Page 23

839 55 1
                                    

👉🏼💍 *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏼

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITE'S* _P. M. L_

                           ©
     *ZULAYHEART RANO*
*My Wattpad Username zulayheartrano89*

*STORE AYSHA WAZIRI*

'''Masha Allah am back my fan's🥰🥰 nasan kun yi kewar wannan labarin?  To kar ku damu daga yau za a fara har sai na kammala shi, sannan kuma ina matukar godiya gareku hakika bani da abin da zan yi maku sai dai nace Allah ya tabbatar da alhairin sa a gareku,  musamman wanda suka kira da wanda suka yi min text messages da na whatAssp ina godiya Allah ya tabbatar da dumbin alhairin sa a garemu baki daya.'''

My besty wato Khadijah S Muhammad na rasa ta ina zan fara gwada maki irn farin cikin da nake saboda kulawar ki a gareni baya misaltuwa sai dai nace Allah ya faranta maki fiye da yadda kike faranta min,  soyayyar da nake yi maki ba zata faduba, Allah yabar amintarmu har jikoki amin.

             *23*
Wani irin kunya ce ta rufe Salmah, ta ji ina ma kasa zata buɗe ta shige ciki, wani tsalle da ta buga sai ganinta kawai ta yi a bedroom ita kanta ta yi mamakin ganinta a kan gado, Siririyar tsaki ta ja tare da lumshe ido,  tun farko abin da ta guda kenan shi yasa taki biye masa, amma ya cika ta da daɗin baki, har bata san lokacin da ta biye masa ba ga shi ya ja mata abin kunya.
       Hmmmm su Yareema namijin duniya , mai makon ya ji kunyar Hajja sai kawai ya gyarawa Areef kwanciya a kafaɗarsa ya saki murmushi yana faɗin "Hajjata sannu da hutawa." Ya gama maganar ya ida shiga cikin falon. Murmushin takaici Hajja ta yi, cikin zuciyarta mamakin rashin kunyar Yareema take, musamman yadda yake mata magana ko a jikinsa. "Hajja na shigo tun dazun baki nan." Maganar Yareema ce ta dawo da ita cikin tunanin ta. "Ina bangaren mai martaba ne." Hajja ta bashi amsa tana amsan Areef daga hannunsa, don ta lura ba kunyar ta yake ji ba.
      "Zuwa babu sanarwa kuma?" Hajja ta yi tambayar baya ta cirewa Areef riga. "Wallahi kuwa Hajja nima ban tashi da nufin zuwa ba." "Madallah ka kyauta."
    Mik'ewa ya yi tsaye yana faɗin "Hajja bari na je gaida  maimartaba da  Baba Waziri." "Ya kamata." Ta bashi amsa tana nufa bedroom. Cikin zuciyarta kuwa ita kaɗai tasan abin da ta shirya masa daga shi har Salmah.
        Yana ganin ta shige shima kai  tsaya sai kawai ya shige bedroom din Salmah, kwance ya ganta ta takure waje daya, dariya ce ta kama Yareema musamman da yaga ta zaro ido cike da tsoro. Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke ganin Yarima ne ya shigo, sai kuma ta haɗe rai domin dariyar sa ta bata haushi. "Ka daina bana so fa." Cike da shagwaɓa Salmah ta dire maganar. "Hhhhh! Allah dole ne mutum idan ya ganki ya yi dariya kinga yadda kika zama kuwa?"  Ya ci gaba "Hajja fa da mijinki ta ganki kuma ita dinma wajen mijinta ta je, amma duk kin tsure kamar wacce ta yi karya." Ya gama tambayar yana zama bakin gadon da take har alokacin bai bar dariya ba. Kara kwaɓe fuska ta yi ta ce "Ai duk kai ka jawo da baka tafi dani ba ai da haka bata faru ba, kawai ka fitar min daga nan." Ta gama maganar cikin hawaye.
      Bai fita ba sai gyara zama ya yi tare da riko hannunta, cike da kulawa ya ce "Haba Ummuna menene abin yin kuka? Kawai don na shigo dakin ki? To ki kwantar da hankalinki yanzu zan fita, abin da nake so dake shine ki share hawayenki domin Hajja bata ce komai ba, hasalima ta amshi Areef sun shiga bedroom dinta." Ya dire maganar yana share mata fuska. Murmushi ta yi wanda ya kara fito da kyaunta ta ce "Hamma da gaske?" Gyada kai ya yi cikin tabbatar mata da haka.
     "Tom shi kenan yanzu ka tashi kaga babu wanda ya san kazo fa."

"Eh! Yanzu zan fita dama zuwa na yi naga halin da kike ciki."

"Lafiya lau nake ai." Ta gama maganar tana sakin murmushi.

Yarima baice komai ba ya fice daga dakin, kai tsaye yana fita fadar maimartaba ya yi wa tsinke, Maimartaba ya samu tare da Baba Waziri sosai suka gaisa suka dan taba hira sannan ya yi masu sallama, yana fita ya fada bangaren Yawuro yana yin sallama Yawuro ta fara washe baki

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now