Page 14

1.1K 74 2
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                               ©
              *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad user name Zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

                  *14*

Wajen da aka shirya abincin suka nufa, da kanta ta zuba masa ta dauki cokali tare da dibowa zata kai bakinsa ya yi saurin amsan cokalin, yana faɗin "no Ummuna kawo ki huta zan iya ci da kaina." Ya dire maganar yana sakar mata murmushi. Bata ce komai ba sai zama ta yi kusa da shi ta jingina kanta a kafadarsa. Sosai ya ci abincin domin dai yunwa yake ji sosai, rabonsa da cin abinci mai dadi irin haka har ya manta, yana gamawa ya juya yana duban Salmah da bacci ya dauketa "Ummuna!" Ya yi furucin yana taɓa ta.
   Buɗe ido ta yi wanda suka fara canza kala ta ce "na'am Hamma ka gama ne?" "Eh! Tashi mu je bangarenmu." Yarima ya faɗa. "A'a Hamma mu jira har Hajja ta dawo." Da kyar Salmah ta yi masa maganar domin baccin na neman cin karfinta, Yarima bai ce komai ba sai dai bin ta da kallo yana dai mamakin yadda Salmah ke bacci. Yana zaune Hajja ta yi sallama, amsa mata Yarima ya yi "a'a baku tafi ba ashe?" Hajja ta yi tambayar cikin mamaki. "Wallahi Hajja kin ganta sai bacci take yi, yanzu na ce ta tashi mu je wai sai kin zo." "To ai gani sai ku tashi, amma ka bita a hankali don bata gama samun kwarin jiki ba." Sam Yarima bai fahimci komai ba sai amsawa ya yi da "to Hajja." Sannan ya fara tashi Salmah, ido fal bacci suka nufi bangarensu, suna shiga ta zube akan kujera ta ci gaba da bacci, girgiza kai kawai Yarima ya yi ya shige bedroom, komai tsaf kamar ba a taɓa amfani da su ba haka suke, kayan jikinsa ya canza zuwa jallabiya sannan ya shiga toilet ya haɗa masu ruwan wanka, falon ya koma har a lokacin Salmah bacci take yi don haka cak ya dauketa, bai zame ko ina ba sai toilet da kansa ya cire mata kayan jikinta sannan ya sanyata cikin ruwan wanka, kamar a mafarki Salmah ta jita cikin ruwa bude ido ta yi tana kallon Yarima, murmushi ya sakar mata sannan ya shiga cikin ruwan.
Lumshe ido kawai Salmah ta yi, bai jira komai ba ya fara murza mata jiki, shiru ta yi takasa magana don jikinta ya gama mutuwa sannan ga bacci, domin koda take cikin ruwan nan baccin bai sake ta ba, duk yadda taso faranta masa abin ya gagara don ta kasa hannunta ma wahalar dagawa take ji, Yarima kam bai damu ba ci gaba da cuda masu jiki ya yi, sannan ya canza masu ruwa ya dauraye masu jiki, sannan suka fita.
    Cream ya ɗauko mai taushi yana bin duk sassan jikinta yana shafa mata, daga haka dai salon ya fara canzawa, ya shiga shafar ta da kai hannu duk inda ya so,  sosai Salmah ta yi kokarin ganin ta faranta masa, Yarima kam ya kasa saurarawa Salmah don ji ya yi yau gaba daya ta canza masa, jinta yake kamar wata zuma, a bangaren Salmah iya gajiya ta gaji dama kokari ta yi don ta faranta masa, da kyar lokacin kusan uku saura ta samu ya barta, ta kasa tashi ta yi wanka don yadda bacci ya ci karfinta sai da aka shiga masallaci da Yarima zai fita ya tashe ta, sannan ya wuce ita kam ta shiga toilet ruwan masu zafi ta hada ta yi wanka tare da dauro alwala.
   Tun kan sallayar bacci ya dauke ta, Yarima na shigowa ya yi karo da ita kan sallaya, murmushi kawai ya yi ya dauke ta daga kasan ya daurata kan gado tare da cusata jikinsa, a haka suka ci gaba da bacci sai tara suka farka, shi din ma azababben yunwa ya farkar da Salmah jikinta har wani rawa yake ta maka mik'ewa, a hanzarce Yarima ya haɗa mata tea sai sannu yake mata don ya firgita tare da mamakin yadda ta koma, iya saninsa Salmah tana kaiwa sha biyu ba tare da ta yi break ba, amma yau tun tara saura har ta galabaita, tana gama shanye wa ta saki wani irin gyatsa zufa ya soma karyo mata "Sannu Ummuna dama baki lafiya ne?" Murmushi ta yi tare da ɗago kai ta kalleshi ta ce "lafiyata lau nake Hamma, kwana biyun nan idan na ji yunwa haka nake yi." "Ayya sannup to, bari na je na dauko mana abin break." Yarima ya gama furucin yana fara tafiya.
    Bayan fitar Yarima Salmah bedroom ɗinta ta shiga, shirin wanka ta yi bata jima ba ta fito  shafe jikinta da mayuka masu kamshi ta yi, sannan ta zura doguwar riga na atamfa ta yi daurin dankwali, sosai ta yi kyau sannan ta nufi falo inda Yarima ke zaune "har kin yi wanka kenan?" Yarima ya tambaya yana sakin fara'a. "Eh! Hamma zafi nake ji shi yasa na yi." Salmah ta bashi amsa tana zama kan cinyarsa ta zagaye hannayenta a wuyarsa.
Ajiyar zuciya Yarima ya saki yana ɗago fuskarta "Ina kwana Hamma an tashi lafiya?" "Lafiya lau Ummuna, fatan kema kin tashi lafiya?" "Lafiya lau." "Ɗazun kin manta da gaisuwa saboda yunwa ko?" Murmushi ta yi tana kara langaɓar da kanta a kafadarsa. "Tashi mu yi break Ummuna mu je gaida Baba Waziri Hajja ta ce baya jin dadi." "Baya da lafiya?" A ruɗe ta yi tambayar. "Ke ba fa ciwo mai zafi bane zazzaɓi ne jiya ya yi kuma ya samu sauki." Da murya mai kwantar da hankali ya yi maganar.
    A jiyar zuciya ta sauke tare da sauka daga jikinsa, Yarima da kansa yake ciyar da ita har ta koshi, sannan shima ya fara ci bayan ya kammala ya ya shiga wanka ya shirya sannan suka fita, bangaren Baba Waziri suka shiga suna duba shi da jiki, sun samu ya ji sauki don yana zaune ana ta hira da shi, ya ji dadin ganin Salmah da Yarima sai albarka yake sanya masu, suna fita bangaren Hajja suka yi don su gaisarta "Hajja ina kwana, an tashi lafiya?" Salmah ta yi maganar tana daura kanta a kan kafadar Hajja. "Lafiya lau Salmatyy, fatan kin tashi lafiya?" "Lafiya lau Hajjata." Salmah ta bata amsa tana gyara kwanciya. "Madalla!" Hajja ta amsa tana shafa kan Salmah. "Bacci nake ji Hajja." Salmah ta fada tana lumshe ido." "Kwanta ki yi yar Hajja." Murmushi Yarima ya yi yana fadin "Hajja wallahi wani irin bacci ne ya sarfaci Salmah, yanzu fa bata wani jima da ta shi ba wai bacci take ji yanzu." "Ai bacci na farin ciki ne." Jakadiya data shigo falon Hajja ta fada." "Dama jiranka nake na baka albishir." Tana washe baki ta gama maganar. "Ina jikinki jakadiya har na kosa na ji wannan albishir din domin daga ji abin daɗi ne." "To Uwardakina tana da juna biyu na satika bakwai." Wani irin Mik'ewa Yarima ya yi don farin ciki, kafin ya ce wani abu har Salmah ta gudu bedroom din Hajja. Sujadar shukur ya yi domin farin ciki, sam ya kasa boye murnar sa Salmah na dauke da cikinsa, lallai wannan abin daɗi ne "kin samu kyautar kujerar hajji da shi kansa Dr da ya duba Salmah ya gano." Murna ne ya rufe jakadiya da kyautar ubangidanta sai zabga godiya take (Ni kam Yar Mutan Rano na ce gaskiya jakadiya kin yi wa Dadah Nasir da Maman Husna yan kundin kaddarata fan's shigar sauri."
Harara Hajja ta aika masa don ta lura rashin kunyarsa ta yi ya wa, aiko da sauri ya mik'e  yana fadin "zan shiga cikin gari sai anjima." Har lau dai murmushin zallar farin ciki ke kwance a fuskar sa "A dawo lafiya." Hajja ta fada cikin kulawa. Kunya sosai ya kama Salmah don jin Yarima yasan tana da ciki , har ji ta yi kamar kar ta kuma hada ido da shi, a haka bacci ya dauke ta
Bangaren Yarima tun da ya fita yake rabon kudi don farin ciki, kowa ya shaida yana cikin murna bai dawo ba sai da aka yi azahar, abinci suka ci Salmah sai kasa take da kanta taki yadda su hada ido da Yarima suna gamawa suka koma sashinsu.
Tun daga bakin kofar shiga falo Yarima ya yi sama da Salmah, cilli take da kafa akan ya sauketa domin ta san kwanan zancen, amma ina sam Yarima yaki ajeta har sai da suka shiga bedroom ɗinsa, akan gado ya ajeta shima ya haye "Please Hamm." Bai bari ta k'arasa ba ya jefa harshen sa cikin bakinta, dole badan ta so ba ta sakar masa bakin yana yadda yaso, a gaggauce ya rabata da rigar dake jikinta, ya fara romance ɗinta rike masa hannu ta yi tare da marairaice fuska ta ce "Hamma ka yi hakuri Please wallahi bacci nake ji na gaji sosai." "Kin gaji ko Ummuna? Sorry sau daya kawai zan yi, wallahi bana gajiya dake ne kina bani matukar farin ciki." Kuma sai na hukunta ki tun da baki fada min ina da ajiyar a wajenki ba duk tsayin kwanakin nan." yana magana yana shafe jikinta "ka yi hakuri ai na yi tunanin ba a fada." Yau zaki gane fada ake ba a barinsa a yi shiru."  "Hamma..." Bakinsa ya jefa cikin nata, take suka ɗauke wuta sosai suka dage suna faranta wa juna rai, Salmah fa ta gaji don
Tun tana jin dadin abin da yake har ta fara gajiya, don haka sai ta sakar masa kuka tana rokon ya barta amma ina sam yaki saurara mata hasalima bai san tana yi ba, rike ciki Salmah ta yi ido na hawaye don mugun murɗa mata cikin ke yi "fadi take cikinna Hamma! Wayyo cikina zan mutu." a sukwane Yarima ya raba jikinsa da nata tare da rikota yana tambayar ta "cikin ki me ya samu cikin Ummuna?" A kidime yake tambayar. Juyi take akan gadon cikin zallar azaba ta zame kanta daga jikinsa ta ce "zan mutu don Allah ka kira min Hajja da Yawuro."
Da sauri ya jawo wayarsa ya danna kira layin Hajja, don baya jin zai iya barin Salmah a wannan halin, ringing biyu Hajja ta dauki wayar haka kawai ta ji gabanta ya fadi "Hajja Sal Salmah zata mutu don Allah ki zo..." Bai gama maganar ba ganin jini yana biyo kafar ta. "Jini?" Ya yi tambayar da karfi.

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now