khadijah. Dan waiwayowa ya yi tare da kallon wajen, cikin sauri ya nufe su yana faɗin
  “A'a su Khadijah ne a gidan namu?” Ya yi tambayar cike da kulawa.
   “Eh! Hamma ai tun jiya muka zo, da yake dama Hajja ta ce mana kun yi tafiya, sannu da dawowa.”
  “Yawwa aiko kun kyauta, bari na je na watsa ruwa sai na dawo mu yi hira, sakkowar mu daga jirgi kenan yanzu.” Ya faɗa yana tafiya, ba tare da ya cewa Salmah komai ba, hasalima ma bai kula tana wajen ba. Hawayen da Salmah take riƙewa suka samu damar zubowa, da sauri ta kai hannu ta share don ba ta son su Adda su gani, amma ta san ita kam a iya tsayin rayuwarta wannan shi ne cin mutunci mafi girma da aka taɓa yi mata.
“Adda bari na shiga ciki na shiryawa su Hamma abinci, tun da wanda muka dafa ya ƙare.” Salmah ta faɗa tana miƙewa.
Da kallo suka bita kallo irin na tausayawa, ita kuwa da sauri ta shiga ciki. Hankali kwance ta fara aikin abincin ba ta wani daɗe ba ta kammala, don ba abinci mai wahala ta girka ba, farfesun kan sa ne sai kuma shinkafa da miya, dama Allah Ya sa ma suna da miyar, shinkafar da farfesun kawai ta yi.
Cikin babban tire ta shirya abincin sannan ta kira Zaituna a kan ta miƙa masu, su dai su Adda Khadijah sun zubawa sarautar Allah ido, suna kuma mamakin halin Salmah. Ita dama Adda Hafsah don takaici ba ta ma tsaya a Falon ba, ita ma ganin haka sai Adda Khadijah ta bar falon sai Salmah kaɗai.
  Tana zaune tana tasbihi idanuwanta a rufe, sam ba ta ji shigowar ta ba sai jin saukar abu mai zafi ta yi a jikinta, ba ta san lokacin da ta kwarma ihu ba, wanda ya yi sanadiyar fitowar su Adda Khadijah da sauri. Suna fitowa suka fara tsinkayar muryar Nuwaira tana faɗin “Ke har kin isa ki ce za ki shiga tsakanina da Mijina? Idan ban da munafurci mene ne na ki na aiko wa da abinci? Uban wa ya ce maki muna bukatar abinci? Idan kika kuma yi mana shishigi Wallahi sai na yi maki abin da ya fi hak...” Allah Ya yo Adda Hafsah da zafi, a duniya ba ta ɗaukar raini ba ta yi ba ta son a yi mata, ba kuma ta son a yi wa wani, ballantana kuma Salmah da take 'yar uwa a gareta kuma matar ɗan'uwa mafi soyuwa a gareta, don haka ido rufe ta isa ga Nuwaira. Wasu zafafun mari Adda Hafsah ta zabgawa Nuwaira a kumatun ta biyu, ta daura da cewa “Ke wacce irin dabba ce mara mutunci mara hankali? Ke har kin isa ki ce za ki yi wa Salmah rashin mutunci? Wacece ke? Me kike taƙama da shi? To Wallahi idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri domin Salmah ba sa'ar yinki ba ne, daga ke har zuri'arku.”
  “La! La!! La!!! Kika mareni? Wallahi sai kin san kin mareni yau a gidan nan.” Nuwaira ta yi maganar hannu riƙe da kunci.
“Ki je ki faɗawa ko waye ne ki ce Ni na mareki, ya zo ya ɗaukar maki mataki.” A hasale ta dire maganar.
   “Ayya Adda da kin sani ba ki mareta b...” Cikin tsawa Adda Khadijah ta katse Salmah ta hanyar cewa “Salmah ashe haka kike? Ashe har lusarancinki ya kai haka? Ki yi mata abin arziki ta saka maki da tsiya an ɗauki mataki ki zo kina wani magana? Wallahi kin bani kunya da har za ta ci maki mutunci ki kasa ramawa, sannan kuma ki hana wani rama maki.” Nan fa suka balbale Salmah da faɗa.
  A zafafe Yarima ya shiga falon jikinsa har yana tsuma, yana gaba Nuwaira tana biye da shi a baya tana yi masa kukan kissa, gadan-gadan wajen Adda Khadijah ya nufa shi a dole an dakar masa mata bai tsaya tambayar ba'asi ba ya daga hannu da niyyar zabga mata mari, ai kuwa da sauri ta ja baya Allah Ya taimake ta bai sameta ba, dama ita Adda Hafsah ba a kusa da shi take ba. A masife ya fara magana “Wallahi duk wacce ta ƙara dukar min mata sai na yi mata abin da ba ta taɓa tunani ba, an gaya maku jaka na auro da za ku sanyata a gaba da duk..?” “Haba Hamma, me ya sa ba ka ga laifin matarka ba? Bayan kuma ita ce bata da gaskiya? Don kawai Salmah ta aika maku da abinci shi ne za ta zo ta juye mata a jiki bayan kuma abincin yana da zafi?” Da sauri Adda Hafsah ta katse Yarima.
  “Baby ta juyewa Salmah abinci a jiki?”
“Duba ka gani Hamma ai ga Salmar nan.” Adda Hafsah ta dire maganar tana nuna Salmah, jikin Yarima ya ɗan yi sanyi maimakon ya fara yi wa Nuwaira faɗa ga mamakinsu sai kawai suka ji ya fara magana ido rufe yake zazzaga masifa “Ai gara da ta yi mata haka, ko an ce mata da yunwa muka dawo? Idan ban da iyayi irin nata, ni bana son shishshigi, kuma wallahi duk wacce ta kuma dukan matata sai na rama mata, marasa mutunci kawai.” Daga haka ya ja hannun Nuwaira suka yi waje.
  Suna shiga ɓangaren su Yarima ya fara rarrashin Nuwaira.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now