37

141 10 0
                                    

KYAKKYAWAR ALAƘA
37

"Da kyau Salmah ashe shi ya sa kika rame kika yi duhu kika lalace? Ashe dai zaman ukuba da rashin 'yanci kike yi a cikin wannan gida? Amma shi ne za ki faɗa mini Wai kin yi rashin lafiya? To wallahi wannan magana sai ta je ga Maimartaba da Hajja, wajibi ne su san irin zaman da kike yi."
"A'a Aunty Wallahi haka ba ta taɓa faruwa ba sai ya..." "Da Allah Malama rufe mana baki, dole ne Hajja ta san wannan magana." Adda Khadijah ta faɗa tana barin falon, ita ma Adda Hafsah bar mata wajen ta yi rai ba ce.
Haka nan jiki babu ƙwari Salmah ta bar falon kai tsaye toilet ya shiga sai da ta gyara jikinta, Allah Ya taimaketa yaji bai shigar mata ido ba kuma abincin baya da zafin da zai iya kona mutum. Zuciyarta sam babu daɗi da faruwar wannan al'amari gaban su Adda Khadijah, yanzu ga shi sun tabbatar mata da sai sun sanar da Hajja har ma da Maimartaba, wanda hakan na iya zama silar rabuwar aurenta da mijinta uban 'ya'yanta, abin da take ji ba za ta lamunta ba. Za ta san yadda za ta yi don ganin Hajja ba ta samu wannan labari ba.
"Ya zama dole na yi wani abu." Ta yi furucin ba tare da ta san ya fito fili ba, har sai da ta ji Adda Hafsah na faɗin "Ki bayar da himma ki yi wani abin, amma duk abin da za ki yi sai Hajja ta ji wannan labari."
"Don Allah Adda ki yi hakuri Wallahi ina son Hamma bana son abin da zai raba mu da shi, kuma na san duk wannan abin da yake yi ba yin kansa ba ne ki taimaka ki yi mini rai kar a rabamu." Cikin kuka Salmah ke magana.
"A'a ai ba rabaku zan ce a yi ba, a'a so nake a amso maki 'yanci daga wajensa, don haka gobe kamar haka Hajja ta samu labarin nan, in Sha Allah za ta yi maki maganin abin da yake damunki." Duk roƙon da Salmah ta yi wa su Adda Khadijah amma fir suka ki amincewa don abin ya tsaya masu a rai, sun so ma kiran wayar Hajja su sanar mata sai dai kuma sun san hankalinta zai iya tashi har ta ce za ta taho a daren, shi ya sa suka bari har zuwa lokacin da za su koma gida.
Ai ko washegari bayan sun karya sun yi wanka suka shirya ko ta kan Yarima ba su bi ba suka bar gidan, don ba ƙaramin haushin sa suke ji ba. Ba wacce ta nufi gidanta kai tsaye gidan Sarki suka nufa don isar wa da Hajja sako.
Tarba mai kyau samu a wajen Hajja, bayan sun gama cin abinci Hajja ke tambayarsu lafiyar Khairat da Salmah. "Hajja Khairat lafiya take, tana gudunta ko ina yanzu ma da zamu taho sai kuka take ta yi." "Ayya ai da kun sani kun zo da ita kila ma uwar juna biyu ke gareta, kar a kuma irin ta Areef."
"Hmmm! Hajja kenan a irin wannan zaman da Salmah ke yi ne har za ta samu juna biyu? Tab." Adda Hafsah ta faɗa tana miƙewa.
"A'a ban gane ba? Ya muna magana za ki mike kuma? Wanne irin zama Salmatyy take yi?" Hajja ta yi tambayar har jiki yana rawa, ina fatan masu karatu ba ku manta kaunar Hajja ga Salmah ba?
"Maganar gaskiya Hajja yanzu fa Salmah ba zaman jin daɗi take a gidan Hamma ba, gabaɗaya ban da wulakanci babu abin da take fuskanta a zaman gidan." Nan dai Adda Khadijah ta kwashe komai da komai da aka yi ta sanar da Hajja. Iya ɓacin rai Hajja ta shiga a zafafe ta miƙe da zumar zuwa Bauchi, da ƙyar su ka shawo kanta har ta yarda ta gasar, amma fa ta jaddada masu gobe da sassafe zata wuce Bauchi za ta dauko Salmah da kanta. Sosai suka gamsu da maganarta, cigaba da kwantar mata da hankali suka yi har sai da suka ga ta dawo daidai sannan ko wacce ta nufi gidanta.
****
"Wai lafiya kuwa Hauwa'u?" Maimartaba ya tambaya cike da damuwa.
Hajja bata motsa ba haka kuma ba fasa kukan da take yi ba, hankalin Maimartaba ya kai ƙololuwar tashi domin tun da yake da ita bai taɓa ganin ta yi irin wannan kukan ba.
"Ki yi wa Allah Hauwa'u ki yi faɗa mini abin da ya sanyaki kuka haka? Ki sani wannan kukan da kike yi ba fa shi ne mafita ba."
"Ya zama dole na yi kuka ranka ya daɗe, yanzu saboda Allah abin da Yaron nan zai saka ma Ummu Salmah da shi kenan?"
"Wanne Yaro kenan? Me kuma ya yi wa Ummu Salmar?"
"Yarima mana."
"Yarima?" Da mamaki ya ke tambayarta.
"Eh! Su Khadijah sun dawo ɗazun suke bani labarin halin da yarinyar ke ciki." Nan ta kwashe ma shi labarin abin da su Adda Khadijah suka faɗa mata.
Shi kan shi Maimartaba ransa ya ɓaci, amma sai ya dake ya fara bata haƙuri tare da rarrashi ya kuma sanar mata da zai dauki mummunar mataki a kan Yarima.
Washegari haka Maimartaba ya sanya aka yi taron gaggawa kan yadda za a ɓullowa lamarin. Bayan kowa ya hallara sai ya yi bayanin maƙasuɗin abin da ya sanya shi kiran su, jikin kowa ya yi sanyi da jin wannan bayani musamman Hamma Ɗan Waziri da ya ke jin kamar ya fi kowa shiga tashin hankali.
Daga karshe Maimartaba ya ce dole zai sanya a je a dauko masa Salmah, don ba zai zuba ido Yarima da matarsa suna ci mata mutunci ba.
"Haka ne ranka shi daɗe, amma sai dai abu guda zan yi maka tuni sanyawa a dauko maka Salmah ba fa shi ne mafita ba, a bar Salmah ta cigaba da zama a gidan aurenta, don duk macen da ka gani a gidan aure to fa tana da ƙalubalen da take fuskanta, shi kuma Yarima addua' za mu yi masa Allah Ya ya ye Masa damuw..."
"Dakata Waziri! Maimartaba ya yi saurin katse shi, ita kam Hajja kululun bakinciki ya ma hanata cewa komai, cikin ranta kuwa ita kaɗai ta san abin da take rayawa. Maimartaba ya cigaba da magana "Ya zama dole mu ɗauki mataki, babu yadda za a yi a ce mu zuba ido muna ganin yarinya cikin wahala, ba zai taɓa yiwuwa ba."
"Amma Hamma ai ba ita ta ce tana cikin matsala ba, kuma ban ma yarda da maganganun su Khadijah ba kawai daga yin kwana biyu har sun fuskanci halin da suke ciki a cikin gidan sam magajin sarki ba zai aikata abin da suka faɗa ba?"
"Tsaya Aysha idan har hasashena ya zama gaskiya ke da Waziri ba ƙaunar Salmah kuke yi ba, ta ya yarinya tana cikin matsala amma kuna yin wata magana ta daban?"
"Amma ai Adda..." "Karki ce mini komai Aysha, na gama lura da take-takenku ke da Waziri, dama tun a lokacin da ya fara maganar aure kuka yi uwa kuka yi maƙarɓiya, ni na san auren na sa ba komai zai jawo ba sai irin wannan tashin hankalin, ai ga irinta nan." A matuƙar hasale Hajja ke magana.
Gabaɗaya zaman haka aka tashi zuciyar kowa a jagule, babu kamar Hajja da take ganin kamar su Baba Waziri ba sa ƙaunar Salmah. Shi ya sa ana tashi ba tare da ta tsaya bi ta kan kowa ba ta bar falon, Hamma Ɗan Waziri ya bi bayanta da niyyar rarrashinta.
"Hajja ki yi haƙuri don Allah kar ki tashi hankali a kan wannan matsalar."
"Dole na tashi hankali Al-ameen, yanzu saboda Allah abin da ya yi ya kyauta kenan?"
"A'a Hajja amma a yi haƙuri."
"Ba zan haƙura ba, idan kuwa kana son na haƙura yanzun ba sai anjima ba, ka je ka ɗauko mota ka kaini gidansu."
Toh Hajja da ladabi Hamma Ɗan Waziri ya amsa, don ya san Hajja fa yau ta je makura. Shi ya sa salin alin ya kawo mota ya dauketa Suka kama hanyar Bauchi.

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now