Page 16

1K 61 7
                                    

👉🏽💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                         ©
     *ZULAYHEART RANO*
*Wattpad username zulayheartrano89*

*STORY AYSHA WAZIRI*

*Ina matukar godiya gareku da addu'oin da kuka min, na samu sauki sosai Alhamdulillah*

                    *16*
Raba jikinsa da nata ya yi a hankali tare da sakin numfashi, da gudu Salmah ta shige bedroom don ta ji matukar kunyar ganin da Hajja ta yi mata a jikin Yarima, shi ko Yarima ko a jikinsa domin dai zama ya yi yana fadin "Hajja ina yini?" Harara ta aika masa sannan ta ce "lafiya lau me ya kawo ka bangaren nan da dare?" Fuska daure take yi masa magana. Hannu ya kai saman sumarsa yana shafawa ya ce "emm dama dai zuwa na yi na ce, gobe zan tafi shi ne nake son ki bani Salm..." Wani mahaukacin kallo Hajja ta jefa masa wanda ya yi sanadin makalewar harfofin da zai fada. "To kuma ina ruwan tafiyarka da Salmah? Ko ka manta bata da lafiya ne?"  "Ai Hajja naga kamar ta warke ne shi yasa." "To ta warke kuma ba zata bika ba, idan ka cika cikakken mara kunya ka zo ka dauketa." Tana dire maganar ta shige bedroom, shiru Yarima ya yi zuciyarsa na yi masa kuna tabbas maganar Hajja ta bata ransa, ta ya shi da matarsa amma kullum cikin jan masa rai ake, babu shakka wannan karon zai yi watsi da lamarin Salmah duk kuwa da irin soyayyar da yake yi mata, tashi ya yi ya fita, a wannan rana da kyar bacci ya ɗauki Yarima gari na wayewa ya tattara kayansa ya koma Bauchi, cike da haushin abin da Hajja ke masa akan Salmah.
   Salmah kam na ganin Hajja ta shigo bedroom din sai ta kara runtse ido, don a tunaninta Hajja zata mata magana, amma sai ta ji shiru bata ce mata komai ba, don haka sai ta gyara kwanciya tana tunanin Yarima da irin soyayyar sa, kewarsa kawai take ji tana son kasancewa da shi tana wannan tunanin har bacci ya kwashe ta, karfe tara na safiya tana zaune tana yin break Aliyu ya shigo bayan sun gaisa suka fara hira cikin hiran ne Aliyu ya ce "Adda Salmah ba na ji Hamma Yarima ya ce idan ya dawo zai koma tare zaku koma ba?, kuma naga ya wuce ɗazun shi daya." Wani irin zabura Salmah ta yi sai kuma ta yi sauri ta koma don ta mata Hajja tana falon zaune, maida kwallarta ta yi don ta ji babu dadi "Yarima ya tafi ko ya yi mata Sallama, me ta yi masa da ya zabi ya kuntata mata haka? Wato ita bata nuna ta ji zafin abin da ya mata ba sai shi babu komai tun da haka ya zaba. A je cup din tea da take sha ta yi ta shige bedroom tare da hayewa gado ta saki kuka mara sauti.
     Da kallo Hajja ta bi Salmah, ganin daga fadin Yarima ya wuce ta sauya fuska, girgiza kai ta yi tare da tabe baki cikin zuciyarta ta ce "zaku yi zaku gama daga ke har shi don na lura baku da kunya." A zuciyarta ta yi wannan maganar. To haka dai kwanaki suke ta shuɗewa, kwanaki na komawa makonni, mokonni na komawa watanni a maganar da ake yi yau watan Yarima biyu kenan da tafiya, a wata biyun nan ko sau daya basu taɓa magana da Salmah ba, to ta kira shi baya dauka haka ko ta yi masa text baya budewa don fushi yake da ita sosai, tun tana damuwa har ta ɗan rage ma kanta. Yau da ya cika wata biyu cur Yawuro ce ta iso falon Hajja bayan sun gaisa ta ce
       "Wai nikam ko dai an yi wa magajin sarki wani abu ne Adda?" "Me ki ka gani?" Cike da kulawa Hajja ta yi tambayar. "Yau watansa biyu tun da ya tafi bai dawo ba shi ne nake tambaya Allah yasa ba wani abu aka masa ba." "Babu komai lafiya lau yake, kila áiki ne ya rike shi." "Ai shi kenan dama ina tunanin ko ya ji haushi ne da ki ka hana masa ya ɗauki matarsa." "Haushi? Ai indai don ya tafi da Salmah ne sai ya yi ta jin haushi domin ba zan bashi Salmah ba yarinyar nan bata san kowa a Bauchi ba." "Kai Adda amma kin manta aure babu inda baya kai mutum? Ai ita din macace don haka shawara kawai ki bashi matarsa." "Sai na yi shawara tunkun." Murmushi kawai Yawuro ta yi tana tsananin mamakin halin Hajja domin bata kaunar abin da zai rabata da Salmah.
     Daga haka suka yi sallama ta koma bangaren ta, duk wannan hiran da suke Salmah tana jinsu, a zuciyarta har addu'a take Allah yasa Hajja ta yadda da maganar bin Yarima Bauchi, babu abin da take so sai ganinta jikin Yarima tana shakar daddaɗar kamshinsa, yana yi mata soyayyar sa mai tsayawa a rai. Salmah ce zaune ta daura hannu akan cikinta da ta ji yana motsi, tashi ta yi ta matsa kusa da Hajjac sosai kamar zata shige jikinta, ta ce  "Hajja cikina na motsi kuma ba ya min ciwo, jiya sai da na jika magani na sha amma bai daina ba" Ta gama maganar tana jawo hannun Hajja ta daura saman cikin. "Hajja kin ji yadda yake yi fa." Karshen maganar ya yi daidai da zubowar hawaye. Zame hannunta daga cikin salmar ta yi tana fadin "daina kuka Salmatyy wannan ba abin tashi hankali bane, bari a kira Dr." Cikin sigar lallashi take mata maganar. A zuciyarta tana mamaki da hukuncin Allah, domin motsin da cikin Salmah ke yi babu shakka Yaro ne, sai dai bata tabbatar ba amma bari Dr ya zo, daukar waya ta yi ta kira Dr, bai jima ba ya shigo gwajin farko ya gano akwai ciki, ɗago da kai ya yi tare da duban su Hajja ya ce "Shugaba ai ciki ne a jikin Salmah, gashi nan har ya fara motsi." "Ciki Dr?" Da mamaki Hajja ta yi tambayar. "Eh! Shugaba ciki har na wata huɗu ga shi nan, Allah kenan buwayi gagara misali, shi yasa wancan lokacin na ce maku ban tabbatar cikin ko ya zube ko yana nan ba, ashe yana nan kwance a cikin mahaifiyarsa." Kyakkyawar murmushi ne ya kubcewa Hajja don tabbas ta kasa boye murnar ta da farin cikinta.
Ita kam Salmah mamaki ya kamata na yadda aka ce ciki bai zube ba, godiya ta rika yi wa Ubangiji domin ta ji dadin wannan lamarin, sai dai ta yi mamakin yadda bata yi wani kasala ba abu daya ta sani shi ne tana cin abinci fiye da tunani.
      "Wai Dr dama ko mutum ya yi zuban jini lokacin da yake da ciki, cikin jikinsa yana iya zama?" Adda Khadijah ce ta jefa masa tambaya. "Kwarai kuwa matukar dai ba bangaren cikin jinin ya zuba ba, kuma ko da ta wajen ne idan Allah yasa zai taka doron kasa ba zai fita ba sai dai ya dawo baya na wasu kwanaki kamar dai yadda wannan ya yi." Jinjina kai Adda Khadijah ta yi tana girmama hukuncin Allah.
    Lokaci ƙalilan har maganar cikin Salmah bai zube ba ya bazu a gidan sarki, gaba daya gidan sun ɗauki murna da farin ciki, don kusan burin su shi ne su ga jinin Yarima, sosai Salmah take samun kula a wajen alhalin gidan sarki, kowa so yake ya faranta mata, yau juma'a haka nan tun da ta tashi ta ji tana sha'awar shiga bangaren su, don haka sai ta nemo su Zaituna akan su gyara mata gidan, karfe sha biyu na rana suka gama gyara gidan tsaf sannan suka koma suka fada mata, godiya ta yi masu sannan ta ci gaba da harkokin ta don so take yi ta yi yammaci a bangaren, domin kewar Yarima ke azalzalar ta.
Bayan ta kammala cin abinci ta shiga toilet ta yi wanka, zama ta yi ta tsara kwalliya mai kyau, turaruka masu kamshi ta feshe bak'ar jallabiya ta sanya, ta yane kanta da dankwalin jallabiyar sosai ta yi kyau "iyye yammatan Hajja sai ina haka aka ɗauki irin wannan wanka?" Hajja ce ke tambayar tana shiga bedroom. Langaɓar da kai Salmah ta yi ta ce "Hajja bangaren su Adda Ameena zan shiga da wajen Yawuro, na gaji da zama waje daya ne." Murmushi Hajja ta yi a zuciyarta ta ce "hmm! Salmatyy kenan." Amma a fili sai ta ce "a dawo lafiya."
      "To." Kawai ta amsa ta fita falo, tana fita sai kuma ta ji kamar bata son tafiyar don haka sai ta zauna tana latsa waya, kamar a mafarki ta soma jiyo kamshinsa da wani irin yanayi ta daga kai ido huɗu suka yi ita da shi, kara bude ido ta yi don ta tabbatar shi din ne ba mafarkin da ta saba yi ba "bude ido da kyau Ummuna nine dai Hafiz dinki." Can kasan makoshi ya yi maganar. Lumshe ido ta yi ta bude fes ta sauke idon akan kyakkyawar fuskar Yarima da murmushi ke kwance. "Hamm..." "Kar ki ce komai sai mun je bangarenmu Ummuna, tashi da sauri kafin Hajja ta fito." Yana gama maganar ya riko hannunta, daidai da fitowar Hajja da sauri ya sakin hannun yana fadin "sannu da gida Hajja." "Yawwa har ka gama fushin kenan?" Fuska babu walwala ta yi magana. "Emm ai dama ba fushi na yi ba kawai aiki ne ya rike ni." Ya bata amsa  yana shafa sumarsa. Hmmm! Kawai Hajja ta ce ta fita daga ɓangaren. Yarima na ganin haka sai ya suri Salmah.
    "Please Hamma ka saukeni kaga akwai mutane a waje." Da shagwaɓaɓiya murya ta yi magana. "To ina ruwana da mutane ai matata na dauka ko?" "A'a ni dai ka barni na yi tafiya da kaina." Sauketa ya yi amma duk da haka sai da ya rike hannunta, suna shiga bangaren ya ce "woww Ummuna gaskiya gyaran ya yi kyau." Murmushi ta yi ta ce "wallahi yau din nan kawai na ji ina son yin yammaci a nan shi ne na sanya su Zaituna su gyara Hajja ma bata sani ba." "Lallai na yadda da soyayyar Ummuna ga Hafiz wato jikinki ya fada maki zanzo ko?" Murmushi ta yi tana zama kan kujera. "Ummuna a matse nake fa, wallahi tun da na barki a wahale nake kwana, kila yau na sake maki wani cikin." Hankali kwance yake magana "Au ai na yi tunanin ka yi fushi da Salmah, tun da har ka tafi ba tare da ka yi sallama dani ba ka manta da KYAKKYAWAR ALAK'AR dake tsakanin mu?" "Aje wannan maganar a gefe Please." Ya gama maganar yana daga ta sama "Please Hamma ka yi a hankali dani don karka je ka aikata na gaske don ciki na nan bai fita ba." Rikon da Yarima ya yi mata ya sanya ta kasa karasa maganar.

🤭🤭 Kai Yarima ya cika jaraba, kullum aikin abu daya ko dan irin fushin nan babu? Sannu Salmah da kokari kina aiki kam. Gara da kika fada masa kar ya kuma kalar na waccan time din.

Vote me
Comment
& Shere on wattpad

Zulayheart Rano

KYAKKYAWAR ALAK'AWo Geschichten leben. Entdecke jetzt